Video Assistant Referee, Chelsea 1-3 Nottingham Forest
An je duba VAR kan cewar da da akwai satar gida.
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga 4 zuwa 8 ga watan Mayun 2026.
Mohammed Abdu
An je duba VAR kan cewar da da akwai satar gida.
Chelsea na neman doke Nottingham Forest gida da waje a gasar Premier League karo na biyu kacal, bayan 1998-99.
Nottingham Forest ta sha kashi sau biyu cikin wasa takwas da ta je gidan Chelsea a Premier League (Ta yi nasara biyu da canjaras huɗu), kuma ba ta taɓa shan kashi ba a wasa uku da ta ziyarci Stamford Bridge tun dawowarta gasar a 2022 (Ta yi nasara ɗaya da canjaras biyu).
Chelsea ta ci 1-0 da 3-0 a wasanninta biyu na ƙarshe da Nottingham Forest – karo na ƙarshe da ta yi nasara sau uku a jere a kan Forest shi ne tsakanin Afrilu da Agusta 1966.
Chelsea ta sha kashi kuma ba ta ci ƙwallo ba a wasa biyar a bayan nan a Premier League da kasa zura ƙwallo a raga.
Abu ne da ba kasafai ake gani ba—ba a yawan samun wasanni da kowanne bangare ke canji fiye da sau ɗaya, saboda raunin kai. Ni ma ban taba ganin haka ba sai a wanna karawar.
A kowane lokaci muna fatan samun sauki ga Jesse Derry, Zach Abbott, Robert Sánchez da Morgan Gibbs-White.
Morgan Gibbs-White da Robert Sanchez an canja su, inda Chris Wood da Filip Jorgensen suk ashiga fili.
Morgan Gibbs-White yana da bandeji a kansa, amma yana iya tafiya da kansa zai fita daga filin wasan.
Idanun kowa na kan wasan Brighton & Hove Albion da Wolverhampton Wanderers a ranar Asabar mai zuwa kenan.
Chelsea ta kai kai hari — Cole Palmer ya yi ƙwallo mai kyau amma ta bi bayan raga, amma Neco Williams ya yi jarumtar tare ƙwallon da kai a daidai lokacin da Marc Cucurella ke shirin buga ta da volley.
Marc Cucurella ya buga ƙwallo da ƙarfi, amma ta yi waje, ta fita daga fili zuwa ga gefen filin don a jiya ta ɗaya ɓangaren..
Magoya bayan Chelsea kuma sun fara yiwa ƴan wasa ihu..
Tun daga Igor Jesus, Chris Wood da Taiwo Awoniyi, Nottingham Forest na da manyan ƴan gaba uku masu sa matsi a Premier League.
Kenan za su ci gaba da taka rawar gani da ga duk abokiyar hamayya da suka fuskanta.
Ɗan wasan gaba na Nottingham Forest, Taiwo Awoniyi, ya zura Ƙwallo ta biyu kuma na uku, inda ya tura ta cikin raga daga bugun da ya samu daga wajen Morgan Gibbs-White a gaban raga, bayan Elliot Anderson—wanda shi ma ya fito fili daga benci—ya yi ƙallo mai kyau ya bashi damar kai wa.

Asalin hoton, Getty Images
Ƙwallon da Malo Gusto ya bugo ta wuce Liam Delap kadan daga baya, sai ƙwallon ya ratsa ta cikin yanki na shida a wajen raga.
Forest kuma ta yi canje-canje uku a lokacin hutun rabin lokaci.
Elliot Anderson, Morgan Gibbs-White da Nikola Milenkovic sun maye gurbin Igor Jesus, Nicolas Dominguez da Jair Cunha.
Wani ƙwararren buge ƙwallo! Chelsea har yanzu ba ta samu cin ƙwallo ba a gasar Premier League ba, domin Matz Sels ya yi tsalle zuwa damarsa ya tare bugun fenariti da yatsun hannu da Cole Palmer ya buga.
Sels ya tashi da sauri bayan haka ya kuma rje yana ta yi wa Palmer ihu, wanda ya kasa sarrafa ƙwallon da ya kara bugawa.

Asalin hoton, Getty Images
Derry, wanda ke buga wasansa na farko a Premier League, an maye gurbinsa da Liam Delap.
Zach Abbott ba zai iya ci gaba da fafatawar ba, an kuma canja shi da eco Williams.
Magoya bayan Chelsea sun korafin sun samu fenariti. Wannan karon lallai kamar sun samu bugun daga kai sai mai tsaron raga. Ɗan wasan Nottingham Forest, Dilane Bakwa ne ya yi sakaci inda ya yiwa Malo Gusto keta, har ya jawo faɗuwar ɗan wasan Chelsea.
Amma Anthony Taylor tare da VAR sun yanke shawarar cewa kawai haɗuwa ce ta wasa, ba fenariti ba.
Joao Pedro yana da karancin taɓa ƙwallo a karawar, shi ne mai mafi karaci a fafatawar tsakanin ƴan wasa mai bakwai kacal.
Hakan na nuna maka yadda Chelsea ke cin karo da koma baya na rashin kwazo daga wasu ƴan wasan da ake sa ran za su fitar da ita kunya.
Nottingham Forest tana taka rawa sosai. Tsarinsu yadda suke taka leda a filin wasan yana da kyau, ba ta yawan kuskure tana buga karawar da kwarin gwiwa, kuma tan yin abin da ake bukata, kamar ta shiryawa wasan nan da kyau.
Chelsea kuwa ba ta yin abin da zai kai ta farke ƙwallayen da aka zura mata. Duk lokacin da take kokrin kai kora, sai kaga Forest na cikin shiri sosai. Har yanzu ba abin da za ka ce ya firgita Forest daga Chelsea.

Asalin hoton, Getty Images