Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 25/11/2026

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. An kama wani mutum kan zargin tono gawa a wata makabarta a Kebbi

    Rundunar ƴansanda a jihar Kebbi ta kama wani mutum mai shekaru 30 mai suna Tapro Tareza, wanda ake zargi da tono wata gawa a makabartar Machika da ke yankin Ribah.

    An kama mutumin mazaunin ƙauyen Changu ta Gwazawa da ke ƙarƙashin gundumar Kanya ne bayan rahotannin da aka dade ana samu na lalata kaburbura a makabartar.

    Wata sanarwa da kakakin ƴansanda a jihar, SP Bashir Usman ya fitar ranar Talata, ya ce an kama mutumin ne da yammacin ranar 10 ga Nuwamba, jim kaɗan bayan binne wani mamaci.

    Binciken farko da aka gudanar, ya gano cewa ana zargin mutumin da cire wasu sassa daga jikin gawawwakin, inda ya kuma amsa cewa yana da hannu a lalata kaburbura a makabarta, ciki har da cire likkafanin wani mamaci ya tafi da shi.

    Yansandan sun ce ana ci gaba da gudanar da bincike kan mutumin, inda za a gurfanar da shi idan aka same shi da laifi.

    Sun kuma yaba wa al’ummar yankin bisa taka-tsantsan da haɗin gwiwar da suka nuna, tare da gargadin jama’a da su guji ɗaukar doka a hannunsu.

  2. Fitaccen tauraron fina-finai Pete Edochie ya rasu

    An tabbatar da mutuwar ɗan wasan fim na Najeriya Pete Edochie.

    Iyalan shahararren ɗan fim ɗin ne suka fitar da sanarwar rasuwarsa yana da shekara 79 a duniya bayan ya yi fama da cutas kansar bakin mafitsara.

    Edochie ya rasu ne da kimanin ƙarfe 12:30 na daren ranar Laraba.

    Edochie tsohon ɗan jarida ne kuma ɗan fim wanda ya yi suna a kan rawar da ya taka a fina-finan Najeriya, kamar labarin 'Things Fall Apart' da aka yi fim a kan shi, wanda Chinua Achebe ya rubuta.

    Ya rasu ya bar ƴaƴa shida, ciki har da taurarin fina-finai Yul da kuma Linc.

    Fina-finansa da suka shahara sun haɗa da Cross fire, Avenge me Iwene my son, Oracle da kuma Lost Kingdom.

  3. Libya ta ce an kashe mata soji biyu a harin da Ukraine ta kai

    Hukumomi a gabashin Libya sun ce sojojinsu biyu sun mutu sakamakon wani hari da jirgi maras matuki da Ukraine ta kai wa wani jirgin ruwan yaki na Rasha da kuma wani jirgin dakon kaya a birnin Benghazi a ranar Lahadi.

    Mahukuntan sun ce akalla mutum goma sun jikkata.

    A Libya akwai gwamnatoci biyu, ɗaya na zaune a Benghazi da ke gabashin kasar, wadda Rasha ke mara wa baya, da kuma gwamnatin da ƙsashen duniya suka amince da ita wadda ke zaune a Tripoli da ke yammacin kasar.

    Dukkan ɓangarorin biyu sun yi Alla-wadai da harin da Ukraine din ta kai.

  4. An kashe sojojin Rasha 500,000 tun fara yaƙin Ukraine

    Wasu bayanan gwamnati da aka fallasa daga Rasha sun nuna cewa kusan sojojin kasar dubu 500 ne suka mutu tun bayan fara yaki da Ukraine.

    Sashen BBC na Rasha, ya yi nazari kan bayanan mutuwar da wasu masu kutse ta intanet daga Belarus da Ukraine suka samu, inda bayanan suka bayyana irin asarar rayukan da Rasha ta yi a wasu yankuna na Ukraine.

    Bayanan sun nuna cewa kimanin sojojin Rasha dubu 20 ne suka mutu a yayin fafatawar kwace iko da wasu kauyuka goma kacal, wadanda yawan mutanensu kafin barkewar yakin bai wuce mutum dubu 12 ba.

    Rasha dai ba ta fitar da alkaluman mutanen da suka mutu ko suka jikkata a yakin ga jama'a ba.

  5. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Laraba.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.