'Mun haɗa kuɗin fansa sama da miliyan 150 amma ba a sako ƴan'uwanmu ba'

Asalin hoton, @HQNigerianArmy
Kimanin wata biyar kenan bayan da ƴan bindiga suka dira a ƙauyen Woro na jihar Kwara, inda suka yi wa mutane ɗaya daga cikin kisan gilla mafi muni da aka gani a baya-bayan nan a Najeriya.
Ɓarnar da ƴan bindigar suka yi ta ƙazanta, lamarin da ya janyo hankalin ɗaukacin al'ummar Najeriya da ma masu sanya ido kan harkar tsaro a ƙasashen ƙetare.
Ƴan bindiga sama da 100 ne ɗauke da makamai suka kai harin a ƙauyuka biyu – Woro da Nuku – suka yi kashe-kashe, suka ƙona gidaje sannan suka tafi da wasu.
Mazauna yankin sun ce yanbindigar sun kashe mutum fiye da ɗari biyu da sittin, kuma suka yi awon gaba da mutum dari da saba'in da shida, baya ga kona gidaje fiye da talatin.
"Sun kashe yarana biyu, sun sace matata da yarana uku," in ji Umar Salihu, mai sarautar gargajiya na yankin.
Sai dai yayin da lokaci ke tafiya, kowace daƙiƙar agogo da ta wulga, tamkar ƙarin raɗaɗi ne a zukatan iyalan waɗanda aka tafi da nasu, kasancewar ba su san halin da suke ciki ba a inda suke cikin daji tare da mahara.
Abin ma ya fi zafi ganin cewa har an ceto wasu da aka sace daga baya a jihar Oyo mai maƙwaftaka, inda a yanzu mutunen Woro ke ganin tamkar hukumomi sun yi watsi da su.

Asalin hoton, Reuters
A kan haka ne ƙungiyoyin ci gaban al'ummar yankin suka ƙara ƙaimi wajen kiraye-kirayen da suke yi game da ceto mutanensu da ƴanbindigar suka sace tun a ranar 3 ga watan Fabrairun 2026.
Mutanen yankin sun gudanar da zanga-zangar lumana domin jaddada rokon a taimaka a kuɓutar da mutanen da aka sace, kamar yadda aka yi ƙoƙarin kubutar da malamai da ƴan makarantan da aka sace daga baya a jihar Oyo.
Sun ce mutanen da aka sace sun ƙunshi mata da yara ƙanana yayin da wasu matan ke ɗauke da ɗanyen goyo.
Alhaji Abdul Ibrahim, wani wanda aka sace mutum talatin da biyar, kuma aka kashe goma daga cikin danginsa ya shaida wa BBC cewa "Mun haɗa kuɗi miliyan 155 mun kai wa ƴanbindigar, amman ba su amsa kuɗin ba, sun ce sun yi masu kaɗan sai komawa muka yi da su."
"Babu abin da za mu iya yi wanda ya wuce mu kai kukan mu ga gwamnatin tarayya da ta jihar Kwara domin su taimake mu, saboda ba mu da labarinsu tun bayan sace su sau biyu muka yi magana da su," in ji shi.
Sai dai biyan kuɗin fansa domin karɓo wanda ake garkuwa da shi laifi ne a dokokin Najeriya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ibrahim ya ce ƴanbingar sun shaida masu cewa idan har gwamanti ba ta yi abin da ya dace ba za su auri wasu daga cikin ƴan mata masu kyau daga cikin wadanda suka sacen, "Sun yi barazanar kashe sauran bayan sun zaɓi waɗanda suke so."
Alhaji Sulaiman Bukata, Dan Sadaukin Kaiama, daya daga cikin shugabanni al'umma, ya ce har zanga-zangar lumana suka gudanar kwanan nan kan wannan batu.
"Ba a kula da mutanenmu ba, saboda bayan sace su ne aka ɗauke na Oyo, amman gashi har an ceto su, amman ba wani ƙoƙari da gwamnati ta yi kan mutanenmu."
Al'ummar yankin sun yi kira ga hukumomin gwamnati da masu zaman kansu da su taimaka su kai masu ɗauki domin ganin an kuɓutar da mutanensu.
Honarabul Sa'idu Baba Ahmed, mai wakiltar yankin a majalisar dokokin jihar ta Kwara, ya shaida wa BBC cewa ya damu matuƙa saboda jinkirin kubutar da wadanda aka sacen.
"Idan mun tuntuɓi gwamnati suna fada mana suna aiki a kai, sai dai har yanzu shiru babu wani labari, saboda haka muna roƙon gwamnatin tarayy da ta ji tausayin yara ƙanana da mata masu ciki da goyo.

Najeriya na ci gaba da fuskantar matsalolin hare-haren yanbindiga kuma matsalar hare-haren ta fara ƙamari a jihar Kwara da ke tsakiyar Najeriya.
Ƙungiyoyin ƴanbindigar sun fi ƙarfi a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, baya ga mayakan Boko Haram da Iswap da suka addabi yankin arewa maso gabashi.
Akwai ƙungiyoyin mahara sama da 100 da suke aika-aikar, kamar kai hare-hare da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa da sauransu.
Masana sun ce ƙungiyoyin suna ƙara samun ƙarfi ne saboda talauci da rashin aikin yi, sannan sun fara ne da satar shanu da ƙananan rikice-rikice, kafin ayyukansu suka ta'azzara tare da faɗaɗa.












