Manyan Musulman da suka fi tasiri a duniya

Asalin hoton, Getty Images
Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif, da babban hafsan sojojin ƙasar, Field Marshal Aasim Munir sun kasance a matsayi na farko tare a sabon jerin Musulmi 500 da suka fi tasiri a duniya.
Jerin ya kuma ƙunshi sunayen Sarkin Saudiyya, Salman bin Abdulaziz, da Yarima mai jiran gado, Mohammed bin Salman, da kuma Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan.
Tsohon Firaministan Pakistan, Imran Khan, shi ma yana cikin jerin.
Rahoton ya yi tsokaci kan rawar da Aasim Munir ke takawa a harkokin cikin gida na Pakistan, tare da ambaton tsare Imran Khan da kuma tsauraran matakan da ake amfani da su wajen murƙushe masu adawa da gwamnati.
Cibiyar Royal Islamic Strategic Studies Centre (RISSC), da ke birnin Amman na ƙasar Jordan, ce ke fitar da wannan jerin a duk shekara, wanda aka fi sani da The Muslim 500.
Jerin ya ƙunshi fitattun Musulmai da ake ganin suna da tasiri sosai a duniyar Musulunci.
A cewar cibiyar, jerin na shekarar 2027 shi ne karo na farko da mutane biyar suka kasance a sahun gaba tare.
RISSC ta ce babban dalilin wannan matsayi shi ne yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa ta Makkah (Makkah Mutual Defense Treaty), wadda aka rattaba hannu a kanta a ranar 7 ga Agusta, 2026.
A cewar rahoton cibiyar, yarjejeniyar ta haɗa ƙarfin tattalin arzikin Saudiyya, da ƙarfin fasaha da masana'antu na Turkiyya, da kuma ƙarfin sojin Pakistan, domin samar da ƙawancen tsaro guda ɗaya.
Rahoton ya bayyana cewa wannan haɗin gwiwar tsaro, ta sauya alkiblar siyasar yankin matuƙa.
Rawar da Aasim Munir ke takawa a bayan fage da kuma shaharar Imran Khan

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Rahoton da aka fitar tare da jerin Musulmi 500 mafi tasiri a duniya ya ƙunshi bayanai na musamman kan Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif, da babban hafsan sojojin ƙasar, Aasim Munir.
A cewar rahoton, Shahbaz Sharif shi ne Firaminista na 24 a tarihin Pakistan, wanda ya sake komawa kan kujerar mulkin ƙasar a karo na biyu a watan Maris na 2024.
An bayyana shi a matsayin shugaba mai ƙwazo da jajircewa, inda rahoton ya ce a lokacin mulkinsa Pakistan ta samu damar fita daga mummunan yanayin matsin tattalin arziki da barazanar durƙushewar tattalin arziƙi, tare da samun ci gaba zuwa ga daidaituwar tattalin arziki.
A cewar rahoton, wasu alamomin tattalin arzikin ƙasar sun inganta, hauhawar farashi ta ragu, yayin da ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙaru.
Rahoton ya kuma yi tsokaci kan yadda Shahbaz Sharif ya rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro ta haɗin gwiwa ta Makkah tare da shugabannin Saudiyya da Turkiyya, wadda aka bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro a duniyar Musulunci.
Bugu da ƙari, rahoton ya jaddada rawar da ya taka a ƙoƙarin sasanta rikice-rikice a Gabas ta Tsakiya, musamman yadda aka gabatar da Pakistan a matsayin ƙasa mai tsaka-tsaki da ke ƙoƙarin shiga tsakani kan takun-sakar da ke tsakanin Iran, Amurka da Isra'ila.
Sai dai rahoton ya kuma bayyana cewa Shahbaz Sharif na ci gaba da fuskantar ƙalubalen cikin gida, ciki har da matsalolin tattalin arziki, hauhawar farashi, yawan basussuka, rikicin siyasa da kuma ci gaba da farin jinin tsohon Firaminista Imran Khan, wanda ke tsare a gidan yari.
Dangane da Aasim Munir, rahoton ya ce shi ne shugaban rundunar tsaron Pakistan kuma kwamandan sojojin ƙasar, waɗanda ke cikin manyan rundunonin soji shida mafi girma a duniya.
A cewar rahoton, lokacin da aka ƙara masa matsayi zuwa Field Marshal a watan Mayun 2025, tasirinsa a harkokin siyasa, da soja da kundin tsarin mulkin ƙasar ya ƙaru.
Rahoton ya kuma bayyana cewa shi ne shugaban rundunar sojin Pakistan na farko da ya haddace Alƙur'ani baki ɗaya.
Rahoton ya yi tsokaci kan muhimman matakan da ya kai a aikin soja, ciki har da jagorantar hukumar leƙen asirin soji da kuma hukumar leƙen asirin ƙasar ta ISI, rawar da ya taka a rikicin India da Pakistan na shekarar 2025, da kuma shigarsa cikin yarjejeniyar tsaro ta Makkah da Saudiyya da Turkiyya.
A cewar rahoton, diflomasiyyar Aasim Munir da yake gudanarwa a bayan fage ta taimaka wajen sasanta Amurka da Iran, wanda ya kai ga cimma yarjejeniyar tsagaita wuta na wucin gadi a yankin. Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yaba da wannan rawar a bainar jama'a.
Da yake magana kan rawar Field Marshal Aasim Munir a harkokin cikin gidan Pakistan, rahoton ya ce ya ɗauki tsauraran matakai wajen tabbatar da doka da oda a ƙasar, tare da ƙoƙarin samar da kwanciyar hankali a siyasa da tattalin arziki.
Rahoton ya ce: "Wannan ya haɗa da tsare tsohon Firaminista Imran Khan da kuma murƙushe masu nuna adawa da gwamnati ta hanyar amfani da tsauraran matakai."
Imran Khan ma yana cikin jerin
Rahoton ya kuma ƙunshi wasu fitattun mutane daga Pakistan.
Tsohon Firaminista Imran Khan na cikin jerin, inda ya zo na 24 a rukunin shugabanni da 'yan siyasa.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Rahoton ya ce: "Duk da tsawon lokacin da ya shafe a gidan yari, Imran Khan na ci gaba da samun gagarumin goyon bayan jama'a. Jam'iyyarsa kuwa, duk da matsin lamba daga hukumomi da kuma matakan murƙushe ta, ta lashe mafi yawan kujeru a babban zaɓen shekarar 2024."
Jerin ya kuma ƙunshi fitaccen malamin addinin Musulunci, Taqi Usmani, wanda ya zo na bakwai, shahararren mai wa'azi, Mawlana Tariq Jamil, wanda ya zo na 32, da kuma Mawlana Nazarur Rahman na ƙungiyar Tablighi Jama'at, wanda ya zo na 41. Haka kuma, wanda ya kafa ƙungiyar Dawat-e-Islami, Muhammad Ilyas Attar Qadri, ya zo na 44.
A ɓangaren kafafen yaɗa labarai kuwa, akwai fitaccen ɗan jaridar Pakistan, Hamid Mir, da kuma mamallakin tashar talabijin ta ARY, Salman Iqbal.
Sauran waɗanda ke cikin jerin sun haɗa da shugaban jam'iyyar Jamaat-e-Islami ta Pakistan, Hafiz Naeemur Rahman; wanda ya kafa cibiyar Idara Minhaj-ul-Quran, Tahir-ul-Qadri; Malala Yousafzai, wadda ta lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya saboda fafutukar tabbatar da ilimin 'ya'ya mata Dr Umar Saif, ƙwararre kan fasaha da harkokin mulkin dijital; da Farfesa Irfan Siddiqui, masanin kimiyyar lissafi, tare da wasu fitattun 'yan Pakistan a fannoni daban-daban.
Baya ga shugabannin Saudiyya, Pakistan da Turkiyya da suka zo na farko tare, jerin ya kuma ƙunshi jagoran addini na Iran, Ayatollah Ali Khamenei, da Sarkin Qatar, Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani, da Sarkin Morocco, Mohammed VI da Sarkin Jordan, Abdullah II da kuma Sarkin Oman, Haitham bin Tariq.
Jagoran ƙungiyar Taliban ta Afghanistan, Mullah Haibatullah Akhundzada, shi ma yana cikin jerin, inda ya zo na 19.
Jerin ya kuma ƙunshi Magajin Garin Landan, Sadiq Khan, da Magajin Garin New York, Zohran Mamdani, da kuma shugaban ƙungiyar Hamas ta Falasɗinu, Khalil al-Hayya.
A kan wane ma'auni ake zaɓen waɗannan mutane?

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Cibiyar Royal Islamic Strategic Studies Centre ta bayyana a cikin rahotonta cewa jerin ya ƙunshi mutanen da suka yi gagarumin tasiri ga al'ummar Musulmi ko kuma suka bayar da muhimmiyar gudummawa ga ci gabanta. Ta kuma yi bayanin abin da take nufi da kalmar 'tasiri' wajen tsara jerin.
A cewar cibiyar, tasiri na nufin ikon da mutum yake da shi na sauya tunani ko shafar al'ummar Musulmi da duniyar Musulunci, ta fuskar al'adu, da akida, da tattalin arziki, da siyasa ko kuma wasu abubuwan da za a iya gani a aikace.
Rahoton ya ce ana iya kallon wannan tasiri ta fuskoki daban-daban, ko na alheri ne ko akasin haka. Sai dai, babban ma'aunin da ake amfani da shi wajen tsara jerin shi ne irin tasirin da mutum yake da shi.
A lokaci guda, cibiyar ta fayyace cewa sanya sunan mutum cikin jerin ba yana nufin tana goyon bayan ra'ayoyinsa ko matsayinsa ba ne.
A cewar rahoton, ba a auna tasirin mutum da yawan mabiyansa, da littattafan da ya wallafa ko shahararsa kawai ba. Ana kuma la'akari da irin tasirin da ya yi ga mutane da al'umma, da girmansa, da kuma tsawon lokacin da wannan tasiri ya ɗauka.
Saboda haka, ana ba da fifiko ga tasiri mai ɗorewa da gudummawar da mutum ya bayar a tsawon rayuwarsa, maimakon shaharar da za ta iya kasancewa ta ɗan lokaci.
Rahoton ya ce ana tsara jerin ne bisa la'akari da wasu ma'aunai na zamantakewa, ra'ayin jama'a da kuma ra'ayoyin masana.
A duk shekara, cibiyar tana ba jama'a damar wata guda domin gabatar da sunayen mutanen da suke ganin sun cancanci shiga jerin, sannan ta tantance shawarwarin da aka gabatar.
Kamar yadda rahoton ya bayyana, ana ba da muhimmanci sosai ga gudummawa da tasirin da mutum ya yi a tsawon rayuwarsa, maimakon ayyukan da yake yi a halin yanzu kawai. Haka kuma, ana ba da fifiko ga mutanen da suka buɗe sabbin hanyoyi a fannonin da suke aiki, ko kuma suka yi tasiri mai girma wanda ya bazu zuwa wurare da dama.
Cibiyar ta raba mutanen da ke cikin jerin zuwa rukuni 13, waɗanda suka haɗa da malaman addini, 'yan siyasa, masu gudanar da harkokin addini, masu wa'azi da jagororin ruhi, masu ayyukan agaji, masu harkokin zamantakewa, 'yan kasuwa, masana kimiyya da fasaha, masu fasaha da al'adu, 'yan jarida, 'yan wasa da kuma ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi.
Sai dai duk shekara ana fuskantar suka kan wannan jerin, inda shigar wasu mutane cikinsa ke haifar da ce-ce-ku-ce.
Misali, wani rahoto da jaridar The Guardian ta wallafa a shekarar 2009 ya bayyana cewa da dama daga cikin mutane 50 da suka zo kan gaba a jerin ko dai shugabannin ƙasashe ne, waɗanda matsayinsu ke ba su damar yin tasiri kai tsaye, ko kuma mutanen da suka gaji muƙamansu daga magabatansu.



























