Abin da muka sani kan sansanin sojin saman Jordan da Iran ke kai wa hari

Asalin hoton, Getty Images
Sansanin sojin sama na 'Muwaffaq Al-Salti' wanda aka fi sani da sansanin sojin sama na Azraq, na daga cikin sansanin soji mai matuƙar muhimmanci a ƙasar Jordan.
Wata muhimmiyar cibiya ce ta ayyukan rundunar sojin sama ta ƙasar Jordan, sannan a baya-bayan nan wurin ya ƙara samun martaba a kuma yana taka muhimmiyar rawa a harkar tsaro a Gabas ta Tsakiya.
Wurin ya zamo babban abin da ke jan hankali a kwanan nan bayan sake ɓarkewar yaƙi a Gabas ta Tsakiya, inda rahotannin suka ce ana amfani da shi a matsayin sansanin hadin gwiwa na ayyukan soji tsakanin Jordan da Amurka da kuma sauran ƙasashe masu ƙawance, sai dai ƙasar Jordan ta tabbatar cewa sansanin na rundunar sojinta ne.
Cibiyar ayyukan soji ta Amurka ta sanar cewa a ranar Asabar sojojinta biyu sun mutu sannan ba a ga guda ɗaya ba a lokacin da suke aikin kwance ɗamarar wani makami mai linzami na Iran.
Wata sanarwa da cibiyar ayyukan sojin na Amurka CENTCOM ta fitar ta ce an kashe sojoji biyu a ranar Juma'a a bakin aiki a ayyukan da dakarunta ke yi tare da haɗin gwiwar ƙawayenta wajen daƙile hare-haren Iran.
A ranar Juma'a kuma Dakarun juyin juya hali na Iran sun sanar cewa sun kai farmaki kan tankokin mai a sansanin soji na Azraq da ke Jordan.
Kafafen yada labarai na Iran sun ruwaito cewa dakarun Iran sun yi amafani da makamai masu linzami da kuma jirage marasa matuƙa wajen kai harin.
Wuri mai muhimmanci a tsakiyar rairayi
Sansanin yana a yankin Azraq, kimanin kilomita 100 arewa maso gabashin Amman, babban birnin ƙasar, kuma sansani ne da ke a wurin da yake ba shi damar lura da yanki mai fadi na sararin samaniyar ƙasar ta Jordan da kuma iyakokinta na gabas da arewa.
An samar da sansanin ne tun shekarar 1918, lokacin da wani sojan Birtanya, Thomas Edward Lawrence ya yi amfani da yankin a matsayin sansanin soji domin amfani da yankin arewaci mai yawan ciyayi a matsayin wurin yada zangon jiragen da ke kan hanya zuwa Daraa a lokacin boren Larabawa.
Wurin yana da kyawun yanayi kuma yana da sauƙin shawagi ga jirage.
A shekarar 1981 an sanya wa sansanin suna wani jami'in soji, laftanar Muwaffaq al-Salti domin karrama shi, wanda aka kashe a wani yaƙin sama da dakarun Isra'ila a ranar 13 ga watan Nuwamban 1966.
Sansanin soji mafi girma a Jordan
Rundunar sojin ƙasar Jordan ta ce sansanin Muwaffaq al-Salti shi ne mafi girma a Jordan, inda ya mamaye kimanin murabba'in kilomita 35, kuma ya ƙunshi dakarun sojojin ko ta kwana, da masu kula da na'urori da kuma garkuwa daga hare-haren jiragen sama.
A sansanin akwai jiragen yaki samfurin F-16 mallakin dakarun sojin sama na Jordan, wanda ya zama ginshiƙi ga ayyukan dakarun sama na Jordan tun daga shekarun 1990.
Ayyukan sansanin ba su taƙaita kan sojin sama ba, ana gudanar da wasu ayyuka na kula da kuma zamanantar da jiragen saman yaƙi samfurin F-16.
Rundunar sojin sama ta Jordan ta tabbatar cewa ana iya gudanar da ayyuka masu wahala na gyaran jiragen yaƙi tare da hadin gwiwar hukumomi na Amurka, wanda hakan ke taimakawa wajen ƙara tsawon ran jiragen yaki.
Ana gudanar da ayyukan sojin ƙasashen ƙawance
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Sansanin ya ƙara ɗaukar hankalin duniya lokacin da aka tsananta wajen yaƙi da ƙungiyar Islamic State, inda rahotanni suka bayyana cewa dakarun Amurka na amfani da shi wajen ayyukan ƙasashe masu ƙwance a lokacin.
Sansanin Muwaffaq Salti na daga cikin inda aka jibge sojojin Amurka a Jordan a ƙarƙashin wata yajejeniyar hadin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.
A baya-bayan nan ministan harkokin waje na Jordan Ayman Safadi ya bayyana cewa akwai dakarun Amurka a ƙasar ƙarƙashin yarjejeniyar da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Rahotannin kafofin da ke sanya ido kan ayyukan tsaro sun ce dakarun sama na Amurka sun yi amfani da sansanin wajen sauƙe sojojin lema da jiragensu da kuma jirage marasa matuƙa a shekarun baya-bayan nan.
Sai dai Amurka ba ta fayyace waɗanne irin dakarunta ko makamanta ne a sansanin ba, wanda hakan ya saɓa wa yadda aka saba game da sansanonin soji da ke yankin.
Sannan hotunan tauraron ɗan'adam da kamfanin dillancin labarai na Reuters sun nuna ƙaruwar jiragen soji a sansanin yayin da ake samun rikici a yankin, kuma Amurkar ba ta yi bayani kan hakan ba.












