Yadda dillalan miyagun ƙwayoyin Mexico suka kafa cibiya a Najeriya

Anti drug officers inspect a site allegedly used as a clandestine methamphetamine laboratory - Ogun state, Nigeria - 22 July 2026.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jami'an hana sha ta fataucin miyagun ƙwayoyi na duba wurin sarrafa ƙwayar a tsakiyar dajin jihar Ogun
    • Marubuci, Simi Jolaoso
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Africa correspondent
    • Aiko rahoto daga, Ogun state
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Alƙalin Najeriya sanye da tufafin shari'a yadda ya kamata, lauyoyi kuma sun bi ƙa'idoji da ladubban kotu, tare da gudanar da zaman bisa doka.

Sai dai wannan shari'ar ba a yi ta a cikin daɗi a zauren kotun Legas ba, a maimakon haka an gudanar da ita ne a cikin wani ɗakin gwaje-gwaje da ake zargin ana sarrafa miyagun ƙwayoyi a cikinsa, wanda ke tsakiyar wani daji mai duhu.

An gurfanar da wasu ƴan Mexico uku da ƴan Najeriya bakwai, hannayensu ɗaure da ankwa, yayin da mai shari'a Musa Kakaki ke duba sinadarai da kayan aiki, an zarge su da yin amfani da su wajen sarrafa miyagun ƙwayoyi da sinadarin methamphetamine, da aka fi sani da meth.

Wani wari mai shiga numfashi, ya mamaye ilahirin ɗakin gwaje-gwajen na wucin-gadi, wanda ke fitowa daga wani ƙaton mazubi cike da sinadarin sarrafa ƙwayoyin, wanda ake cikin sarrafawa.

Haka kuma akwai wani warin da ke fitowa daga wasu kwantenoni da aka buɗe, waɗanda ke ɗauke da wani ruwa mai kauri da danƙo, wanda masu aiki a wurin suka bayyana a matsayin ''ɗanyen'' ruwan sinadarin methamphetamine, wanda har yanzu ba a kammala sarrafa shi ba.

Akwai kuma wasu kayyaki da ke baje a gefen ɗakin, ciki har da tukwanen gas da jakankunan soda da kuma wasu gine-gine da ba a kammala ba.

Wannan mataki da Kotun Tarayya ta ɗauka na gudanar da zaman wucin-gadi a wani wuri da ke da tazarar kusan tafiyar mota ta awa biyu daga Legas, abu ne da ba a saba gani ba a tsarin shari'ar Najeriya.

Sai dai Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta ce hakan ya zama dole domin a fahimci girman wannan shari'a

A lokacin da aka kama waɗanda ake zargin a watan Mayu, hukumar ta bayyana lamarin a matsayin mafi girman kama miyagun ƙwayar methamphetamine da aka taɓa yi a tarihin ƙasar.

Ta ce ta gano fiye da tan biyu na ƙwayar, waɗanda kuɗinsu ya kai kimanin dala miliyan 360.

A lokacin, NDLEA ta sanar cewa ta "yi wani babban kamu kan masu safarar miyagun ƙwayoyi", tare da rusa wata "ƙungiyar Najeriya da Mexico mai ƙarfi da ƙwarewa fasaha, da ke samar da methamphetamine''.

A series of blue plastic buckets lined up. Inside each bucket is a grey sludge.
Bayanan hoto, Akwai alamun da ke nuna cewa an yi wa masana'antar illa sosai
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan wata guda, jami'an sun sake gano wani ɗakin gwaje-gwaje da ake sarrafa Meth boye cikin wani daji a jihar Oyo.

A wannan lokaci sun kama mutum 5, ciki har da ɗan Mexico ɗaya, wanda ƙwararren mai sarrafa sinadarin methamphetamine ne.

Wannan samamen ya nuna wani yanayi da ke ƙara ƙamari, wato yadda Afirka, musamman Afirka ta Yamma, ke ƙara taka muhimmiyar rawa a kasuwancin miyagun ƙwayoyi a duniya.

Haka kuma yana nuna yadda ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke sauya salon aikinsu, inda ba wai kawai suke amfani da nahiyar a matsayin hanyar wucewa da miyagun ƙwayoyin ba, har ma a matsayin cibiyar sarrafa su.

A cewar hukumomin yaƙi da laifuka da masu bin doka, ƙwararrun mutanen Mexico masu ƙera methamphetamine, waɗanda aka fi sani da "cooks", na ƙara bayyana, suna aiki tare da mutanen ƙasashen da abin ya shafa a ɗakunan gwaje-gwajen sarrafa miyagun ƙwayoyi a Turai da ma Afirka

Sarrafa sinadarin meth na ci gaba da ƙaruwa cikin gomman shekaru.

Rundunar sojin Amurka da ke kula da ayyukan soji a nahiyar Afirka, Africom ta samar wa hukumomin yaƙi da miyagun ƙwayoyi na ƙasashe da dama bayanan sirri domin taimaka musu wajen gudanar da samame da kama masu laifi.

"Duk wanda yake son amfani da methamphetamine ya san cewa methamphetamine ɗin da ake samarwa a Mexico shi ne mafi inganci a duniya domin wannan manufa," in ji James Griego shugaban sashen yaƙi da fataucin ƙwaya na rundunar sojin Amurka.

Karo na farko da NDLEA ta sanar da gano wani ɗakin gwaje-gwajen sarrafa methamphetamine da ke da alaƙa da mutanen Mexico shi ne a shekarar 2016, lokacin da ta bayyana wurin a matsayin wani "babban ɗakin gwaje-gwaje na zamani" (super lab).

An armed officer in khaki uniform and black stab vest stands guard in front of a makeshift room.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Zauren zaman kotun na wucin gadi, inda aka gabatar da wadanda ake zargin a ranar Laraba da shaidu.

Tuni aka gano irin waɗannan ɗakuna da ƴan Mexico ke amfani da su wajen sarrafa ƙwayoyi a ƙasashen Kenya da Mozambique da Afirka ta Kudu.

Tuyn shekarar 2023 zuwa yanzu "mun gano ɗakuna gwaje-gwaje 14 da ƴan Mexico ke amfani da su a Mozambique, a 2024 mun gano ƙarin shida yayin da a 2025 muka gano ƙarin biyar'', a cewar Griego.

"A wannan shekara kuma da muka gano biyar, huɗu daga cikinsu a Najeriya suke,'' in ji shi.

Bayanan sirri daga rundunar Africom da hukumar yaƙi da ƙwaya ta Amurka sun alaƙanta waɗannan wurare da aka gano a Najeriya da wasu manyan ƙungiyoyin dillalan ƙwaya na Mexico biyu: Gungun Sinaloa da kuma gungun Jalisco New General.

An aerial shot showing an expanse of green forest with a compound of buildings in the middle surrounded by a wall.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Cibiyar sarrafara ƙwayar na can ɓoye cikin daji

Afirka ta Yamma na da abubuwa da dama da ke jan hankalin ƙungiyoyin masu safarar ƙwayoyi na Mexico.

Daga ciki akwai dazuzzuka masu yawa, waɗanda suka dace da kafa wuraren sarrafa miyagun ƙwayoyi a ɓoye ba tare da an gano su cikin sauƙi ba.

"Yawan al'ummar yankin ma na daga cikin abubuwan da ke jan hankalinsu, musamman yadda ake da matasa masu yawa. Hakan na nufin za a iya samun sauƙin ɗaukar ma'aikata da za su yi aikin cikin kuɗi mai sauƙi da kuma kasuwar cikin gida da za ta iya amfani da miyagun ƙwayoyin," in ji kakakin NDLEA, Femi Babafemi, a wata hira da BBC

Akwai fargaba a tsakanin hukumomi cewa amfani da methamphetamine zai ƙara yawaita a Najeriya.

Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2018 ya nuna cewa kashi 14.4% na matasan ƙasar sun taɓa amfani da wani haramtaccen miyagun ƙwayoyi, adadin da ya ninka matsakaicin adadin duniya fiye da sau biyu, kamar yadda Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya Mai Yaki da Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) ta ƙiyasta.

A cewar ƙungiyar Global Initiative Against Transnational Organized Crime, amfani da wannan ƙwaya ya bazu a sassa daban-daban na nahiyar Afirka.

A Gabashin Afirka, wannan ƙwaya ta zama ruwan dare a ƙasashe irin su Kenya da Tanzaniya.

Haka kuma ta yaɗu a Kudancin Afirka, musamman a Afirka ta Kudu, inda ake kiranta da suna "tik".

Ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi ba su mayar da hankali ne kawai kan kasuwannin duniya ba, har ila yau suna da sha'awar kasuwannin cikin gida da ke ƙara bunƙasa.

Bugu da ƙari, matsayin da nahiyar Afirka take da shi a taswirar duniya na sauƙaƙa isa ga kasuwannin Asiya da Turai.

A concrete cylinder with a temperature gauge on the side sits in the middle of a room - pipes are coming out of the top and a grey tube is coming out of the bottom. Plastic sheeting can be seen in the place of a wall to the right.
Bayanan hoto, Wurin da dafa sinadarin domin saffara shi zuwa ƙwaya a masana'antar da ke dokar daji

Sarrafa miyagun ƙwayoyi a Afirka ta Yamma na bai wa masu safarar su damar amfani da hanyoyin jigilar kayayyaki na Tekun Atlantika.

Idan aka haɗa wannan da yadda iyakokin yankin ke da sauƙin ketarewa da kuma ƙarancin tsauraran dokoki kan shigo da sinadaran da ake amfani da su wajen ƙera miyagun ƙwayoyi, hakan na taimaka musu wajen rage kuɗaɗen gudanar da harkokinsu yayin da suke kai kayayyakin zuwa kasuwanni masu riba.

A Turai, Hukumar UNODC ta ce amfani da methamphetamine ya ƙaru da kashi 47 cikin 100 tsakanin shekarun 2014 da 2024.

A Gabashi da kudu maso gabashin Asiya kuma, yawan methamphetamine da hukumomi suka kama ya kai matakin da ba a taɓa gani ba a shekarar 2024.

"Wannan na rage musu tsawon hanyar da suke bi wajen kai kayan zuwa kasuwannin Asiya, haka kuma yana taƙaita hanyar shigarsu zuwa Turai," in ji Griego.