Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me ya sa rashin nasarar Ingila a hannun Argentina ta zama mafi raɗaɗi?
Shekarun da tawagar Ingila ke bakin cikin kasa lashe kofin duniya za su haura 60 yanzu haka, amma rashin nasarar da tawagar ta yi 2-1 a hannun Argentina a zagayen daf da karshe ranar Talata na iya zama mafi raɗaɗi daga abin da ta fuskanta a wasannin baya.
Rabon Ingila da kofin duniya tun 1966 a Wembley lokacin da ta karɓi baƙuncin gasar.
Ƴan wasan Ingila da kocinsu Thomas Tuchel sun samu damar da za su kafa tarihin lashe kofin a bana, inda Anthony Gordon ya zura ƙwallo a raga a minti na 55, wato bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.
Sai dai wannan damar ta kubuce musu, sakamakon yanke shawara daga Tuchel wanda ya haifar da karin kai hare-hare daga Argentina ɗaya bayan ɗaya karkashin jagorancin Lionel Messi.
Bayan da lokaci ya ja sosai sai Argentina ta farke ƙwallon ta hannun Enzo Fernandez, saura minti biyar lokaci ya cika.
Daga nan Ingila ta kara shiga cikin matsin lamba da ta kai Lautaro Martinez ya karya musu gwiwa a lokacin da ya kara ƙwallo na biyu.
Ingila ba ta samu damar farke ƙwallon ba, balle a kai ga karin lokaci ko kuma ta kai ga bugun fenariti - hakan ya kawo ƙarshen mafarkin Ingila na lashe kofin bana, wadda ba ta kai wasan ƙarshe ba, amma tana da damar buga neman mataki na uku da Faransa ranar Asabar.
Tuchel ya gaza aikin da aka ba shi a Ingila
Babban abin da ya bambanta Tuchel lokacin da ya gaji Sir Gareth Southgate a aikin horar da tawagar Ingila shi ne tunanin cewa zai lashe kofin duniya da magabacinsa bai iya yi ba.
Tuchel yana gudanar da aikinsa cikin nutsuwa, kuma kawo yanzu bai samu suka irin yadda aka yi wa Southgate lokacin da ya sha kashi a wasan karshe a Euro a hannun Italiya da Sifaniya, da kuma karawar kusa da ƙarshe a Kofin Duniya a 2018 a hannun Croatia ba.
Yanzu dai Tuchel ne zai fuskanci irin waɗannan sukar, saboda wannan shawarar da ya yanke da sauye-sauyen da ya yi a karawar daf da karshe da Argentina.
Hukumar Kwallon Kafar Ingila ta zabi naɗa shi da gaggawa, domin maye gurbin Southgate bayan kammala Euro 2024, inda suka ɗauki gogagge mai iya lashe kofuna wanda aka ɗora masa alhakin lashe Kofin Duniya na 2026, da hakan zai sa a kara ɗora ''tauraro na biyu a kan rigar tawagar Ingila'' kamar yadda Tuchel ya bayyana.
Kaiwa wasan Ingila zagayen daf da karshe za a iya kallon shi a matsayin matsakaicin sakamako, kuma a mafi tsananin hukunci, gazawa ce, saboda an ɗauke shi ne domin Ingila ta fita daga takaicin kasa lashe kofin duniya da take ta jira sama da shekara 60.
Dole a yi ta nemo laifin da Tuchel ya yi da ta kai Ingila ta kasa kaiwa zagayen karshe, wasu na cewa sauyin ƴan wasa da ya yi, wasu na cewar yadda Ingila ta koma tsare baya, saboda ta ci ƙwallo, bayan da saura lokaci da yawa kafin a tashi daga karawar.
Sai idan irin wannan salon ya yi wa Ingila a karawa da Mexico da kuma Norway, amma hakan ya kasa tasiri a kan Argentina mai ƙwararren koci da fitattun ƴan wasa da kuma kyaftin Messi.
Kuskuren Tuchel karara shi ne da ya cire Gordon, wanda ya ci ƙwallon ya saka mai tsaron baya, Ezri Konsa saura minti 18 a tashi, sannan ya koma tsarin masu tsaron baya biyar.
Sannan ya saka Nico O'Reilly da Dan Burn a madadin Declan Rice da Reece James.
Nan take Tuchel ya bayyana cewar ya yi kuskure.
Domin tsarin da ya yi ya sa Ingila ta kara shiga matsin lamba daga Argentina, kuma bai hana a farke a kuma kara musu ƙwallo na biyu ba.
Kusan duk laifin wannan rashin nasarar yana kan Tuchel ne.
A alkaluma wasan sun nuna kuskuren Tuchel da cewa Ingila ta mallaki ƙwallo kashi 12% ne kawai tsakanin lokacin da ta fara jagoranci da kuma ƙwallon da Lautaro Martinez ya farke a kusan minti 40 tsakani.
Saboda tsananin bukatar kai hari ga Argentina daga ƙarshe, Tuchel ya saka Ivan Toney bayan minti na 96, wanda shi ne karon farko da aka saka shi a gasar.
Wannan takaitaccen lokacin da aka bai wa Toney dama, ya sake jawo tambayoyi kan wasu daga cikin canjin Tuchel.
Shin an gayyaci Toney ne kawai domin bugun fenariti ne ko kuwa?
Haka kuma mahawara kan zabin masu tsaron baya da Tuchel ya yi, musamman daga ɓangaren dama za a ci gaba da yin ta.
Haka kuma Tuchel ya yi caca da ya gayyaci Reece James mai yawan fama da rauni, saboda haka lokacin da dan wasan Chelsea ya samu matsalar sai aka samu ɓaraka a gurbin da yake bugawa.
An rika sauya ƴan wasa tsakanin Jarell Quansah wanda ya ji rauni a wasan Panama sannan aka kore shi a wasan Mexico, inda ake saka Djed Spence da Ezri Konsa kafin James ya murmure ya kuma buga wasan daf da karshen.
Duk wannan na faruwa ne yayin da Trent Alexander-Arnold ke kallon gasar daga gida, saboda ba a gayyace shi ba.
Haka kuma dole za a yi nazari za a sake shawarar da Tuchel ya yi watsi da Cole Palmer da Phil Foden, duk da cewa dukkan su ba sa kan ganiya a kakar da aka kammala da kuma Morgan Gibbs-White na Nottingham Forest.
Shin wannan ne mafi raɗaɗin rashin nasarar Ingila?
Ingila ta sha wahala sosai tsawon shekaru a neman sake lashe kofin duniya, duk da cewar tana da gasar tamaula mafi shahara a duniya, sau ɗaya ta taɓa lashe kofin a 1966, wanda wasu suke ganin ya kamata a ce tana da kofunan da yawa.
Wasan da Ingila da Argentina ta buga a ranar Laraba na hamayya ne a koda yaushe, akan bar tarihi da yin abin bajintar da za a dade ana tunawa.
Da yake karawar ta daf da karshe ce a gasar kofin duniya, za ta kasance ana tunawa da ita har abada, watakila Ingila, da ba Argentina ta haɗu da ita ba, ta kai wasan karshe, domin akwai karawar da ita ake fara ci daga baya ta farke ta kara ta kuma kai zagayen gaba.
Wannan ita ce dama ta baya-bayan nan don fafatawar neman mataki na uku da za ta kara da Faransa a ranar Asabar, yayin da ake sa ran buga karawar karshe ranar Lahadi a New Jersey.
Ƙwallon da Gordon ya zura a raga ta ba Ingila wani matakin kaiwa zagayen gaba a wasan da ya kasance na hamayya, daga baya Ingila ta koma ta tare gida da ta kai Argentina ta yi mata illa, lokacin da Ingila ke hangen kaiwa wasan karshe.
Ganin irin damar da Ingila ta samu da sakacin da ta yi a wasan Ingila zai daɗe a tarihi da ba za a manta da shi ba a fannin taka leda a duniya.
Me Ingila za take tunawa a wannan Gasar Kofin Duniyar?
Ingila za ta ci gaba da tuna wani abin mamaki da ta yi a filin Azteca da ke Mexico City lokacin da ta yi kokari sosai ta doke mai masaukin baki Mexico da ci 3-2 a zagayen ƴan 16.
Daya ne daga cikin manyan nasarorin Ingila a Gasar Kofin Duniya, lokacin da Jude Bellingham ya taka rawar da ta kai yana zaman gwarzon wasa karo da dama, kuma sauye-sauyen Tuchel da dabarunsa suka nuna cewa watakila shi ne wanda zai iya kai Ingila har karawar ƙarshe.
Bellingham yana kan ganiya tare da kyaftin Harry Kane, amma dan wasan Bayern Munich zai ji zafin wannan samun koma bayan, domin zai kai shekara 36 da haihuwa kafin Gasar Kofin Duniya ta gaba da za a yi a 2030.
Ingila ta nuna juriya wajen da aka zura mata ƙwallo a raga daga baya ta kai zagayen gaba a kan DR Congo da kuma fafatawa da Norway a wasan kwata-fainal.
Wane kalubale ne a gaban Tuchel?
Ƙwantiragin Tuchel da Hukumar Kwallon Kafar Ingila tun farko an tsara ta ne har zuwa karshen wannan Gasar Kofin Duniya, amma a watan Fabrairu an ba shi sabuwar yarjejeniya har zuwa Euro 2028.
Wannan ya zo da mamaki kuma ya kasance babban nauyi ga Hukumar, musamman ganin cewa ba ta san yadda Gasar Kofin Duniya za ta kaya ba.
Ba za a iya cewa gasar da Tuchel ya kai Ingila zuwa wannan matakin an samu nasara ba, saboda kofin ake son ya lashe, amma yana da goyon bayan Hukumar don jagorantar tawagar zuwa gasar nahiyar Turai wato Euro ta nan gaba.
Ingila za ta bukaci wani mataki na sake gina tawagar, kuma da alama fitaccen John Stones ya kammala buga wa Ingila wasa.
Sannan kuma, ko Tuchel zai ci gaba da yarda da Marcus Rashford?
Mai tsaron gida Jordan Pickford yana da shekara 32 don haka zai iya ci gaba, amma dole ne a samo matasa wadanda za su gaje shi.
Rio Ngumoha mai shekaru 17 na Liverpool tauraron Ingila ne, wanda ya taka rawar gani a wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.
Saboda haka Tuchel yana da aikin gina sabuwar tawagar Ingila, domin fuskantar Euro na nan gaba da za a saka ran zai lashe kofin.
Da zarar komai ya tafi yadda ake so watakila ya ci gaba da aiki zuwa karshen gasar kofin duniya ta 2030, idan kuma bai yi kokari ba a raba gari bayan gasar nahiyar Turai.
Declan Rice da Elliot Anderson za su iya zama ginshikin gurbin tsakiya a shekaru masu yawa, yayin da Bukayo Saka idan yana cikin koshin lafiya zai kasance babbar kadara ga Ingila.
Har yanzu Tuchel na da Foden da Palmer da Gibbs-White da zai yi la'akari da su, tare da Adam Wharton na Crystal Palace, yayin da matashi mai wasa daga gefen gaba mai shekara 17 na Liverpool Rio Ngumoha zai ci gaba da kokari fiye da yadda ya yi a lokacin wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya.
Akwai kuma matashi mai shekaru 16 na Arsenal, Max Dowman, wani karin misali da ke nuna cewa makomar Ingila na iya zama mai haskakawa.
Amma a halin yanzu, zafin rashin nasarar da aka yi a hannun Argentina, da yadda abin ya faru, zai dauki lokaci kafin Ingila da Tuchel da magoyan Ingila su mance da abinda ya faru.