Me ya rage wa Najeriya wajen kafa ƴansandan jihohi?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Yunƙurin kafa ƴansandan jihohi a Najeriya ya taka wani muhimmin mataki na samun tabbatuwarsa.

A wannan mako ne shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Godswill Akpabio ya ce majalisun dokokin jihohi 30 ne suka amince da ƙudirin.

Ko a ranar Alhamis ma shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Opeyemi Bamidele, ya bayar da tabbacin cewa za a kammala shirin kafa ƴansandan jihohin kafin ko a cikin watan Disamban 2026.

Da yake magana kan ƙudirin, Bamidele, ya ce amincewar majalisun jihohi kusan 30 ta cika sharaɗin buƙatar samun goyon bayan kashi biyu bisa uku na jihohin ƙasar kamar yadda Sashe na 9(2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada.

Dama dai abin da dokar ƙasar ta tadanar shi ne a samu amincewar kashi biyu bisa uku, wato jihohi 24 ciokin 36 na majalisun dokokin jihohin ƙasar kafin a ci gaba da ƙoƙarin aiwatar da ƙudirin.

Yanzu me ya rage?

Sanata Ali Ndume, ɗaya daga cikin ƴanmajalisar dattawan ƙasar ya kuma shaida wa BBC cewa yanzu abin da ya rage shi ne majalisar dokokin ƙasar ta yanke hukunci na gaba.

''Za a kawo batun gaban majalisar dokoki ta ƙasa, inda za mu ƙara muhawara don kaɗa ƙuri'ar amincewa da matakin ko akasin haka'', in ji shi.

Sanatan ya ci gaba da cewa ana buƙatar amincewar kashi biyu bisa uku na duka ƴanmajalisar dokokin ƙasar domin tabbatuwar matakin.

Ɗanmajalisar dattawan ya kuma ce daga nan ne sai a kai wa shugaban ƙasar domin ya sanya hannu don matakin ya zama doka, kuma a fara shirye-shiryen aiwatar da shi.

Matakan amincewa da ƙudurin doka a Najeriya

Barista Sanusi Musa SAN, wani babban lauya kuma masanin kundin tsarin mulkin Najeriya ya ce abin da ya rage yanzu shi ne a kai wa shugaban kasar kudirin domin ya sanya masa hannu.

''Idan aka kai wa shugaban ƙasa shi kuma yana da kwana 30 na ya amince da dokar ya sanya mata hannu, ko kuma ya yi gyare-gyare ya sake aika wa majalisar domin ta sake amincewa da gyaran da ya yi'', in ji shi.

Babban lauyan ya ce idan shugaban ƙasa ya sanya hannu kan ƙudirin shikenan ya zama doka, sai kuma a fara shirye-shiryen fara aiwatar da shi.

Dole ne sai kowace jiha ta yi ƴansandan jiha?

Barista Sanusi Musa ya ce abin da dokar ke nufin shi ne Najeriya ta amince da samar da ƴansandan jihohi.

Amma kuma ba dole ba ne sai kowace jiha ta kafa nata ƴansandan jihar, kamar yadda ya yi ƙarin haske.

''Abin da hakan ke nufi shi ne Najeriya na ta bayar da damar kafa ƴansandan jihohi, don haka duk jihar da ke so, to za ta kai ƙudirin majalisar dokokinta, domin amincewa da ƙudirin'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa idan majalisar jihar ta amince, shikenan jihar sai ta samar da ƴansandanta domin su fara aiki.

''Amma idan jiha ba ta buƙata shikenan, ba sai ta yi ba, tun da ba dole ba ne'', in ƙwararren lauyan.

Yaya aikinsu ƴansandan jiha zai bambanta da na tarayya?

Wata tambaya da ƴanƙasar da dama suka jima suna yi ita ce me zai bambanta ayyukan ƴansandan jihohi da na tarayya?

To amma Barista Sanusi ya ce kundin tsarin mulki zai bambance komai.

''Ai idan shugaban ƙasa ya sanya hannu, to kuma majalisar dokoki za ta zauna ta fayyace ikon kowace runduna'',

Ya ce a inda kuma aka samu cin karon ayyuka, to kundin tsarin mulki zai gyara domin bai wa ƴansandan tarayya fifiko.