Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me takarar Mustapha Kwankwaso a jam'iyyar NDC ke nufi?
A ranar Litinin ne jam'iyyar NDC ta sanar da Mustapha Rabi'u Kwankwaso wanda ɗa ne ga tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, a matsayin mataimakin ɗan takarararta na gwamnan jihar Kano a zaɓen da ke tafe a 2027.
Sanarwar ta zo ne bayan kammala wata ganawa ta masu ruwa da tsaki a gidan jagoran jam'iyyar a Kano, Sanata Rabi'u Musa kwankwaso.
Mustapha Kwankwaso zai zama mataimaki ga Aminu Abdussalam Gwarzo wanda shi ne ɗan takarar gwamnan jihar ta Kano a jam'iyyar ta NDC.
Mustapha wanda shi ne babban ɗa ga jagoran na Kwankwasiyya ya riƙe kujerar kwamishinan matasa a gwamnatin Abba Kabir Yusuf.
Sai dai tun bayan sanarwar da jam'iyyar ta fitar ƴan siyasa da masu fashin baƙi ke ta tofa albarkacin bakinsu kan al'amarin da suke yi wa kallo da ba-sabun ba.
Me takarar Mustapha Kwankwaso ke nufi?
Malam Kabiru Sufi malami a kwalejin share fagen shiga jami'a a Kano wato CAS kuma masanin kimiyyar siyasa ya ce al'amarin yana da fuskoki daban-daban.
"Ya kamata a duba wasu abubuwa da suka haɗa da cewar Mustapha Rabi'u Musa kwankwaso ɗan ƙasa ne kuma yana da ƴancin tsayawa takara a kowane matsayi idan dai har ya cika sharruɗa," in ji shi.
To sai dai kuma malam Sufi ya ce baya ga abin da dokar ƙasa ta tanadar na cancanta ga dukkan ɗan ƙasa akwai kuma wasu abubuwan da ake dubawa musamman domin cire shakku daga zukatan ƴan jam'iyya da masu zaɓe.
"Akwai waɗanda kuma ba sa inkarin cewa ya cika sharuɗɗan sai dai akwai dalilai na siyasa da dalilai na mutuntaka da kuma dalilai na lura da al'amuran da ka je su zo da suke sa wasu ke ganin akwai alamun tambaya a kan al'amuran."
Ko takarar Mustapha za ta shafi nasarar jam'iyyar?
Dangane da faɗin da wasu ke yi cewa kasancewar ɗan gidan Kwankwaso ka iya sa tikitin takarar jam'iyyar ta NDC a Kano ya samu karɓuwa, Malam Sufi ya ce.
"Akwai masu duba cewa shin takarar tasa za ta ƙara wa tikitin jam'iyyar tagomashi ko kuma a'a, wanda akan hakan ma akwai ra'ayoyi guda biyu - akwai wadanda suke ganin sunan mahaifin nasa zai ƙara wa tikitin nasa tagomashi. Akwai kuma masu ganin ba haka ba ne."
Bugu da ƙari, Malam Sufi ya ƙara da cewa abin tsoron shi ne idan ƴan jam'iyya da masu zaɓe suka samu rashin gamsuwa da takarar bisa tuhumar cewa an yi tuwo na mai na a fitar da ƴan takara ko akwai damuwa.
"Akwai kuma masu ganin an yi abin da ake kira 'nepotism' wato tuwo na mai na kuma hakan ka iya raunana takarar da rashin samun karɓuwa a wurin ƴan jam'iyya da jama'ar gari masu zaɓe," in ji Malam Kabiru Sufi.
Kwankwaso ne ya fara tsayar da ɗansa takara?
Ba tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso ne ɗan siyasar da ya fara tsayar da ɗansa takara a jihar Kano da ma Najeriya ba.
Sai dai wataƙila abin da ya sa jama'a suka yi masa ca ba zai rasa nasaba da irin kalaman sukar tuwo na mai na da Kwankwason ya yi a baya ba.
"Duk da dai idan aka tsaya aka kalli al'amarin za a ga ba Kwankwaso ba ne mutumin da ya fara tsayar da ɗansa ba. An yi shi a jihohi da dama inda shugabannin al'umma suka saka ƴaƴansu ko ƴan uwansu ko kuma surukansu takara. Kuma wasu sun kai ga nasara wasu kuma ba su kai ba.
"Ko da shi Sanata Rabi'u Musa kwankwaso a baya ya sha ƙalubalatar wasu da suka yi haka ɗin da kuma danta rashin nasara da abin da suka yin.
"Idan muka duba za mu ga ko a Kanon an samu a jam'iyyar PDP a zaɓen da ya gabata. An gani a jam'iyyar PDP ɗin a jihar Jigawa a zaɓuka biyu da suka gabata. Mun gani a jihar Sokoto da Zamfara a baya," in ji Malam Kabiru Sufi.