Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, An tashi wasa, Chelsea 1-3 Nottingham Forest

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Za mu kawo mukun wasan Everton da Man City

  2. An tashi wasa, Chelsea 1-3 Nottingham Forest

  3. , Chelsea 1-3 Nottingham Forest

    Cole Palmer ya bugo ƙwallo, amma Levi Colwill ya kasa samu .

    Ƙwallon ya yi waje.

  4. GOAL Chelsea 1-3 Nottingham Forest, Joao Pedro

    Ƙwallo ce mai ɗan karen ƙyau da aka zura a raga.

    Chelsea ta ci kwallon farko a Premier League cikin wata biyu, kuma cikin salo mai ban mamaki.

    Marc Cucurella ya dawo da ƙwallon da kai daga dogon cross sai ta yi yankin raga.

    João Pedro ya sarrafa ta da kirji, ya ɗaga ta sama, sannan ya juya jikinsa ya buga ta kai tsaye da ta nufi cikin saman raga — ƙwallo mai kyau sosai!

  5. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Saura minti biyu lokaci ya cika, filin wasa na Stamford Bridge ya yoye, ƴan kallo da yawa sun fice daga filin, wannan wane irin abin kunya ne haka a Chelsea.

  6. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Liam Delap ya samu dama mai kyau a tsakiyar fili, amma bugunsa daga kusa ya samu sauyin hanya da ta kai ƙwallon ya tashi sama ya fita.

    Chelsea ta ɗauki bugun kusurwa cikin sauri, sannan Cole Palmer ya buga ƙwallo mai ƙarfi ƙasa daga nesa, amma Matz Sels ya tare ta da hannu cikin ruwan sanyi.

  7. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Shin duk wanda ke da alaƙa da wasanni sun ziyarci Stamford Bridge.

    Mai horar da ƙasar Portugal, Roberto Martínez, da kuma tsohon ɗan Chelsea kuma mai horar da Ingila, Thomas Tuchel, suma suna nan a wurin kallon wasan.

  8. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Matz Sels ya tashi tsaye ya murmure daga faɗuwar da ya yi, don haka ba shi ne za a cire ba.

    A maimakonsa, Dilane Bakwa ya bar filin wasan, inda aka maye gurbinsa da Omari Hutchinson.

  9. Video Assistant Referee, Chelsea 1-3 Nottingham Forest

    An je duba VAR kan cewar da da akwai satar gida.

    An tabbatar dacewar da akwai satar gida daga Joao Pedro lokacin da Marc Cucurella ya bugo ƙwallon.

  10. GOAL Chelsea 1-3 Forest, Joao Pedro

    Marc Cucurella ya bugo ƙwallo zuwa wajen João Pedro, wanda ya fara buga ƙwallo mai kyau. Sai dai Pedro ya tari ƙallon ya sa kai ta faɗa raga.

  11. Chelsea za ta kara da Forest, Chelsea 0-3 Forest

    Chelsea na neman doke Nottingham Forest gida da waje a gasar Premier League karo na biyu kacal, bayan 1998-99.

    Nottingham Forest ta sha kashi sau biyu cikin wasa takwas da ta je gidan Chelsea a Premier League (Ta yi nasara biyu da canjaras huɗu), kuma ba ta taɓa shan kashi ba a wasa uku da ta ziyarci Stamford Bridge tun dawowarta gasar a 2022 (Ta yi nasara ɗaya da canjaras biyu).

    Chelsea ta ci 1-0 da 3-0 a wasanninta biyu na ƙarshe da Nottingham Forest – karo na ƙarshe da ta yi nasara sau uku a jere a kan Forest shi ne tsakanin Afrilu da Agusta 1966.

    Chelsea ta sha kashi kuma ba ta ci ƙwallo ba a wasa biyar a bayan nan a Premier League da kasa zura ƙwallo a raga.

  12. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Abu ne da ba kasafai ake gani ba—ba a yawan samun wasanni da kowanne bangare ke canji fiye da sau ɗaya, saboda raunin kai. Ni ma ban taba ganin haka ba sai a wanna karawar.

    A kowane lokaci muna fatan samun sauki ga Jesse Derry, Zach Abbott, Robert Sánchez da Morgan Gibbs-White.

  13. An yi Canji, Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Morgan Gibbs-White da Robert Sanchez an canja su, inda Chris Wood da Filip Jorgensen suk ashiga fili.

  14. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Morgan Gibbs-White yana da bandeji a kansa, amma yana iya tafiya da kansa zai fita daga filin wasan.

  15. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Idanun kowa na kan wasan Brighton & Hove Albion da Wolverhampton Wanderers a ranar Asabar mai zuwa kenan.

    Chelsea ta kai kai hari — Cole Palmer ya yi ƙwallo mai kyau amma ta bi bayan raga, amma Neco Williams ya yi jarumtar tare ƙwallon da kai a daidai lokacin da Marc Cucurella ke shirin buga ta da volley.

  16. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Marc Cucurella ya buga ƙwallo da ƙarfi, amma ta yi waje, ta fita daga fili zuwa ga gefen filin don a jiya ta ɗaya ɓangaren..

    Magoya bayan Chelsea kuma sun fara yiwa ƴan wasa ihu..

  17. , Chelsea 0-3 Nottingham Forest

    Tun daga Igor Jesus, Chris Wood da Taiwo Awoniyi, Nottingham Forest na da manyan ƴan gaba uku masu sa matsi a Premier League.

    Kenan za su ci gaba da taka rawar gani da ga duk abokiyar hamayya da suka fuskanta.

  18. GOAL Chelsea 0-3 Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi

    Ɗan wasan gaba na Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi, ya zura Ƙwallo ta biyu kuma na uku, inda ya tura ta cikin raga daga bugun da ya samu daga wajen Morgan Gibbs-White a gaban raga, bayan Elliot Anderson—wanda shi ma ya fito fili daga benci—ya yi ƙallo mai kyau ya bashi damar kai wa.

  19. , Chelsea 0-2 Nottingham Forest

    Ƙwallon da Malo Gusto ya bugo ta wuce Liam Delap kadan daga baya, sai ƙwallon ya ratsa ta cikin yanki na shida a wajen raga.

  20. , Chelsea 0-2 Nottingham Forest

    Forest kuma ta yi canje-canje uku a lokacin hutun rabin lokaci.

    Elliot Anderson, Morgan Gibbs-White da Nikola Milenkovic sun maye gurbin Igor Jesus, Nicolas Dominguez da Jair Cunha.