United na son Collins, Liverpool na dab da cimma sabuwar yarjejniya da Ngumoha

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Manchester United na harin ɗan wasan Brentford Nathan Collins, a matsayin wanda ta ke son ganin lallai ya koma ƙungiyar a watan Janairu. (TalkSport)

Ɗan wasan Japan Ao Tanaka, na dab da shiga sabon kwantaragi da Leeds United zuwa 2029 (Sky Sports News)

Ɗan wasan Leeds Dominic Calvert-Lewin, shi ma na tattaunawa kan tsawaita zamansa a ƙungiyar a dai-dai lokacin da Manchester United ke harin ɗan wasan. (Mail - subscription required)

Bournemouth ta sanya fam miliyan 100 kan ɗan wasan Eli Junior Kroupi ya yin da Arsenal, da Barcelona da Paris St-Germain ke harin ɗan wasan. (TalkSport)

Liverpool na dab da cimma yarjejeniyar tsawaita kwantaragin Rio Ngumoha. (Teamtalk)

Roma na son ɗauko aron Callum Hudson-Odoi daga Nottingham Forest a watan Janairu. (Football Insider)

Como da Napoli na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗauko ɗan wasan Manchester United Joshua Zirkzee a watan Janairu, inda dukkan ƙungiyoyin ke sauraron shirin Mauricio Pochettino akan ɗan wasan. (Sky Sports)

Newcastle United ba za ta siyar da Lewis Hall, ba a kakar siyar da ƴan wasan da za a buɗe a watan Janairu. (iPaper)

Manchester United da Barcelona sun ƙara matsa ƙaimi a shirin su na ɗauko ɗan wasan Borussia Dortmund Mathis Albert. (Teamtalk)

Napoli ta yi wata ganawa da wakilin Scott McTominay a Manchester don ci gaba da tattaunawa kan tsawaita zaman dan wasan. inda kwantaraginsa za ta ƙare a 2028. (Gianluca Di Marzio)