Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ko Sifaniya za ta sake taka irin rawar da ta taka a gasar kofin duniya ta 2010?
- Marubuci, Mohammed Abdu
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 3
Sifaniya za ta kara da Argentina a wasan ƙarshe a gasar cin kofin duniya 2026 ranar Lahadi a birnin New York ɗin Amurka.
Sifaniya mai kofin duniya ta kawo wannan matakin, bayan doke Faransa da cin 2-0 a zagayen daf da karshe ranar Talata.
Ita kuwa Argentina mai rike da kofin kuma na uku jimilla, ta samu damar nan sakamakon fitar da Ingila daga gasar da cin 2-1 ranar Laraba.
Ƙasar Sifaniya ta fara lashe kofin duniya tilo a karon farko a gasar da aka buga a 2010 da Afirka ta Kudu ta shirya.
To sai dai kuma tawagar ta Sifaniya da ta lashe kofin duniya na 2010 tana da kamanceceniya da wadda take buga gasar bana.
Jerin kamanceceniya tsakanin Sifaniya ta 2010 da ta 2026
Sifaniya ta halarci gasar kofin duniya a matakin mai rike da kofin nahiyar Turai
- 2010: Ta lashe Euro 2008 .
- 2026: Ta ɗauki Euro 2024.
Sifaniya ta doke Portugal 1-0 a zagayen ƴan 16
- 2010: David Villa ne ya ci Portugal 1-0.
- 2026: Mike Merino ne ya zura ƙwallo a ragar Portugal.
Real Madrid ta ɗauki Jose Mourinho kafin a fara gasar kofin duniya
- 2010: Mourinho ya koma Real Madrid daga Inter Milan.
- 2026: Mourinho ya sake komawa Real Madrid daga Benfica
Real Madrid ta yi kaka biyu ba tare da lashe kofi ba
- 2009/10
- 2025/26
Wasan farko a buɗe gasar kofin duniya shi ne tsakanin Afirka ta Kudu da Mexico
- 2010: Afirka ta Kudu 1–1 Mexico.
- 2026: Afirka ta Kudu 2-0 Mexico
Sifaniya ta dogara da ƙwazon ƴan wasan Barcelona
- 2010: Xavi da Iniesta da Busquets da kuma Xabi Alonso.
- 2026: Rodri da Pedri da Fabián Ruiz da kuma Dani Olmo.
Ɗan wasan Barcelona da ya zama gwarzo a gasar kofin duniya
- 2010: Andrés Iniesta yana daga cikin wanda ya bayar da gagarumar gudunmuwa
- 2026: Lamine Yamal yana daga cikin fitattun ƴan wasan tawagar Sifaniya a bana
Ƴan wasan Barcelona ne suka fi yawa a tawagar Sifaniya
- A shekarar 2010 ƴan wasan Barcelona ne suka fi yawa a tawagar Sifaniya
- A 2026 ma, ƴan ƙwallon Barcelona aka fi gayyata daga ciki har da Lamine Yamal da Pedri da Pau Cubarsí da sauransu.
Sifaniya ta lashe kofin da ƙwallaye da yawa bai shiga ragarta ba
- A 2010 Sifaniya ta ci ƙwallo takwas jimilla, wasu wasannin da 1-0, kuma guda biyu ne suka shiga ragarta.
- A 2026 tawagar Sifaniya ta zura ƙwallo 15 a raga an kuma ci ta ɗaya tal, duk da an kara yawan kasashen da ke buga babbar gasar tamaula ta duniya.
Hakan ne ya sa wasau masu bibiyar wasannin tamaula suke hasashen cewar watakila Sifaniya ce za ta lashe kofin duniya na bana, saboda irin kamanceceniya tsakanin tawagarta ta 2010 da kuma mai buga wasannin bana.
Sai dai abin tambaya ko sau nawa aka haɗu tsakanin kasashen biyu a babbar gasar tamaula ta duniya?
Wannan shi ne karo na biyu da kasashen za su kece raini a gasar kofin duniya, bayan 1966 a Villa Park, lokacin da Ingila ta gudanar da gasar ta kuma lashe kofin a karon farko, wanda shi ne tilo da take alfahari da shi.
Argentina ce ta yi nasarar cin 2-1, kuma a zagaye na biyu aka ci dukkan ƙwallo uku.
Ɗan wasan Argentina, Luis Artime ne ya zura ƙwallo biyu a raga, yayin da Pirri ya ci wa Sifaniya ɗaya.
Za a buga wasan karshe ranar Lahadi a birnin New York ɗin Amurka.