Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE , Abubuwan da ke faruwa da Najeriya da sauran sassan duniya, 24/11/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa da Najeriya da sauran sassan duniya, 24/11/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. 'Jiragen ruwa biyu sun kama da wuta bayan taka nakiya a mashigar Hormuz'

    Rundunar Sojin Ruwa ta Iran ta sanar da cewa wasu jiragen dakon mai guda biyu sun taka nakiyoyi a mashigar Hormuz, lamarin da ya haddasa gobara a cikinsu da safiyar yau.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ambato wta sanarwa daga rundunar sojin ƙasar na tabbatar da faruwar lamarin.

    A wani ɓangaren kuma, Babban Kwamandan Rundunar Sojin Iran, Manjo Janar Amir Hatami, ya ce mashigar Hormuz "za ta ci gaba da kasancewa cikin tsauraran matakai kowace rana, kuma yanayi zai ƙara yin wahala ga abokan gaba."

    A baya mun ruwaito cewa wani jirgin dakon kaya ya kama da wuta a tekun kusa da gaɓar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), kamar yadda Hukumar Kula da Harkokin Kasuwancin Ruwa ta Birtaniya (UKMTO) ta bayyana.

    Hukumar, wadda ke da alaƙa da rundunar sojin ruwan Birtaniya, ta sanar da afkuwar lamarin kwanaki biyu da suka gabata.

  2. Amurka za ta kori ƴan Najeriya 157 daga ƙasar

    Ma’aikatar Cikin Gida ta Amurka (DHS) ta ƙara sunayen wasu ’yan Najeriya 24 a cikin jerin mutanen da take shirin kora daga ƙasar, wanda hakan ya sa jimillar ’yan Najeriyar da ke cikin jerin ta kai 157.

    Hukumar ta ce ta kama mutanen ne bisa zargin aikata manyan lafuka a Amurka.

    Bayanan da ke shafin hukumar cikin cikin gidan sun nuna cewa sabbin mutanen da aka ƙara a jerin an kama su ne bisa zarge-zargen laifuffuka da suka haɗa da damfara, halasta kuɗaɗen haram, laifuffukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi, satar bayanai da kuma muzgunawa ƙananan yara.

    To amma, wallafa sunayen mutanen a shafin hukumar ba yana nufin cewa an same su da laifukan da ake zarginsu da aikatawa ba.

    Hukumar ta ce matakin wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Donald Trump na fitar da ’yan ƙasashen waje da ake zargi da aikata manyan laifuffuka daga Amurka.

    A cikin bayanin da aka wallafa tare da jerin sunayen, hukumar ta ce tana ƙokarin cika alƙawarin Shugaba Trump na fitar da mafi munin masu laifi daga cikin baƙin haure da ke zaune a Amurka.

    To sai dai hukumar ba ta bayyana lokacin da za a tisa ƙeyar mutanen zuwa Najeriya ba.

    A watan Satumbar da ya gabata ne hukumar ta tsaron cikin gida ta Amurkan ta ce ta kama ’yan Najeriya 134 a cikin jerin masu fuskantar kora daga Amurka kan zarge-zargen damfara da halasta kuɗaɗen haram.

    Tun bayan komawarsa kan karagar mulkin Amurka a 2024, Shugaba Trump ya ƙudiri aniyar rage baƙin haure a Amurka, ta hanyar korar wadanda ya ce sun shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida, ko wadanda takardun zamansu suka ƙare.

    Amurka dai na daga cikin ƙasashen duniya da ke yawan fuskantar baƙin haure daga ƙasashe duniya daban-daban, musamman matalautan ƙasashen.

    Baƙin haure kan je ƙasar ne sakamakon dalilai mabambanta da suka haɗa da gudun hijira da neman ingantacciyar rayuwa ko karatu da sauransu.

  3. Na ga ƙofofin jahannama da shaiɗan har sau uku a rayuwata - Fafaroma Francis

    A rubuce-rubucen kundin tarihin rayuwarsa, marigayi Faparoma Francis ya bayyana cewa ya ga wata halitta da ya bayyana matsayin ganin Shaiɗan da kuma ƙofofin wutar jahannama.

    An wallafa wasu sassa na kundin a ranar Talata, waɗanda suka ƙunshi bayanai daga fiye da shekara 30 na rayuwarsa.

    A cikin rubutun, Faparoma Francis ya ce ya yi karo da abin da ya ɗauka a matsayin Shaiɗan har sau uku a tsawon rayuwarsa.

    Na farko ta tagar mota, sai na biyun a cikin wani ɗakin ibada na mabiya Carmelite, sannan na ƙarshe yayin wani taro a birnin Rome.

    Ya bayyana Shaiɗan da mai idanu masu walƙiya kamar wuta, tare da murya mai ƙarfi da kaushi.

    Kundin ya kuma ƙunshi tunaninsa game da laifi da nadama da kuma tsufa da mutuwa.

  4. Tsohon shugaban ma'iakatan Hegseth ya buƙaci ya yi murabus

    Tsohon shugaban ma'aikatan Pete Hegseth Joe Kasper, ya buƙaci Hegseth ya yi murabus, yana mai cewa ya daina kasancewa cikin halin da zai iya jagorantar rundunonin sojin Amurka yadda ya kamata.

    Kasper ya bayyana hakan ne a wata hira da mujallar Politico, inda ya soki yadda Hegseth ke tafiyar da Ma'aikatar Tsaro, yadda ya gudanar da yaƙin Iran, da kuma korar manyan jami'an soja.

    Ya ce ƙarfin Hegseth na gudanar da ayyukansa ya ragu, kuma nan gaba kaɗan zai iya kasa sauke nauyin aikinsa yadda ya kamata.

    "Saboda wannan dalili da wasu dalilai daban, lokaci ya yi da ya kamata Pete ya sauka daga mukaminsa," in ji Kasper a hirarsa da Politico.

    Har ila yau, ya ce dangantakar Hegseth da Majalisar Dokokin Amurka ta taɓarɓare sosai, yana zarginsa da rusa alaƙar da yake da 'yan majalisar gaba ɗaya.

  5. Bayanin ƙasashe 10 da za su yawan musulmai a 2050

    Najeriya za ta zama ƙasa ta huɗu mafi yawan Musulmai a duniya nan da shekarar 2050, a cewar wani sabon hasashe.

    Baya ga Najeriya, ga jerin ƙasashen da ake sa ran za su fi yawan Musulmai a duniya nan da 2050.

  6. Larabawan Mahmud sun nemi mafaka a Tafkin Chadi

    Fiye da mutum dubu na al'ummar Larabawan Mahamid sun nemi mafaka a yankin Tafkin Chadi.

    Bayan umarnin da hukumomin Nijar suka bayar na cewa su fice daga ƙasar kafin ranar 31 ga Disamban shekarar 2026, Larabawan sun isa garin Daboua da ke ƙaramar hukumar Fouli, inda hukumomin Chadi ke ɗaukar matakan karɓarsu tare da ba su agajin jin ƙai, kamar yadda shafin x na kafar yaa labaran Le N'Djam Post ya wallafa.

    Dangane da wannan lamari, hukumomin Chadi ciki har da shugaban ƙaramar hukumar Fouli, Dimouya Souapebe, sun shirya yadda za a tarbe su, tare da samar musu da agajin gaggawa na farko wanda ya haɗa da abinci da kayan matsuguni domin biyan buƙatun iyalan da suka rasa muhallansu.

    Ministan Sadarwa na Chadi, Gassim Chérif Mahamat, ya sake jaddada aniyar gwamnati ta karɓar waɗannan mutane cikin mutunci, daidai da al'adar ƙasar Chadi ta nuna goyon baya da taimakon jin ƙai ga mabukata.

  7. Sanata Barau ya tara malamai 2,000 don yi wa Tinubu addu'a

    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin, ya nemi goyon bayan malaman addinin Musulunci daga ƙananan hukumomi 13 da ke yankin Sanatan Kano ta Arewa domin sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027.

    Sanata Barau ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da malaman addinin Musulunci sama da 2,000 a Kano.

    Ya buƙace su da wayar da kan jama'a wajen mara wa Shugaba Tinubu da sauran 'yan takarar jam'iyyar APC baya, yana mai cewa shugaban ƙasar na da kyakkyawar manufa ga Jihar Kano da yankin Arewa maso Yamma da Arewa baki ɗaya da kuma Najeriya gaba ɗaya.

    A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Isma'il Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya yaba da addu'o'i da shawarwari da kuma gudunmawar malaman wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Jihar Kano.

    "Wannan taro ne na iyayenmu da shugabanninmu da malamai da limamanmu. Ku ne jagororinmu. Ina maraba da ku baki ɗaya tare da nuna godiyata bisa addu'o'i da goyon bayan da kuke ba mu''.

    Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawar ya ce Kano ta daɗe tana taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa, inda ya tuna da gudunmawar marigayi Malam Aminu Kano da sauran fitattun jagororin jihar.

    Sanata Barau ya kuma tuna cewa bayan zaɓen shekarar 2023, shi ne mutum na farko daga Jihar Kano da ya zama Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa.

  8. An kashe mutum huɗu a hari kan tawagar yaƙin zaɓen Omo-Agege

    Gwamnatin Jihar Delta ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga a ƙaramar hukumar Ughelli North bayan wani hari da aka kai wa tawagar yaƙin neman zaɓen tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya kuma ɗan takarar sanata na jam'iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) mai wakiltar Delta ta tsakiya, Sanata Ovie Omo-Agege.

    Rundunar ƴansandan jihar ta tabbatar da mutuwar mutum shida a lokacin harin.

    Harin ya faru ne ranar Litinin yayin ziyarar yaƙin neman zaɓe da Omo-Agege ya kai ƙauyen Uduere, inda wasu ƴan bindiga suka buɗe wa magoya bayansa wuta, lamarin da ya haddasa firgici a yankin.

    Rahotanni sun ce Omo-Agege bai samu rauni ba, duk da cewa harsasai sun ratsa kusa da kansa lokacin da yake jawabi ga taron da ya taru domin tarbarsa.

    Ɗaya daga cikin waɗanda suka rasa rayukansu shi ne Moses Anaughe, tsohon ɗan Majalisar Dokokin Jihar Delta mai wakiltar mazaɓar Ughelli North II, kuma mataimaki na musamman ga Omo-Agege.

    Rahotanni sun ce ya rasu ne a Babban Asibitin Ughelli, inda aka kai shi domin kula da lafiyarsa bayan ya samu raunukan harbin bindiga a harin.

  9. Amurka za ta lalata fiye da da tan 60 na abubuwan fashewa da suka lalace

    Rundunar sojin Amurka ta ce za ta tarwatsa sama da tan 60 na abubuwan fashewa da suka lalace a ranar Laraba.

    Sanarwar ta zo ne bayan da wani alkali ya yanke hukuncin cewa rundunar za ta iya ci gaba da aiwatar da shirin.

    Tun da farko, mazauna yankunan da ke kusa da masana'antar makamai ta Iowa Army Ammunition Plant sun samu umarnin kotu da ya dakatar da tarwatsa kayan fashewar, saboda fargabar gurbata muhalli.

    Sai dai rundunar sojin ta ce matsanancin sanyin da ake fuskanta na iya sa kayan fashewar su fashe da kansu ba tare da an tayar da su ba.

  10. DR Kongo na neman jirginta da ƴantawaye suka ce sun harbo

    Rundunar sojin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ta ce ana ci gaba da neman ɗaya daga cikin jiragenta bayan wasu ƙungiyoyin ƴan tawaye sun yi iƙirarin cewa sun harbo jirgin a gabashin ƙasar.

    Rundunar sojin ta ce an daina jin ɗuriyar jirgin ne a ranar Lahadi sakamakon mummunan yanayi.

    A ɓangare guda, haɗakar ƙungiyoyin ƴan tawaye na FRN sun ce sun yi nasarar kai hari kan wani jirgin yaƙin gwamnati a wannan rana.

    Rahotanni sun ce faɗan da ake gwabzawa tsakanin sojojin gwamnati da ƙungiyar FRN ya tsananta a yankin gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

  11. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Talata.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukan sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.