KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 6 ga watan Yunin 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. 'Trump bai so ya sake kai wa Iran hari ba'

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu jami’an gwamnatin Amurka sun ce shugaban ƙasar, Donald Trump, bai amince da buƙatar kai wa Iran harin ramuwar gayya ba sai da safiyar ranar Talata, kamar yadda ɗan jaridar Wall Street Journal, Alex Ward, ya ruwaito.

    A safiyar ranar Talata, Trump ya shaida wa Jaridar Wall Street Journal cewa harbo jirgin yaƙin Apache da Iran ta yi "ba wani babban al’amari ba ne", domin matuƙan jirgin sun tsira ba tare da sun samu raunuka ba.

    Sai dai rahoton ya ce daga baya shugaban ya sauya ra’ayinsa ne bayan Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, da shugaban rundunar hafsoshin tsaron ƙasa, Janar Dan Caine, sun ba shi shawarar ɗaukar matakin soja a wani taro da aka gudanar a Fadar White House.

    Daga ƙarshe, Trump ya amince da kai hare-hare kan wasu wurare a Iran a matsayin martani ga harbo jirgin yaƙin Apache, a cewar jami’an Amurka.

    Rahoton ya kuma ce bayan waɗannan hare-hare, rundunar juyin juya halin Iran da sojojin ƙasar sun ƙaddamar da sabbin hare-hare kan sansanonin sojojin Amurka da ke yankin.

  2. China ta buƙaci a rage tashin hankali a Gabas ta Tsakiya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasar China ta bayyana matukar damuwa kan rikice-rikicen da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya, tana mai kira ga ƙasashen da abin ya shafa da su kauce wa ƙara dagula al’amura.

    Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar, Lin Jian, ya ce ya kamata dukkan ɓangarorin su nuna haƙuri da kwantar da hankali, tare da ɗaukar matakai na gaskiya domin rage tashin hankali da gujewa faɗaɗa rikicin.

    Kiran na China ya zo ne bayan musayar hare-hare tsakanin Iran da Amurka, lamarin da ya ƙara tsananta damuwa a yankin baki daya.

  3. Iran ta kai harin makamai masu linzami kan sansanonin sojin Amurka uku

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomin labarai na Iran sun rawaito cewa rundunar juyin juya halin Musulunci (IRGC) ta kai hare-haren makamai masu linzami kan sansanonin sojojin Amurka guda uku da suka haɗa da Jordan da Bahrain da Kuwait.

    Iran dai ta harba aƙalla makamai masu linzami guda huɗu tare da wasu jirage marasa matuƙa da dama zuwa sansanonin sojojin Amurka ɗin.

    Wani jami'in Amurka ya tabbatar da harin, yayin da rahotanni suka ce an kai hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ta kai kan wasu wurare a Iran.

    A cewar IRGC, hare-haren sun kasance wani ɓangare ne na wata babbar martani inda suka yi iƙirarin kai hari kan wurare guda 21 na sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Haka kuma rahotanni sun nuna cewa sojojin Jordan sun ce sun kakkabo wasu daga cikin makaman da aka harba, ba tare da rahoton asarar rayuka ko lalacewar dukiya ba.

    Kafofin yada labarai na Iran sun kuma wallafa wasu bidiyo da suka ce suna nuna lokacin harin da kuma fashewar da ta biyo baya, amma har yanzu ba a tabbatar da ingancin wadannan bidiyoyin ba daga kafafen labarai masu zaman kansu.

  4. Assalamu alaikum

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Aisha Babangida ce za ta sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.