Me ya sa jarirai ba su cika barci da daddare ba?

Asalin hoton, Getty Images
A gidaje da dama, musamman waɗanda aka yi wa sabon haihuwa, dare kan zama tamkar rana na gudanarwa maimakon hutu.
A yayin da iyaye ke fatan samun ɗan barci da hutu bayan gajiya ko dai aiki ko wani abu daban, jarirai kan fara kuka ko farkawa sau da dama, lamarin da ke sa iyaye su riƙa tambayar kansu ko hakan al'ada ce ko kuma alamar wata matsala.
Sai dai masana sun ce rashin yin dogon barci da daddare ga jarirai ba sabon abu ba ne.
Tun daga yadda kwakwalwarsu da jikinsu ke tasowa, zuwa yadda suke buƙatar shayarwa akai-akai, akwai dalilai da dama da ke sa jarirai su fi farkawa da daddare fiye da manya.
To amma me ya sa hakan ke faruwa? Kuma a wane lokaci ne ya kamata iyaye su fara damuwa?
Abin da ke faruwa
Dr Fatima Nasir Faskari, ƙwararriyar likitan yara ce a asibitin koyarwa da ke Katsina, ta bayyana cewa akwai wasu abubuwan gda uku da ke faruwa a cikin ƙwaƙwalwar yara da suke haifar da hakan lokaci bayan lokaci da suka haɗa da;
Ƙwaƙwalwarsu ba ta gama bunƙasa ba
Dr Fatima ta ce ƙwaƙwalwar jariri tana ci gaba da girma bayan haihuwa, don haka ba ta iya sarrafa barci kamar ta manya.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
"Kasancewar jarirai ƙwaƙwalwarsu ƙarama ce, wato ba ta gama girma ba. Shi ake da 'immature brain'."
A cewarta, wannan ne ya sa jarirai kan yi ta farkawa akai-akai maimakon yin dogon barci.
Ba sa iya bambance dare da rana
Likitar ta ce a cikin ƙwaƙwalwa akwai abin da ake kira 'internal clock', wanda ke taimaka wa mutum gane lokacin yin barci da lokacin farkawa.
Sai dai ta ce wannan tsarin bai gama bunƙasa ba a wajen jarirai.
"Su nasu bai girma ba, bai bunƙasa ba. To ba ta iya bambanta lokacin hasken rana da duhun dare."
Saboda haka, jariri na iya yin barci da rana sosai, sannan ya fi kasancewa a farke da daddare.
Sinadarin barci na melatonin bai gama samuwa ba
A cewar Dr Fatima, wani sinadari mai suna melatonin ne ke taimakawa jiki ya shirya yin barci idan dare ya yi bai gama samuwa yadda ya kamata a jikin jarirai ba.
"Shi sinadrin da yamma ne yake fitowa daga ƙwaƙwalwa, sai ya sa a fara jin barci. Su jarirai ba su da sinadarin baki ɗaya."
Har yanzu jarirai suna bin tsarin da suka saba tun suna cikin mahaifiya
Likitar ta ce kafin haihuwa, motsin da uwa ke yi da rana kan sa jariri ya yi barci a cikin mahaifa.
"Lokacin da suke cikin mahaifiyarsu da rana idan tana aikace-aikace, sai yaran su yi ta barci saboda suna ji ne kamar ana jijjiga su."
Da daddare kuwa, lokacin da motsi ya ragu, jaririn kan fi kasancewa a farke.
Ta ce wannan tsarin na iya ci gaba har bayan haihuwa, amma yawanci yana sauyawa tsakanin wata uku zuwa wata shida.
Yunwa na sa jarirai su riƙa farkawa
Dr Fatima ta ce wani babban dalilin farkawar jarirai da dare shi ne buƙatar shan nono ko cin abinci.
Saboda ƙananan cikinsu, ba sa iya cin abinci mai yawa da zai ɗauke su na dogon lokaci.
"Jarirai suna farkawa ne domin cin abinci ko shan nono. Kasancewar jikinsu ƙarami, sai ya zama abu kaɗan za su ci su ƙoshi wanda ba ya riƙe su na tsawon lokaci."
Ta ƙara da cewa idan suka farka, ba lallai ne su fara kuka nan take ba.
"Da zarar sun tashi za ka ga sun yi shiru na wani ɗan lokaci da ake kira 'quiet period'. Bayan sun ɗan yi shirun ne sai su fara koka-koke."
A cewar likitar, wannan yanayi na daga cikin abubuwan da ake tsammani a watannin farko na rayuwar jariri.
Abubuwan lura
Likitar ta ce duk da cewa farkawa da kuka da daddare al'ada ce ga yawancin jarirai, akwai wasu abubuwa da ya kamata iyaye su riƙa dubawa da zai buƙaci zuwa wajen likita kamar haka.
Idan jariri ya wuce wata shida amma har yanzu matsalar ta yi tsanani
Likitar ta ce yawancin jarirai kan fara samun daidaitaccen tsarin barci tsakanin wata shida zuwa shekara ɗaya.
Idan har bayan wannan lokaci jariri na ci gaba da yawan farkawa ko kuka ba tare da wani dalili a fili ba, yana da kyau iyaye su kai shi a duba.
Idan yana tare da zazzaɓi
Dr Fatima ta ce ya kamata iyaye su riƙa taɓa jikin jariri idan ya tashi yana kuka domin tabbatar da ko yana da zazzaɓi.
A cewarta, zazzaɓi na iya nuna cewa kukansa ba saboda yunwa ko rashin barci ba ne, illa wata rashin lafiya ce.
Idan yana kuka lokacin yin fitsari ko bayan gida
Likitar ta ce ya kamata iyaye su lura da lokacin da jariri ke kuka.
"Idan kukansa na faruwa ne musamman lokacin da yake yin fitsari ko ba haya, hakan na iya zama alamar wata matsalar lafiya da ke buƙatar kulawar likita.
A duba kunnen jariri
Dr Fatima ta ce ciwon kunne na ɗaya daga cikin abubuwan da kan sa jarirai su riƙa farkawa ko kuka da daddare.
Ta shawarci iyaye su riƙa lura da kunnen jariri, musamman bayan wanka.











