Abin da ya kamata ku sani kan Gasar Kofin Afirka ta mata ta 2026

Kyaftin Rasheedat Ajibade lokacin da ta ɗaga kofin

Asalin hoton, Backpage Pix

Bayanan hoto, Najeriya ta sake kafa tarihin cin gasar kofin nahiyar Afrika ta Mata karo na 10 da aka yi a Rabat a watan Yuli
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 9

Duk da an samu jinkiri, amma a ƙarshe dai za a fara gasar kofin Nahiyar Afrika ta Mata ta 2026, wadda Morocco take zuwa wasan ƙarshe karo na uku a jere.

Kamata ya yi a fara gasar ranar 17 ga watan Maris zuwa 3 ga watan Afrilu, amma daga baya Hukumar Kwallon Kafa ta Afrika, Caf ta ɗage gasar ana saura kwana 12 a fara.

Wafcon ɗin wannan shekarar da ke zuwa wata 12 kacal bayan jinkirin ta 2024, za a fara ta ne a ranar Lahadi 26 ga watan Yuli, inda Algeria da Senegal za su fara wasan farko a Rabat.

Caf ta ce wasu abubuwa da suka taso babu tsammani ne suka suka haifar da ɗage gasar, amma hakan na da alaƙa da faɗaɗa gasar da aka yi zuwa tawaga 16, kuma za a yi wasa 34, inda za a yi wasan ƙarshe ranar 16 ga watan Agustan.

Wannan shekarar na da muhimmanci saboda an nunka waɗanda za su samu tikitin Gasar Duniya ta Mata da za a yi 2027, ƙasashe huɗu da za su je wasan kusa da ƙarshe duka za su samu tikitin gasar da za a yi a Brazil.

Su kuma huɗun da aka cinye a wasan kusa da dab da na ƙarshe za su fafata da junansu domin samun cikon biyu da za su je gasar da su.

Mene ne abubuwa da suke da muhimmanci da ya kamata mu sani? Wanne salo za a yi amfani da shi a gasar? A ina za a buga wasannin kuma yaushe za a fara gasar?

Bangaren wasannin BBC Afirka ya tattaro muku duk bayanan da suka kamata ku sani a gasar da za a fara karo na 14 a tarihi.

Yadda aka raba rukuni

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tawagogi 16 aka raba zuwa rukuni huɗu mai ɗauke da tawagogi huɗu-huɗu.

A rukuni na ɗaya za a yi wasan hamayya tsakanin Morocco da ke Arewacin Afirka da takwararta Aljeriya, kazalika za a yi tsakanin Senegal da Kenya waɗanda suka dawo tun bayan zuwan su gasar shekara 10 baya.

Najeriya da ke riƙe da kofin take fatan lashe shi a karo na 11, ta kasance tare da Zambia a rukunin C, Malawi da ta fara zuwa za ta kara da Masar.

Afirka ta Kudu da ta lashe gasar a 2022 za ta fafata da Ivory Coast, Burkina Faso da Tanzania a rukunin B.

An haɗa Ghana da Kamaru a Rukunin D da kuma Mali - kasashen biyu da suka je wasan ƙarshe da suke ƙara ƙarfafa kwarewarsu a duniya - sai kuma Cape Verde da ta zo gasar a karon farko.

Kungiyoyi biyun da suka ƙare a saman kowanne rukuni za su kai matakin kwata-fainal.

Rukunin A: Morocco (masu masaukin baƙi ), Algeria, Senegal, Kenya

Rukunin B: Afirka ta Kudu, Ivory Coast, Burkina Faso, Tanzania

Rukunin C: Najeriya (mai rike da kofin), Zambia, Masar, Malawi

RukuninD: Ghana, Kamaru, Mali, Cape Verde

Lokacin da za a fara wasannin Wafcon 2026 da yadda aka tsara su

Za a riƙa fara wasannin ne ƙarfe 17:00 agogon GMT da 20:00 GMT a duka gasar - kuma haka ake sa ran wasan ƙarshe zai kasance.

Za a yi wasan kusa da dab da na ƙarshe ne a ranar 8 da kuma 9 ga watan Agusta, haka su ma wasannin kusa da na ƙarshe a ranar 12 ga watan.

Za a yi wasan ƙarshe ranar Lahadi, 16 ga watan Agusta da ƙarfe 19:00 agogon GMT.

Ina ne wuraren da za a yi wasannin Wafcon 2026?

Filin wasa Moulay Hassan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin wasa Moulay Hassan, wamda aka yi wasa hudu a cikinsa a 2025, yanzu za a yi wasannin rukuni a ciki da kuma wasan ƙarshe.

A bara Morocco ta yi amfani da filayen wasa shida a birane biyar domin bakuncin gasar, amma a wannan karon filaye biyar za a yi amfani da su a birane biyu.

Za a riƙa wasannin ne a babban birnin ƙasar Rabat da Casablanca, a yi amfani da filin wasa na Berkane Mohammedia da Oujda.

A birnin Fez 'yan Rukunin G za su yi wasanninsu, amma wasannin da aka tsara za a yi a filin wasa na Sportif de Fes yanzu duk an mayar da su Casablanca.

Filayen wasa uku da aka yi amfani da su a Afcon 2025 yanzu ana yi musu gyare-gyare saboda shirin Morocco na karɓar baƙuncin Kofin Duniya na 2030.

Atlass Lionesses za su yi wasansu ne a filin wasa na Moulay Hassan, inda za a yi wasannin kwata-fainal da na kusa da ƙarshe.

Har yanzu ba a tabbatar da a inda za a yi wasan ƙarshe ba. Amma dai a tsakanin Filin wasa na Moulay Hassan ko kuma na Yarima Moulay Abdellah dukkan su a Rabat, inda a nan ne a ka yi wasan ƙarshe na gasar Afcon.

Ga filayen wasannin da aka tabbatar za a yi amfani da su:

  • Filin wasa na Moulay Hassan Stadium, Rabat
  • Filin wasa na Olympic Stadium, Rabat
  • Filin wasa na Al Medina Stadium, Rabat
  • Filin wasa na Larbi Zaouli Stadium, Casablanca
  • Filin wasa na Moulay Rachid Stadium, Casablanca

Waɗanne ƙasashe ake tsammanin za su iya lashe kofin?

Ghizlane Chebbak na murnar ɗaya daga cikin kwallayen da ta ci.

Asalin hoton, Backpage Pix

Bayanan hoto, Kyaftin ɗin Morocco Ghizlane Chebbak daga hagu ita ce ta lashe kyautar wadda ta fi zura kwallaye a 2024, inda ta ci kwallo biyar.

A cikin ƙasashe 16 da za su fafata a gasar Najeriya da Afrika ta Kudu ne kawai suka taɓa ɗaukar kofin.

Super Falcons ta Najeriya za ta ƙara halartar gasar a matsayin mai rike da kofin da kuma wadda ake tsammanin za ta iya ƙara lashe kofin, yayin da mai horarwar da ya jagorance su suka ci kofin a baya ɗan ƙasar, Justin Madugu zai ƙara zuwa da su.

Chiamaka Nnadozie ita aka bai wa kyautar mai tsaron ragar da ta fi kowacce kuma kusan shekaru uku tana cin kyautar, yayin da kyaftin Rasheedat Ajibade ta zama wadda ta fi kowacce 'yar wasa ƙwazo a gasar.

Morocco suna ci gaba da zuba kuɗi kan harkokin wasannin kwallon kafa a 'yan shekarun nan, sai dai ɓangaren matan ƙasar har yanzu ya gaza yin irin abun da na maza ke yi, da kuma yadda ta zama tawagar da ta fi kowacce a Afrika.

Da Morocco ake wasan ƙarshe na gasar shekaru biyu da suka gabata, amma har yanzu shiru.

Afirka ta Kudu, ita ce tawaga ta biyu a nahiyar, har yanzu suna jin dadin abin da ya faru lokacin mai horaswa Desiree Ellis, za ta dawo gasar ne a matsayin wacce ta je matsayi na uku a watan Yulin bara.

Zambia ana sa ran su ma za su iya taka rawar gani, duk da cewa tawagar ta Copper Queens ta sha kashi a hannun Najeriya da ci 5-0 a wasan kwata-fainal a bara. Za su iya zarce burin Babra Banda da aka bai wa kyautar mace da ta fi kowacce taka leda a shekarar 2024 a kyautar BBC.

Duk wanda zai yi wasa da su zai iya fuskantar ƙalubalen da ba a yi tsammani ba.

Tsarin wasannin Wafcon 2026

Racheal Kundananji da Barbra Banda,

Asalin hoton, Backpage Pix

Bayanan hoto, 'Yan wasan Zambia Racheal Kundananji (daga hagu) da kuma Barbra Banda (daga dama) dukansu sun ci kwallo uku-uku a matakin rukuni sai dai an cire su a wasan kwata-fainal

Duka wasannin da za a yi a tsarin agogon GMT.

Lahadi, 26 Yuli

Rukunin A: Algeria v Senegal, filin wasa na Olympic Stadium, Rabat, (17:00 GMT)

Rukunin A: Morocco v Kenya, filin wasa na Moulay Hassan Stadium, Rabat, (20:00 GMT)

Litinin, 27 Yuli

Rukunin B: Afirka ta Kudu v Tanzania, filin wasa na Moulay Rachid Stadium, Casablanca, (17:00 GMT)

RukuninB: Ivory Coast v Burkina Faso, filin wasa na Larbi Zaouli Stadium, Casablanca, (20:00 GMT)

Talata, 28 Yuli

Rukunin C: Zambia v Masar, Olympic Stadium, (17:00 GMT)

Rukunin C: Najeriya v Malawi, filin wasa na Al Medina Stadium, Rabat, (20:00 GMT)

Laraba, 29 Yuli

Rukunin D: Ghana v Cape Verde, filin wasa na Moulay Rachid Stadium, (17:00 GMT)

Rukunin D: Kamaru vs Mali, filin wasa na Larbi Zaouli Stadium, (20:00 GMT)

Alhamis, 30 Yuli

Rukunin A: Senegal v Kenya, filin wasa na Olympic Stadium, (17:00 GMT)

Rukunin A: Morocco v Algeria, filin wasa na Moulay Hassan, (20:00 GMT)

Juma'a, 31 Yuli

Rukunin B: Afirka ta Kudu v Ivory Coast, filin wasa na Moulay Rachid, (17:00 GMT)

Rukunin B: Burkina Faso v Tanzania, filin wasa na Larbi Zaouli, (20:00 GMT)

Asabar, 1 Agusta

Rukunin C: Masar v Malawi, filin wasa na Moulay Hassan, (17:00 GMT)

RukuninC: Nigeria v Zambia, Al Medina Stadium, (20:00 GMT)

Lahadi, 2 Agusta

Rukunin D: Ghana v Cameroon, Moulay Rachid Stadium, (17:00 GMT)

Rukunin D: Mali v Cape Verde, Larbi Zaouli, (20:00 GMT)

Temwa Chawinga,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Temwa Chawinga 'yar Malawi za ta fara wasanta da ƙasar na Wafcon a Morocco

Litinin, 3 Agusta

Rukunin A: Senegal v Morocco, Moulay Hassan Stadium, (20:00 GMT)

Rukunin A: Kenya v Algeria, Olympic Stadium, (20:00 GMT)

Talata, 4 Agusta

Rukunin B: Burkina Faso v South Africa, Moulay Rachid Stadium, (20:00 GMT)

Rukunin B: Tanzania v Ivory Coast, Larbi Zaouli Stadium, (20:00 GMT)

Laraba, 5 Agusta

Rukunin C: Egypt v Najeriya, Olympic Stadium, (20:00 GMT)

Rukunin C: Malawi v Zambia, Al Medina Stadium, (20:00 GMT)

Alhamis, 6 Agusta

Rukunin D: Mali v Ghana, Moulay Rachid Stadium, (20:00 GMT)

Rukunin D: Cape Verde v Kamaru, Larbi Zaouli Stadium, (20:00 GMT)

Wasannin dab da kusa da na ƙarshe na Wafcon 2026

Linda Motlhalo,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Linda Motlhalo ta ci kwallo biyu a gasar Wafcon 2024 da Afrika ta Kudu ta zo matsayi na huɗu

Asabar, 8 Agusta

QF 2: Wadda ta yi ta ɗaya a Rukunin B v Wadda ta yi ta biyu a Rukunin A, filin wasa na Moulay Rachid, (17:00 GMT)

QF 1: Wadda ta yi ta ɗaya a Rukunin A v Wadda ta yi ta biyu a Rukunin B, filin wasa na Moulay Hassan, (20:00 GMT)

Lahadi, 9 Agusta

QF 4: Wadda ta yi ta ɗaya a Rukunin D v Wadda ta yi ta biyu a Rukunin C, filin wasa na Larbi Zaouli , (17:00 GMT)

QF 3: Wadda ta yi ta ɗaya a Rukunin C v Wadda ta yi ta biyu a Rukunin D, filin wasa na Al Medina, (20:00 GMT)

Wasan kusa da na ƙarshe na Wafcon 2026

Cynthia Konlan

Asalin hoton, Confederation of African Football

Bayanan hoto, Mai tsaron ragar Ghana Cynthia Konlan ta buge fenariti biyu a wasansu da Algeria wasan 'yan takwas Wafcon 2024

Laraba, 12 Agusta

SF2: Wadda ta yi nasara QF2 v Wadda ta yi nasara QF3, filin wasa na Olympic, (17:00 GMT)

SF1: Wadda ta yi nasara QF1 v Wadda ta yi nasara QF4, filin wasa na Moulay Hassan, (20:00 GMT)

Wasannin neman gurbin gasar duniya ta mata ta 2027

Alhamis, 13 Agusta

Wadda ta yi rashin nasara QF2 v wadda ta yi rashin nasara QF3, filin wasa na Larbi Zaouli, (17:00 GMT)

Wadda ta yi rashin nasara QF1 v wadda ta yi rashin nasarar QF4, filin wasa na Moulay Rachid, (20:00 GMT)

Neman na uku

Asabar, 15 Agusta

Wadda ta yi nasara SF1 v wadda ta yi rashin nasara SF2, filin wasa na Olympic, (17:00 GMT)

Wasan ƙarshe

'Yan wasan Najeriya Michelle Alozie da Jennifer Echegini,

Asalin hoton, Backpage Pix

Bayanan hoto, Jennifer Echegini (daga dama) da ta shigo a benci ta ci kwallo a minti na 88 a wasan karshe na Wafcon 2024 kan mai masaukin baƙi Morocco

Lahadi, 16 Agusta

Wadda ta yi nasara SF1 v Wadda ta yi nasara SF2, a filin wasa na Moulay Hassan Stadium ko Yarima Moulay Abdellah, Rabat, (19:00 GMT).