Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abu 4 da INEC ta haramta game da kamfe a wuraren ibada
Yayin da jam'iyyun siyasa da 'yan takara ke ci gaba da yaƙin neman zaɓen shugaban kasa a zaɓen 2027 da ke tafe, hukumar zaɓen ƙasar INEC, ta sake jan kunnen masu ruwa da tsaki kan wasu dokoki da suka shafi yaƙin neman zaɓe.
Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da dokokin zaɓen ƙasar suka tanada shi ne hana amfani da wuraren ibada, ciki har da masallatai da coci-coci, wajen gudanar da harkokin kamfen na siyasa.
INEC na cewa wannan mataki na da nufin kare wuraren ibada daga rikice-rikicen siyasa tare da tabbatar da cewa ba a amfani da addini wajen neman ƙuri'un masu zaɓe ba.
Dokokin na INEC sun hana aiwatar da wasu abubuwa a wuraren ibadar don guje wa samun rikicin addini.
Mun duba dokokin zaɓen da aka yi wa gyaran fuska a 2026, inda muka tattaro muhimman abubuwa 5 biyar da INEC ta haramta dangane da yaƙin neman zaɓe a masallatai da coci-coci, da kuma dalilan da suka sa aka kafa waɗannan dokoki.
Shirya gangamin siyasa
Dokar ta haramta shirya tarukan gangamin siyasa ko tarurrukan neman goyon bayan masu zaɓe a masallatai da coci-coci.
Ƴansiyasa kan yi amfani da wuraren tarukan jama'a, kamar wuraren ɗaurin aure ko raɗin suna wajen tallata kansu ko jam'iyyunsu, ko kuma yantakarar da suke goyon baya.
Amma INEC ta ce yin hakan a masallatai kjo coci-coci babban laifi ne da doka yta haramta.
Hakan na da nufin hana rikicin siyasa shiga cikin al'ummomin addini.
Jerin gwanon siyasa a harabar wuraren ibada
'Yan siyasa ko magoya bayansu ba su da izinin yin jerin gwano ko wasu ayyukan da ke nuna kamfen a wuraren ibada ba a cewar dokar.
INEC na ganin hakan na iya haddasa rabuwar kai ko takun-saka tsakanin mabiya addinai.
Ƴansiyasa a Najeriya dai kan shirya jerin gwano a wasu wurare da nufin tallata jam'iyyunsu ko ƴantakararsu.
Tallata jam'iyyar siyasa ko ɗan takara a mimbari
Dokar ta hana amfani da hudubobi, ko wa'azi ko jawabai a wuraren ibada domin tallata wata jam'iyya ko ɗan takara ko neman a zaɓe shi.
Wannan mataki na kare wuraren ibada daga zama dandamalin neman ƙuri'u.
A baya-bayan nan dai ana ganin yadda wasu malamai ke amfani da mimbarinsu wajen tallata wasu ƴantakara ko jam'iyyun siyasa a Najeriya.
Wani abu da wasu ke ganin zai iya haifar da raguwar ƙimar malaman a idanun mabiyansu.
Sukar jam'iyyun adawa da manufofinsu
INEC ta kuma haramta amfani da wuraren ibada wajen kushewa ko sukar wata jam'iyya ko ɗan takara ko manufofinsu.
Dokar ta yi tanadin cewa wani ɗan siyasa ko wata jham'iyya ta yi amfani da wuraren ibadar wajen sukar abokan hamayyarsu ba.
Masu lura da al'amura na cewa hakan na taimakawa wajen rage tada zaune-tsaye da kuma kare haɗin kan mabiya addinai.
Waɗannan dokokin INEC na nufin tabbatar da cewa addini da siyasa sun kasance a matsayin abubuwa biyu mabambanta, tare da kare wuraren ibada daga tasirin rikice-rikicen siyasa da kuma tabbatar da adalci ga dukkan jam'iyyu da 'yan takara.
Ko wannan ya ci karo da ƴancin ɗan'adam?
Barista Nuhu Hamza Dantani lauya mai zaman kansa kuma mai rajin kare haƙƙin ɗan'adam ya ce waɗannan dokoki d aINECta gindaya ba su ci karo da ƴancin ɗan'adam da kundin tsarin mulkin Najeriya ya tanadar ba.
'"Shi ƴancin ɗan'adam yanci ne da yake da iyaka, akwai wanda za ka iya kafa hujja da shi, akwai kuma wanda ba za ka iya kafa hujja da shi ba'', in ji shi.
Masanin dokokin Najeriyar ya ce sashe na 45 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da iyaka game da yancin na ɗan'adam.
''Ita kuma INEC, sashe na 153 na dokokinta sun ba ta damar tsarawa da gudanar da zabe cikin zaman lafiya da tsari ta yadda za ta iya kawo ingantaccen zaɓe ga al'umma''.
Ya ci gaba da cewa idan INEC ta lura cewa taron siyasa ko kamfe a wuraren ibada zai kawo tarzoma cikin al'umma to ka ga ya kamata ta hana.
''Don haka idan har akwai yiwuwar samun rikici to ƴancin ɗan'adam ɗin yana da iyaka a nan'', in ji .
''Don haka ni a fahimta ta hakan bai ci karo da ƴancin ɗan'adam ba'', kamar yadda ya ce
Mene ne hikimar keɓance wuraren ibada da kamfe?
Wasu yan ƙasar da dama na mamakin yadda INEC ta sanya ƙa'idar yaƙin neman zaɓe a wuraren ibada.
Sai dai Barista Nuhu Dantani ya ce Najeriya ƙasa ce da addini ke da matuƙar tasiri a cikinta.
''To kuma ka ga siyasa abu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya, wataƙila idan aka yi kamfe a wuraren ibada hakan zai iya tayar da hargitsi da shafar zaman lafiyar ƙasar da mabiya addinai daban-daban'', in ji lauyan.