Manchester United na son Hall, Zubimendi zai iya barin Arsenal

Asalin hoton, Getty Image
Newcastle ba za ta saurari tayin sayen Lewis Hall mai shekara 22 a watan Janairu ba, yayin da Manchester United ka iya sake kokarin sayen dan wasan mai tsaron baya na Ingila.(Telegraph - subscription required)
Dan wasan Arsenal, Martin Zubimendi, a shirye yake ya bar Gunners saboda ƙarancin damar buga wasanni a Gunners, inda Atletico Madrid da Chelsea ke sha'awar daukar ɗan ƙasar Spain mai shekara 27.(AS - in Spanish)
Chelsea ta tsara yadda za ta ɗauki dan wasan Spain mai taka leda a Barcelona, Fermin Lopez, mai shekara 23 da kuma ɗan Faransa, Jules Kounde, mai shekara 28, a watan Janairu, inda ta shirya tayin fam miliyan 150 domin jan hankalin kungiyar ta Catalonia ta sallamar ba tare da jan kafa ba.(El Nacional - in Catalan)
Dan wasan Senegal mai taka leda a Crystal Palace, Ismaila Sarr, mai shekara 28, ya bude dama ga dukkan kungiyar da ke son daukarsa a kasuwar cinikayyar 'yan wasa ta watan Janairu, bayan rashin wani ci gaba a tattaunawar sabunta kwantiraginsa a Selhurst Park.(Football Insider)
Real Madrid na bibiyar yadda wasu yan wasan Brighton ke taka leda a wannan kakar, inda ɗan Croatia mai shekara 19, Luka Vuskovic, da ɗan wasan Spain mai shekaru 21, Chema Andres, suke cikin waɗanda suka ja hankalinta.(Teamtalk)
Matashin mai tsaron raga na Bayern Munich, Leonard Prescott, mai shekara 17, na ƙara kusantar barin kungiyar ta Bundesliga bayan tattaunawar kwantiragi ta tsaya cik. Chelsea,Arsenal, Brighton da Aston Villa na cikin masu sha'awar daukar ɗan wasan matasan Jamus da aka haifa a New York. (Sky Sports Germany - in German)
Leeds United ta tuntubi Stuttgart kan yiwuwar kulla yarjejeniya a watan Janairu domin sayen ɗan wasan Morocco mai shekara 22, Bilal El Khannouss. (Teamtalk)
Barcelona har yanzu tana sha'awar daukar ɗan bayan Croatia mai wasa a Manchester City, Josko Gvardiol, mai shekara 24, amma ba ta ganin yarjejeniya za ta yiwu. (AS - in Spanish)
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Newcastle na shirye-shiryen fafatawa da Liverpool da wasu ƙungiyoyin Premier League domin ɗaukar mai tsaron bayan Faransa mai shekara 21 na Lens, Ismaelo Ganiou. (Football Insider)
Mauricio Pochettino ba shi kaɗai ne mutum da Manchester United ta tuntuba domin maye gurbin Michael Carrick ba, inda kuma aka tattauna da tsohon kocin Faransa, Didier Deschamps. (Talksport)
Har ila yau, shugabannin Manchester United sun tattauna kan yiwuwar daukar kocin Como, Cesc Fabregas, amma batun bai kai ga yin wata magana a hukumance da tsohon ɗan wasan Arsenal ba. (The Athletic - subscription required)
Dan wasan Amurka mai taka leda a Monaco, Folarin Balogun, mai shekara 25, wanda yarjejeniyar komawarsa Everton ta rushe a ranar ƙarshe a kasuwar cinikayyar 'yan wasa, na tattaunawa da AC Milan da Juventus kan yiwuwar komawa can a watan Janairu. (Calciomercato - in Italian)
Tottenham a shirye take ta bar Richarlison ya tafi kan farashin tsakanin fam miliyan 10 zuwa 15 a watan Janairu, yayin da Trabzonspor ke sha'awar ɗaukar ɗan wasan tawagar Brazil mai shekara 29. (Teamtalk)



























