Yadda mutumin da ya mutu ya sake bayyana kwana ɗaya bayan binne shi

Lokacin karatu: Minti 2

Al'ummar garin Masindi da ke ƙasar Uganda sun wayi gari cikin ɗimuwa bayan da wani mutum da aka ce ya mutu ya koma garin ƴan awanni bayan binne gawarsa.

Rahotannin da mujallar Daily Monitor ta intanet ta wallafa ya nuna cewa mutumin mai suna Godwin Baguma da ke Kijana wa a yankin tsakiyar Kijura na ƙasar Uganda aka rawaito ya yi ɓatan dabo na makonni, abin da ya jefa iyalansa da maƙwabtan cikin yanayin damuwa.

Bayanai daga da iyalan Baguma wanda aka ce yana da ɗan taɓin hankali ya shiga duniya ba tare da sanar da kowa ba abin da ya janyo aka tashi neman sa ruwa a jallo.

Al'amarin ya ya sauya a ƙarshen mako lokacin da iyalansa suka sami bayanai daga ƴan sanda cewa sun samo wata gawa da ta ruɓe daga gonar rake a Kisanja ranar Juma'a.

An kai gawar zuwa mutuware a asibitin Masindi inda aka bayar da sanarwar samun gawar ga duk iyalan da ke neman wani nasu da su je su duba.

Mahaifin Baguma, Yakobo kamuturaki ya ce bayan samun sanarwar ne ranar Lahadi, sai ya aiki ƴayansa zuwa mutuwaren domin tabbar da ko gawar ta ɗansa ne da ya ɓace. Kuma bayan yin duban tsanaki kan gawar sai suka koma gida suka tabbatar wa mahaifinsa cewa gawar ta ɗansa ce Baguma.

Jana'izar Baguma

"An fada cewar gawar ta ɓaci. Ƴaƴana sun je kuma sun gano ɗan uwansu. Mun yarda da abin da suka faɗa sannan mun amince da cewa ya mutu," in ji Kamuturaki.

Bayan samun wannan bayanin ne sai iyalansa dandanan suka gaggauta yi masa jana'iza saboda yadda ta zagwanye. Labarin rasuwar Baguma ya yaɗu kamar wutar daji a garin Kijura da kewaye al'amarin da ya sa jama'a suka yi ta tururuwa domin taya iyalansa alhini.

An gudanar da jana'izarsa ranar Lahadi inda iyalan suka shirya yin jana'izar bankwana da mamaci washegari wato ranar Litinin.

To sai dai kuma abin da aka fara a cikin alhini ya sauya zuwa ruɗani da mamaki bayan fitowar rahotanni da ke cewa Baguma yana raye a Kihanguzi da ke garin Labongo a lardin Masindi.

"Da farko mun yi biris da labarin. Tuni mun binne shi. Amma kuma sai muka yanke cewa mu je mu binciki gawar," in ji ƴar'uwar Baguma, Jane Birundi.

Jane ta ce iyalan Baguma sun garzaya zuwa wurin kuma suka samu Baguma a raye. Rahotanni sun ce Baguma yana kwana a gidan abokinsa.

"Lokacin da muka gan shi, mun kaɗu. Ba mu yarda shi ne a raye ba," in ji Birungi.

Ba tare da ɓata lokaci ba sai aka mayar da Baguma gida.

An tono gawa

Abin da ya faru ya sanya iyalan Baguma dandanan suka tono gawar mutumin da suka binne sannan aka mayar da gawar zuwa mutuwaren asibitin Masindi.