Abin da ya janyo taƙaddama tsakanin Tinubu da Atiku

Tinubu/Atiku

Asalin hoton, Tinubu/Atiku/Facebook

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Da alama za a daɗe ba a kawo ƙarshen taƙaddamar da ke tsakanin fadar shugaban Najeriya Bola Tinubu da tsohon mataimakin shugaban ƙasar kuma ɗan takarar shugabancin Najeriya a zaɓen 2027 na jam'iyyar ADC Atiku Abubakar ba, inda dukkan ɓangarorin ke zargin juna da aikata rashawa da manyan laifuka.

Jayayya ta baya-bayan nan tsakanin ɓangarorin ta taso ne bayan da fadar shugaban Najeriya ta zargi tsohon mataimakin shugaban ƙasan da ƙoƙarin yin zagon ƙasa ga siyasar ƙasarsa ta hanyar ɗaukar masu taya shi neman shiga a wajen gwamnatin Amurka, tare da tayar da wasu batutuwa da a cewar ta, ''an riga an wuce zamanin su.''

Fadar shugaban Najeriyan ta ce rashin kishin ƙasa ne ya sanya tsohon mataimakin Atiku Abubakar ya ɗauki wasu masu yi wa mashi kamun ƙafa, waɗanda suka miƙa bayanai ga shugaban Amurka Dolnald Trump game da da zummar tayar da zargin da aka yi wa shugaba Tinubu tun a 1993.

Ta ce tun a wancan lokaci an riga an kammala shari'ar ba tare da samun shugaba Tinubu da laifi ba balle a hukunta shi, domin haka sake tayar da batun ba komai bane illa jirkita tarihi don cin gajiyar muradun wasu da ta kira ''marasa kishin ƙasa.''

To sai dai Atiku Abubakar wanda jigo ne a ɓangaren adawar siyasar Najeriya ya mayar da martani ga fadar shugaban Najeriyan, inda ya ce tayar da maganar tana da muhimmanci sosai saboda zai bayar da damar fayyace abin da ya janyo har ''kotu ta tilastawa shugaba Tinubu sallama wasu ƙaddarorin shi a wata shari'a kan badaƙalar ƙwayoyi.

Abdulrashid Uba Sharada, mai magana da yawun Atiku Abubakar ne, kuma ya ce wannan ai abu ne da ya kamata a yaba ''domin mu san cewa wane irin shugaba ne ya ke fadar shugaban ƙasa a yanzu, wanda mun tabbatar da cewa har yau shugaba Tinubu bai wanke kanshi ba.''

''Ina mai tabbatar maka babu wani batun rashin kishin ƙasa a nan, kuma mun gano suna yaudarar fadar White House da irin waɗannan ''lobyist'' sun kashe aƙalla dalar Amurka miliyan 10 domin a kashe wannan maganar,'' in ji Abdulrashid Sharada.

Amma fadar shugaban Najeriya ta ce yunƙurin na tsohon mataimakin shugaban ƙasar ba komai bane illa shure-shure saboda a cewar ta hatta takarar da Atiku Abubakar ya ɗauki tsawon shekaru yana yi ba komai bane illa neman kariyar diflomasiyya da kaucewa batutuwan shari'a a ƙasashen waje.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Abdulaziz Abdulaziz, ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Najeriya ya ce su a wajen su ''wannan abin mamaki ne da takaici domin ya za a ce kana neman yadda za ka ɓata sunan ƙasar ka a idon duniya domin kawai buƙatar mutum ta biya,''

''Kuma ba wai ya damu da jama'ar ƙasar bane, kawai dai burin sa shi ne ko ana ha-maza, ha-mata ya samu wannan mulki da yake nema,'' in ji Abdulaziz.

Fadar shugaban Najeriyan ta ce idan Atiku zai kashe har dala miliyan daya da dubu 200 wajen kamun kafa, a kai karar Tinubu, to kamata ya yi shi ma ya yi bayani kan halin shari'ar da yake ciki a Amurka.

Ta yi zargin cewa Atiku da tsohuwar matarsa Jennifer Douglas na cikin wadanda aka zarga a wani babban binciken Majalisar Dattijan Amurka na watan Fabrairun 2010. A binciken, in ji gwamnatin Nijeriya, bayanai sun nuna yadda Atiku ya yi amfani da wasu kamfanoni ya shigar da miliyoyin dalolin da ake zargi na cin hanci ne Amurka.

Amma Abdulrashid Sharada, mai magana da yawun Atiku Abubakar ya ce ko kusa babu gaskiya a zargin na fadar shugaban Najeriya.

''Ai tun da Alhaji Atiku Abubakar ya bar gwamnati babu wata kotu da ta taɓa kama shi da wani laifi ko ta yanke hukunci,'' in ji Sharada.

A halin da ake ciki dai, kowanne ɓangare na ci gaba da kare matsayar shi a kan wannan batu, kuma masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya na ganin cewa irin waɗan nan yarfe da cakulkuli ne zai mamaye yaƙin neman zabe a ƙasar, gabanin babban zaɓen 2027.

A gefe guda kuma akwai masu gani akwai buƙatar samun hukunci da zai fayyace gaskiyar zarge-zargen rashawa da na aikata sauran laifuka da ake yi wa ƴan siyasa a ƙasar.