Real Madrid da sauran kungiyoyi 10 mafiya arziki a duniya

    • Marubuci, Michael Emons
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 3

An bayyana Real Madrid a matsayin kungiyar kwallon kafa mafi arziki a duniya, inda Barcelona ta kera Manchester United a matsayin ta biyu, a yanzu United ta samu-koma baya zuwa ta uku.

A jerin kungiyoyi masu arziki na duniya na mujallar Forbes, ya nuna cewa Real Madrid na da arzikin da ya kai dala biliyan 9.5 (fam biliyan 7.06), inda ya karu daga dala biliyan 6.75 (fam biliyan 5.02) da yake, shekara daya da ta gabata.

Barcelona da ke matsayi na biyu na da arzikin da ya kai dala biliyan 7.5 (fan biliyan 5.57) sai kuma Manchester United a matsayi na uku da dala biliyan 7.2 (fam 5.35).

Kudin shiga da United ta samu a kakar 2024-25 ya kama dala miliyan 865 (fam 643), lokacin da ta kare a amatsayi na 15 a teburin gasar Premier kuma ta yi rashin nasara a wasan karshe na gasar Europa.

Gasar Premier na da kungiyoyi 6 a cikin 10n farko kuma tana da kungiyoyi 11 a cikin 30 din da aka lissafo.

Liverpool wadda ta lashe gasar Premier a 2024-2025 ta rike kambinta a matsayi ta 4, inda arzikinta ya kai dala biliyan 6.2 (fam biliyan 4.61) yayin da Manchester City ta rikito daga matsayi na 4 zuwa na 5, inda arzikinta ya kai dala biliyan 5.5 (fam 4.09).

Bayern Munich ce ta shida mai arziki dala biliyan 5.7, (fam 4.24) sai dai zakarun gasar Champions League na 2024-25 Paris St-Germainai na da arziki dala biliyan 5.8, (fam biliyan 4.31bn) inda ta tsallaka daga mataki na 7 zuwa mataki na 5.

Arsenal mai arzikin da ya kai dala biliyan 5.4, (fam biliyan 4.01) ita ce ta 8, sai Chelsea ta 9 da arziki dala biliyan 4.2 (fam biliyan 3.12) ita kuma Tottenham mai arziki dala biliyan 3, (fam biliyan 2.23) ita ce a matsayi na 10.

To sai dai Arsenal za ta iya kara yin sama cikin jerin a shekara mai zuwa ganin cewa ta lashe gasar Premier kuma a karon farko cikin shakara 22 ta kai wasan karshe na Champions League.

Duk da cewa Real Madrid ba Barcelona ne a sama, a matsayi na daya da na biyu, to amma karin kungiya daya tilo daga gasar La Liga ta Sapin ita ce Atletico Madrid wadda ke a matsayi na 11.

Yayin da take da kungiyoyi 11 a cikin 30, gasar Premier ita ce kungiyar da ta fi yawan kungiyoyi a cikin jerin masu arzikin na duniya.

Akwai kuma kungiyoyi 7 daga gasar kungiyoyin kasar Amurka MLS, sai hudu daga gasar Italiya ta Seria A, uku daga gasar Bundusliga ta Jamus sai kuma daddaya daga gasar Ligue 1 ta Faransa da daya daga gasar Primera Liga ta kasar Portugal.

Hakan na nufin kowace kungiya na da dukiya gwargwadon dala biliyan 2.9 a jimlla, inda aka samu habbaka na kashi 21% idan aka kwatanta da alkaluman baya na dala biliyan 2.4 ga kowace kungiya.

Sauran kungiyoyin Premier League da ke cikin jerin kungiyoyi masu arziki na duniya su ne Aston Villa mai jimillar dukiya dala biliyan 1.4 a matsayi na 16, sai Newcastle United mai dala biliyan 1.25 a matsayi na 18, Everton mai dala miliyan 930 a matsayi na 25, Fulham ma da dala miliyan 920 a matsayi na 26, sai Brighton mai dala miliyan 910 a matsayi na 27.