KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 11/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis 11 ga watan Yuni, 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • XXX
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Muslim Muhammad Yusuf da Usman MINJIBIR

  1. Ƴan asalin Najeriya 14 da za su buga kofin duniya a 2026

    Ƴan asalin Najeriya 14 da za su buga kofin duniya a 2026

    Asalin hoton, Getty Images

    Super Eagles ba ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026 da za a fara daga ranar 11 ga watan Yuni ba a Amurka da Canada da kuma Mexico.

    To sai dai tana da ƴan wasa 14 ƴan asalin Najeriya da za su wakilce ta da za a kara tsakanin kasashe 48 a karon farko a tarihin gasar.

    Saboda haka, kasa shiga gasar da Najeriya ta yi ta bana, bai hanata samun ƴan ƙwallonta da za su wakilce ta a babbar gasar tamaula ta duniya.

    Kenan Najeriya tana da wakilci na daban a gasar—wanda ba a kan sunan ƙasa kai tsaye bane—amma ta hanyar ƴan ƙwallo fiye da 14 masu asalin Najeriya da za su wakilci ƙasashe takwas daban-daban a gasar da za a gudanar.

  2. Hare-haren Amurka a Tehran sun jikkata mutum uku

    Hukumomi a Tehran sun ce mutum uku sun samu raunuka a harin da Amurka ta kai birnin.

    Kamfanin dillancin labaran ISNA ya ruwaito shugaban hukumar agajin gaggawa na Tehran na tabbatar da hakan.

    Baya ga hare-haren da Amurka ta kai a safiyar yau, an ji ƙarar fashe-fashe a wasu yankuna na Tehran da Karaj, Abiq, Qazvin, Varamin, Mallard, da Eshtehard.

  3. Iran da Amurka sun sake yi wa juna ruwan wuta

    Iran da Amurka sun yi wa juna ruwan wuta a karo na biyu

    Asalin hoton, Bahrain Interior Ministry/X

    Amurka da Iran sun sake yi wa juna ruwan wuta a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Wannan ce rana ta biyu da ƙasashen ke ci gaba da kaiwa juna hare-haren makamai masu linzami, duk da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma a watan Afrilu.

    Ma'aikatar tsaron Amurka ta ce ta samu nasarar kai hare-haren ramuwar gayya domin kare kanta daga Tehran, inda ta farmaki sansanonin sojin Iran da wasu cibiyoyin leƙen asiri a kudancin ƙasar.

    Wannan na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan Trump ya ce Iran za ta ɗanɗana kuɗarta sakamakon jan ƙafar da take yi wajen tattaunawa kawo ƙarshen yaƙin.

    Tehran ta mayar da martani ta hanyar ƙaddamar da hare-hare kan sansanonin sojin Amurka a yankin da ke Bahrain da Kuwait.

    Rundunar Juyin Juya Halin Iran ta ce ta harba makamai masu linzamu kan sansanin sojin Amurka da ke Jordan, kamar yadda kafar yaɗa labaran ƙasar ta ruwaito.

    Ta kuma ce talalata jiragen yaƙin Amurka masu tarin yawa a harin da ta harba makamai masu linzami 12.

    Kafar yaɗa labaran Jordan ta ruwaito cewa ƙasar ta kakkaɓo makamai masu linzami 20.

  4. Kotu ta umarci INEC ta yi wa Jam'iyyar Matasa rajista

    AUDU BULAMA BUKARTI

    Asalin hoton, AUDU BULAMA BUKARTI

    Kotun tarayya ta umurci INEC ta yi wa jam‘iyyar Access Party da ake kira da Jam'iyyar Matasa ta su Bulama Bukarti rajista.

    Wata kotun tarayya wadda da ke zamanta Abuja ce ta bayar da wannan umurnin, sannan ta umarci INEC ta ba jam'iyyar damar ƙarasa rajistarta.

    Jagororin jam'iyyar Dr. Audu Bulama-Bukarti da Mevon Samuel ne suka maka INEC a kotu a masanin jam'iyyar, bayan hukumar mai zaman kanta da ƙi amincewa da ita, inda ta kafa hujja da cewa tambarin jam'iyyar ya yi kama da tambarin wata jam'iyyar.

    Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun Mai shari'a Obiora Atuegwu Egwuatu na kotu a 11 ya ce hukumar ba ta da hurumin hakan, inda ya nanata cewa hukuncin ba daidai ba ne, kuma ya saɓa da shari'a kamar yadda kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 y tsara da kuma sashe na 79 na kundin zaɓe na 2022.

  5. Fitattun ƴan Najeriya da aka daɗe ana damawa da su a siyasar ƙasar

    ...

    Asalin hoton, OTHERS

    A tarihin Najeriya, an yi gwamnatoci da dama da suka yi mulki suka shuɗe. An yi juyin mulki dabam-daban, an yi jam'iyyu, sun yi tashe sannan suka ɓace, sannan shi kan shi kundin tsarin mulkin ƙasar ya sha sauye-sauye.

    Sai dai wani abu da yake ɗaukar hankali shi ne yadda wasu mutane suka daɗe suna taka rawa a siyasar ƙasar, lamarin da ya sa wasu matasan suke zargin an hana su samun damar shiga a dama da su a harkokin siyasar ƙasar.

    BBC ta suba wasu ƴansiyasa da suka fi daɗewa a fagehn siyasar ƙasar.

  6. Gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya sun lashi takobin kawar da talauci da matsalar tsaro

    ....

    Asalin hoton, Katsina Govt

    Gwamnonin yankin arewa maso yammacin Najeriya, sun fara yunƙurin aiwatar da wata manufar haɗin gwiwa da nufin shawo kan talauci mai fuskoki da dama ta hanyar shirye-shirye da dabarun tallafawa rayuwa a jihohin yankin bakwai.

    Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne bayan kammala wani taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Kano, inda suke fatan za su samar da dabarun da za su magance matsalolin yankin ciki har da batun yaran da basa zuwa makaranta.

    Gwamnoni dai sun hadu ne lokacin wani babban taron tsara manufa na wuni biyu a Kanon a kan matakan rage talauci ta hanyar bunƙasa shirye-shirye da dabarun samar da tallafin kuɗi don inganta rayuwa, wanda inuwar gwamnonin arewa maso yamma suka ɓullo da shi da haɗin gwiwar gwamnatin Najeriya da tallafin tarayyar turai da kuma asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya.

    Gwamnatin Kano itace mai masaukin baki, inda mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo, da ya wakilci gwamnan jihar ya shaida wa BBC cewa, akwai abubuwan da suka ja hankalin gwamnonin yankin da har aka shirya taron aka kuma gudanar da shi.

  7. Barka da Safiya!

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Alhamis.

    A wannan shafin namu na kai tsaye, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.