Yadda Birtaniya ke tura masu laifin fyaɗe zuwa wasu ƙasashen Afrika

Eswatini
    • Marubuci, Jean Mackenzie
    • Aiko rahoto daga, Nairobi
    • Marubuci, Dominic Casciani
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Gwamnatin Birtaniya ta tilasta wa wani ɗan gudun hijira da aka samu da laifin yin lalata da yara komawa ƙasar Eswatini da ke Afirka, duk da cewa ba shi da wata alaƙa da ƙasar.

An komar da mutumin ne ba tare da sanar da majalisar dokokin Birtaniya ko al'ummar ƙasar Eswatini ba.

Mutumin, mai suna Kishanth Peramalya, ɗan asalin Sri Lanka ne, kuma yana da tarihin fama da matsananciyar matsalar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma yunƙurin kashe kansa.

Sai dai ya kashe kansa watanni kaɗan bayan isa ƙasar Eswatini.

BBC ta samu kwafin yarjejeniyar da gwamnatocin ƙasashen biyu suka tsara, wadda ta nuna cewa Birtaniya ta amince za ta ɗauki nauyin kuɗin sake tsugunar da shi a ƙasar har na tsawon shekaru uku.

A lokacin rasuwarsa, gwamnatin Birtaniya na kammala shirye-shiryen da za su ba Peramalya, mai shekaru 35, damar ci gaba da zama a Eswatini har abada.

Masana harkokin ƙaura sun shaida wa BBC cewa wannan ne karon farko da aka samu sanannen misali na gwamnatin Birtaniya ta tilasta wa wani ɗan gudun hijira sake tsugunar da shi na dindindin a wata ƙasa ta ƙetare ta wannan hanya.

A shekarar 2024, gwamnatin jam'iyyar Labour ta soke wani shiri mai cike da ce-ce-ku-ce na tura masu neman mafaka zuwa Rwanda, waɗanda har yanzu ba a kammala nazarin buƙatunsu na neman mafaka ba.

Tsallake Whatsapp
BBC News Hausa WhatsApp latsa nan domin shiga tasharmu
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Yanzu haka gwamnatin na son tura mutanen da aka ƙi amincewa da buƙatunsu na neman mafaka zuwa wasu ƙasashe na uku, idan ba zai yiwu a mayar da su ƙasashensu na asali ba. Sai dai har yanzu ba ta sanar da wata yarjejeniya da kowace ƙasa kan hakan ba.

A makon da ya gabata, wasu ƙasashen Tarayyar Turai guda biyar sun cimma yarjejeniyar tura mutanen da aka ƙi amincewa da buƙatunsu na neman mafaka zuwa Rwanda.

Yarjejeniyar da Birtaniya ta kulla da Eswatini ta haifar da tambayoyi kan irin bayanan da ya kamata gwamnatin Birtaniya ta bayyana game da irin waɗannan yarjejeniyoyi, da kuma yadda take kare mutanen da take turawa ƙasashen waje da kuma al'ummomin da za su karɓe su.

Gwamnatin Birtaniya ta shaida wa BBC cewa kare al'ummar ƙasar shi ne babban abin da ta sa a gaba, kuma tana ci gaba da aiki tare da hukumomin Eswatini dangane da wannan batu.

Iyalan Peramalya na neman ƙarin bayani kan yadda aka kula da shi, yayin da masu sukar matakin a Eswatini suka zargi Birtaniya da amfani da ƙasarsu a matsayin wurin zubar da mutanen da ba ta buƙata.

Rundunar sojojin Birtaniya ta ceto wasu

A shekarar 2021, rundunar sojojin ruwan Birtaniya ta ceto Peramalya tare da wasu 'yan Sri Lanka da dama da ke neman mafaka, a tekun Indiya, yayin da suke ƙoƙarin tafiya daga Indiya zuwa Kanada ta ruwa.

Daga nan aka tsare su a wani sansani da ke tsibirin Diego Garcia, wanda wani ɓangare ne na yankin Birtaniya da ke Tekun Indiya, kuma ake amfani da shi a matsayin sansanin sojojin Birtaniya da Amurka kaɗai.

Hukumomin tsibirin, waɗanda ke ƙarƙashin ikon gwamnatin Birtaniya da ke Landan, sun amince cewa ba zai yiwu Peramalya da sauran mutanen su koma Sri Lanka cikin aminci ba. Saboda haka, suka ba su kariyar da ake bai wa 'yan gudun hijira.

Sai dai ƙungiyar ta ci gaba da zama a sansanin na tsawon shekaru uku, yayin da jami'an Birtaniya ke tattaunawa kan makomarsu. Daga baya, wata kotu ta yanke hukuncin cewa tsare su da aka yi ya saɓa wa doka.

Photo shows three round beige tents on green grass. In the background there is a hut

Tun yana matashi, Peramalya ya sha azaba da cin zarafin lalata daga jami'an sojin Sri Lanka. Daga baya kuma an gano yana fama da matsalar tabin hankali sakamakon raɗaɗin abubuwan da suka faru da shi.

Takardun kotu sun nuna cewa yanayin lafiyar kwakwalwarsa ya ƙara tabarbarewa a lokacin da yake tsare a tsibirin Diego Garcia. Ya riƙa fama da baƙin ciki da fargaba, sannan ya yi ƙoƙarin kashe kansa sau da dama. Haka kuma, masu sa ido na Majalisar Ɗinkin Duniya da suka kai ziyara tsibirin sun nuna damuwa kan yanayin da ake tsare da shi.

A lokacin da yake tsibirin, ya aikata laifuka daban-daban, ciki har da kai hari da kuma ƙona kadarori, a yayin ƙoƙarin kashe kansa guda biyu. Saboda haka, ya shafe makonni 24 a gidan yari. An kuma same shi da laifin cin zarafin mutane ta fuskar lalata a tuhume-tuhume guda huɗu, inda aka yanke masa hukuncin ɗaurin kurkuku da aka dakatar da aiwatarwa.

A watan Disamban 2024, an ba yawancin masu neman mafaka daga Sri Lanka izinin shiga Birtaniya, amma ministocin ƙasar sun ƙi barin Peramalya ya bi sahunsu saboda laifukan da ya aikata. Hakan ya sa ya ci gaba da zama a tsibirin Diego Garcia.

Babbar Kotun Birtaniya ta tabbatar da matakin da ƙasar ta ɗauka na ƙin shigar da shi, a wani ɓangare saboda barazanar da ake ganin zai iya haifarwa, da kuma ƙoƙarin gaske da ministocin ke yi na nemo masa wata ƙasa mai aminci da zai zauna.

Takardun kotu da BBC ta gani sun nuna cewa Birtaniya ta tuntuɓi ƙasashe fiye da 20, amma ta kasa cimma yarjejeniya da ko ɗaya daga cikinsu.

A watan Fabrairun 2026, Amurka ta fara amfani da sansaninta na soji da ke tsibirin Diego Garcia a yakin da take yi da Iran. Hakan ya sa hukumomin tsibirin suka fara kwashe ma'aikatan da ba su da muhimmanci ga gudanar da ayyukan yau da kullum.

A ƙarshen watan Maris, kasar Maldives ta miƙa tayin karɓar Peramalya na tsawon kwanaki 30. Daga nan aka kai shi ƙasar kafin daga bisani a tura shi Eswatini, wadda a da aka fi sani da Swaziland.

A lokacin da ya rasu, gwamnatocin Birtaniya da Eswatini na kammala yarjejeniyar da za ta ba Peramalya damar zama a ƙasar har abada. A ƙarƙashin yarjejeniyar, Birtaniya za ta biya kuɗaɗen da suka dace na masaukinsa, kula da lafiyarsa da sauran tallafin da yake buƙata na tsawon shekaru uku.

Takardar ba ta fayyace adadin kuɗin da za a kashe ba, ko kuma yadda gwamnatocin biyu za su shawo kan haɗarin da Peramalya zai iya fuskanta ko kuma ya iya haifarwa ga wasu. Sai dai ta amince ƙarara cewa yana buƙatar tallafin da zai biya masa buƙatunsa na yau da kullum, tare da kare lafiyarsa ta jiki da ta kwakwalwa da kuma jin daɗinsa.

Iyalin Peramalya sun shaida wa BBC cewa da farko an sauke shi ne a wani gidan baƙi da ke keɓe, inda yake zaune shi kaɗai.

Da take magana daga Indiya, 'yar'uwar Peramalya ta ce iyalinsu ba su da masaniyar shirin mayar da zamansa a ƙasar ta Eswatini na dindindin. Ta kuma ce yanayin lafiyar kwakwalwarsa ya ƙara tabarbarewa a lokacin da yake ƙasar.

Ta ce ɗan'uwanta kan kira ta har sau huɗu a rana.

"Ɗan'uwana sam bai son zuwa can. Ya kasa jure zama shi kaɗai a wurin, domin yana cikin kaɗaici sosai," in ji ta.

Iyalin sun kuma ce ba su da masaniyar laifukan cin zarafin lalata da ya aikata.

Ta ce da farko yana ganin likitan masu fama da matsalar tabin hankali sau ɗaya a mako. Sai dai daga baya, bayan yanayinsa ya ƙara tsananta, aka riƙa shirya masa ganawa da likitan a kullum, sannan aka ɗauko wani mai kula da shi domin dafa masa abinci.

A ranar 13 ga watan Satumba, ya kashe kansa.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya, wadda a baya ta nuna damuwa kan halin da Peramalya yake ciki a tsibirin Diego Garcia, ta ce ta yi matuƙar alhini kan rasuwarsa. Ta kuma jaddada muhimmancin kare haƙƙin 'yan gudun hijira da masu neman mafaka da ake ƙaura da su zuwa wasu ƙasashe.

Abin da ba a saba gani ba

Peter Walsh, na Cibiyar Binciken Hijira ta Jami'ar Oxford, ya bayyana lamarin a matsayin wanda ba kasafai ake ganin irinsa ba.

"A mafi yawan lokuta, mutanen da aka samu da laifuka amma ba za a iya mayar da su ƙasashensu na asali ba, sukan ci gaba da zama ne a Birtaniya. Ƙasashe na uku kuwa ba kasafai suke amincewa da karɓar waɗanda aka samu da laifuka daga wasu ƙasashe ba," in ji shi.

Ba a bayyana yadda Birtaniya ta zaɓi Eswatini ba, sai dai tuni ƙasar ta amince da karɓar mutanen da Amurka ke korarwa daga ƙasarta, a ƙarƙashin babban shirin Shugaba Donald Trump na tura 'yan ci-rani zuwa ƙasashe daban-daban na Afirka da Latin Amurka.

A shekarar 2025, gwamnatin Trump ta biya Eswatini dala miliyan 5.1 kwatankwacin fam miliyan 3.9, domin karɓar mutane har 160.

Melusi Simelane, na Cibiyar Kare Haƙƙin Bil Adama ta Kudancin Afirka, wanda ke ƙalubalantar yarjejeniyar Amurka da Eswatini a kotu, ya ce tura 'yan ci-rani zuwa ƙasarsu na ƙara wa ƙasarsu nauyi, duba da ƙarancin albarkatun da take da su.

"Tsarin kula da lafiyarmu na dab da durƙushewa, balle ma bangaren kula da lafiyar kwakwalwa. Don haka, babban nauyi ne karɓar mutanen da ke buƙatar kulawa da tallafi sosai zuwa cikin al'ummarmu," in ji shi.

"Afrika na zama wurin da duniya ke zubar da matsalolin da ta kasa magancewa."

Gwamnatocin Birtaniya da Eswatini ba su amsa tambayoyin BBC kan yadda aka gudanar da aikin mayar da Peramalya zama a Eswatini ba. Sai dai wani mai magana da yawun gwamnatin Birtaniya ya ce:

"Kare lafiyar al'ummar Birtaniya zai kasance babban abin da muka fi ba wa muhimmanci a kowane lokaci, kuma za mu ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kare al'ummar ƙasar. Hakan ya haɗa da ɗaukar matakai don tabbatar da cewa manyan masu aikata laifuka daga ƙasashen waje ba su samu damar shiga Birtaniya ba."

Ƙarin rahoto daga Alice Cuddy da Swaminathan Natarajan.