Waɗanne sansanonin sojin Amurka ne Iran ta kai wa hari?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta bayyana cewa ta kai hare-hare kan wasu sansanonin sojin Amurka da ke Jordan, Bahrain da Kuwait, a wani mataki na martani yayin da rikici tsakanin Iran da Amurka ke ci gaba da tsananta.

A cewar sanarwar da jami'an hulda da jama'a na IRGC suka fitar, sun ce sun kai hari kan sansanin sojin saman Yarima Hassan a Jordan, da sansanin sojin saman Sheikh Isa a Bahrain, tare da sansanin sojin saman Ali Al Salem da Ahmed Al Jaber a Kuwait.

Iran ta ce ta lalata cibiyoyin sarrafa jiragen yaƙi marasa matuka na Amurka a Bahrain, sannan ta ƙona wasu manyan rumbunan adana makamai masu linzami da tankokin mai a wani sansanin soji da ke Jordan ta amfani da makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa.

Haka kuma, rundunar IRGC ta yi iƙirarin cewa ta lalata tankokin ajiye mai da kuma tsarin kariyar sararin samaniyar Patriot a sansanin Ali Al Salem, tare da lalata tsarin kare gobara a sansanin Ahmed Al Jaber da ke Kuwait.

A lokaci guda, rundunar sojin Amurka ta CENTCOM ta sanar da ƙaddamar da sabon jerin hare-hare kan Iran, inda ta ce ta kai farmaki kan wurare da dama da ake ajiye makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa da kuma tsarin kariyar sararin samaniya da sauran cibiyoyin soja.

CENTCOM ta ce an gudanar da hare-haren ne da jiragen yaƙi da jiragen ruwa da kuma jirage marasa matuƙa bisa umarnin shugaban Amurka Donald Trump, domin rage ƙarfin Iran na kai hare-hare kan zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz.

A wani ɓangare kuma, kafafen yaɗa labaran Iran sun ce rundunar ruwan IRGC ta dakatar da wasu jiragen ruwa biyu da ta zarga da yin barazana ga zirga-zirgar ruwa kafin hare-haren Amurka.

Rahotanni daga kamfanin dillancin labaran Iran na IRNA sun ce mutum daya ya mutu, yayin da wasu hudu suka jikkata bayan wani hari da Amurka ta kai kan cibiyar tace ruwa a birnin Mahshahr.

Haka kuma, gidajen talabijin Iran sun ba da rahoton jin karar fashe-fashe a yankunan Sirik, Qeshm, Jask da wasu sassan lardin Bushehr da ke kudancin kasar.

Muhimman sansanonin Amurka da Iran ta ce ta kai wa hari:

Sansanin sojin saman Yarima Hassan – Jordan

Sansanin sojin saman Sheikh Isa – Bahrain

Sansanin sojin saman Ali Al Salem – Kuwait

Sansanin sojin saman Ahmed Al Jabe – Kuwait

'Hare-haren sun lalata ƙoƙarin diflomasiyya'

Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce hare-haren da Amurka ta kai sun yi wa ƙoƙarin sasanta rikicin ta hanyar diflomasiyya babban cikas.

"A cikin sanarwar, ma'aikatar ta zargi sojojin Amurka da aikata abin da ta kira 'ayyukan ta'addanci', tana mai cewa sun jefa wasu ƙasashen yankin Tekun Fasha cikin abin da ta bayyana a matsayin wani haramtaccen yaƙi da kuma laifin da ake aikatawa al'ummar Iran."

Ta ƙara da cewa an yi amfani da yankuna da wuraren waɗannan ƙasashe wajen shirya hare-haren soja kan Iran.

Iran ta kuma gargadi maƙwabtanta da su guji haɗin gwiwa da waɗanda ta kira "masu tayar da tarzoma", tana mai jaddada cewa duk wata ƙasa da aka yi amfani da yankinta ko cibiyoyinta wajen kai hari kan Iran za ta iya fuskantar hare-hare mafi muni daga Iran ɗin.

Sanarwar ta kuma ce iƙirarin shugaban Amurka game da tattaunawar Muscat da aka gudanar a ranar Asabar "ba gaskiya ba ne".

A cewar Iran, tattaunawar ta fi mayar da hankali ne kan yadda za a tafiyar da mashigar Hormuz da hanyoyin sufuri na teku, tana zargin Amurka da daƙile cimma matsaya kan wannan batu tare da matsa lamba ga Oman.

Ma'aikatar ta kuma zargi Amurka da haddasa sabuwar rashin kwanciyar hankali a mashigar Hormuz, tare da kawo cikas ga harkokin kasuwanci na ƙasashen duniya, sakamakon abin da ta bayyana a matsayin tsoma bakin da Amurka ke yi a matakan da Iran ke ɗauka a yankin."

A gefe guda, rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta musanta rahotannin wasu kafafen yaɗa labaran Iran da suka ce an kashe sojojin Amurka uku a Kuwait sakamakon hare-haren Iran.

CENTCOM ta ce babu wani rahoto na mutuwa ko rauni a tsakanin sojojinta a yankin, kuma dukkan jami'anta na cikin ƙoshin lafiya.

A halin da ake ciki, farashin mai ya yi tashin gwauron zabo a kasuwannin duniya a ranar Litinin bayan sabbin tashin hankalin da suka ɓarke tsakanin Iran da Amurka a ƙarshen mako, da kuma sanarwar Tehran cewa za ta rufe mashigar Hormuz.

Farashin ɗanyen man Brent na watan Satumba ya ƙaru da kashi 3.75 cikin ɗari zuwa dala 78.86 kan kowace ganga, yayin da ɗanyen man West Texas Intermediate (WTI) na watan Agusta ya tashi da kashi 3.65 cikin ɗari zuwa dala 74.02 kan kowace ganga.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira a dakatar da hare-hare

Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) ta nuna damuwa kan yadda rikici ke ƙaruwa a yankin Tekun Fasha, inda ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da su dakatar da hare-hare tare da guje wa ƙara ruruta rikicin.

Kakakin Sakatare Janar na MƊD ya ce sabon faɗan da ya haɗa da hare-haren Iran a mashigar Hormuz da kuma hare-haren Amurka kan Iran na barazana ga zaman lafiya da tattalin arziƙin duniya.

Ya kuma jaddada muhimmancin tabbatar da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin 'yanci a mashigar.

Sai dai kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Iran, Ismail Baghaei, ya mayar da martani yana cewa abin da ke faruwa ba faɗa ba ne, illa ci gaba da abin da ya kira hari marar hujja daga Amurka da Isra'ila.

Ya ce hare-haren da Iran ta kai kan sansanonin sojin Amurka kariya ce ta kai da dokokin ƙasashen duniya suka amince da ita, yana mai kira ga MƊD ta matsa lamba kan ƙasashen da ke ba Amurka damar amfani da ƙasarsu wajen kai hare-hare kan Iran.

Ana ci gaba da musayar wuta tsakanin Amurka da Iran, yayin da har yanzu ake taƙaddama kan matsayin mashigar Hormuz ko a buɗe take ko a'a.