Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Sanatoci 8 da ba su gabatar da ƙuduri ko ɗaya ba a Majalisa 10
Ƙungiyar da ke nazarin bayanan siyasa da tattalin arziki na cikin gida da na ƙasashen duniya, StatiSense, ta fitar da sunayen sanatocin Najeriya da ba su gabatar da ko da ƙuduri ko ɗaya a Majalisar Dattawa ba tun bayan hawansu kan mulki.
Ƙungiyar ta wallafa sunayen manyan 'yan majalisar, maza da mata, waɗanda kawo yanzu ba su gabatar da wani batu da za a tattauna ko kuma nazari a kansa a majalisar ba.
Zaɓen shekarar 2023 ne ya kafa majalisa ta 10, wadda a yanzu ta shafe shekaru uku da watanni shida.
Rahoton na StatiSense ya ƙunshi bayanan da aka tattara daga shekarar 2023 zuwa watan Nuwamban 2026.
Waɗanne Sanatoci ne?
A rahoton da StatiSense ta fitar kwanan nan, ƙungiyar ta bayyana sunayen sanatoci takwas tare da mazaɓun da suke wakilta.
Ga sunayensu:
- - Nwachukwu Emmanuel, mai wakiltar Anambra ta Kudu.
- - Abdulaziz Abubakar Yari, mai wakiltar Zamfara ta Gabas.
- - Ahmad Ibrahim Lawan, mai wakiltar Yobe ta Arewa.
- - Olaka Nwogu, mai wakiltar yankin Kudu maso Gabashin Ribas.
- - Dayo Faduyile, mai wakiltar Ondo ta Kudu.
- - Jiya Peter Ndalikali, mai wakiltar yankin Kudancin Neja.
- - Ikeje Israel Asogwa, mai wakiltar Enugu ta Arewa.
- - Danladi Envulu-Anza, mai wakiltar Nasarawa ta Arewa.
Ƙungiyar ta jaddada cewa wannan bayanin ba ya da alaƙa da sauran ayyuka da matakan da sanatocin suka ɗauka wajen tunkarar batutuwan da suka shafi majalisar.
Sanatocin da suka fi gabatar da ƙudurori a Majalisar Dattawa tun 2023
Tsakanin watan Yunin 2023 zuwa Nuwamban 2026, aƙalla sanatoci 14 ne suka gabatar da ƙudurori a gaban Majalisar Dattawa.
Jimillar ƙudurorin da suka gabatar sun kai 25, inda aka tantance da kuma tattauna da dama daga cikinsu, wasu kuma suka zama dokoki.
Ga sunayen sanatocin da adadin ƙudurorin da kowannensu ya gabatar:
- - Sanata Michael Opeyemi Bamidele – ƙuduri tara.
- - Sanata Barau I. Jibrin – ƙuduri uku.
- - Sanata Adeola Solomon Olamilekan – ƙuduri biyu.
- - Sanata Joel-Onowakpo Thomas Ewomazino – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Fadeyi Oluwole Olubiyi – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Mohammed Sani Musa – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Ikra Aliyu Bilbis – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Umar Shehu Buba – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Sani Bello Abubakar – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Ekpenyong Asuquo – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Mukhail Adetokunbo Abiru – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Patrick Ndubueze – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Abdulhamid Mallam-Madori Ahmed – ƙuduri ɗaya.
- - Sanata Jibrin Isah – ƙuduri ɗaya.
Rahoton ya ce daga cikin ƙudurori 25 ɗin, mafi yawan waɗanda aka amince da su Shugaban Ƙasa ya sanya wa hannu, yayin da kashi 36 cikin 100 na ƙudurorin Sanata Michael Opeyemi Bamidele ya gabatar da su.
Haka kuma, sanatoci uku ne suka gabatar da kashi 56 cikin 100 na dukkan ƙudurorin.
Sauran sanatoci 11 kuma kowannensu ya gabatar da ƙuduri guda ɗaya.
Mata da suka nemi kujerar sanata a zaɓen 2023
Haka kuma, rahoton ya bayyana adadin matan da suka tsaya takarar kujerar sanata a zaɓen 2023 a yankuna daban-daban na Najeriya.
Ga yadda adadin ya kasance:
- - Kudu maso Kudu – 'yan takara 22.
- - Kudu maso Yamma – 'yan takara 21.
- - Arewa maso Gabas – 'yan takara 21.
- - Kudu maso Gabas – 'yan takara 16.
- - Arewa ta Tsakiya – 'yan takara 10.
- - Arewa maso Yamma – 'yan takara bakwai.
Yankuna uku na kudancin Najeriya sun samu jimillar mata 'yan takara 59, wanda ya kai kashi 60.8 cikin 100 na jimillar mata 97 da suka tsaya takara a faɗin ƙasar.