Yadda gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya suka lashi takobin kawar da talauci da matsalar tsaro

Wasu daga cikin gwamnonin arewa maso yammacin Najeriya

Asalin hoton, OTHER

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

a Najeriya gwamnonin yankin arewa maso yammacin ƙasar ne, suka fara yunƙurin aiwatar da wata manufar haɗin gwiwa da nufin shawo kan talauci mai fuskoki da dama ta hanyar shirye-shirye da dabarun tallafawa rayuwa a jihohin yankin bakwai.

Gwamnonin sun cimma wannan matsaya ne bayan kammala wani taron kwanaki biyu da suka gudanar a birnin Kano, inda suke fatan za su samar da dabarun da za su magance matsalolin yankin ciki har da batun yaran da basa zuwa makaranta.

Gwamnoni dai sun hadu ne lokacin wani babban taron tsara manufa na wuni biyu a Kanon a kan matakan rage talauci ta hanyar bunƙasa shirye-shirye da dabarun samar da tallafin kuɗi don inganta rayuwa, wanda inuwar gwamnonin arewa maso yamma suka ɓullo da shi da haɗin gwiwar gwamnatin Najeriya da tallafin tarayyar turai da kuma asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya.

Gwamnatin Kano itace mai masaukin baki, inda mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo, da ya wakilci gwamnan jihar ya shaida wa BBC cewa, akwai abubuwan da suka ja hankalin gwamnonin yankin da har aka shirya taron aka kuma gudanar da shi.

Ya ce,"mun ga cewa gara a hadu gaba daya domin a fito da sabbin dabaru na yakar talauci, domini dan abu ya yi yawa to dole sai an samu shawarwari daga masana da al'umma ta yadda za a fito da sabbin dabaru na magance duk wata matsala."

"Akwai abubuwa da dama da ke janyo talauci kamar yawan mutane a yankinmu na arewa maso yamma da yawan yaran da basa zuwa makaranta da tabarbarewar tsaro da na noma da ma rashin sana'oin dogaro da kai." In ji shi.

Mataimakin gwamnan Kano, y ace," A yayin taron an cimma matsaya akan yadda za a tallafawa bangaren ilimi sosai ta yadda kowanne yaro da ke yankin zai samu damar zuwa makatanta musammamma mata."

" Baya ga batun inganta ilimi a yankin na arewa maso yamma, an kuma cimma matsaya akan yadda za a inganta fannin lafiya da noma da ma tsaro, wanda yana daga cikin abin da yad amu gwamnoni da ma al'ummar yankin baki daya." In ji shi.

Murtala Sule Garo, y ace," Batun tallafawa matasa ma na daga cikin abubuwan da aka tabo a yayin taron, kuma da Zarar an cimma matsaya dukkan gwamnonin yankin za su sanya hannu da ma tara kudaden da za a yi amfani da su wajen cimma gaci."

Kwararru da dama dai sun halarci taron da kungiyoyin kasashen waje, inda aka tattauna tare da bayar da shawarwarin yadda za a magance talauci da matsalar yaran da basa zuwa makaranta a yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda ake fatan gwamnonin za su yi aiki tare.

Matsanancin talauci da rashin aikin yi musamman tsakanin matasa na daga cikin manyan dalilan da suka sa miliyoyin yara musamman 'yan mata ba sa zuwa makaranta a arewacin Najeriya, abin da kwararru da masu sharhi kan al'amuran yau da kullum ke shawartar gwamnatocin yankin da cewa lokaci ya yi da za su tashi tsaye su yi abubuwan da suka kamata ba kawai a yi taro a yi rubutu a takarda.