Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 30/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 30/10/2026

Rahoto kai-tsaye

Aisha Aliyu Jaafar da Aminu Kutama

  1. Gwamnatin Yemen ta ce ƴan Houthi sun kai hari filin jirgin Aden da Fadar Shugaban Ƙasa

    Gwamnatin Yemen ta ce mayaƙan Huthi masu samun goyon bayan Iran sun kai hari da makamai masu linzami an filin jirgin saman ƙasa da ƙasa na Aden da kuma harabar Fadar Shugaban Ƙasa ta Maashiq.

    Sanarwar da kakakin rundunar sojin gwamnatin Yemen ya fitar ba ta bayyana ko an samu asarar rayuka ko jikkata ba, haka kuma ba a bayyana irin ɓarnar da aka yi ba.

    Har ila yau, ba a tabbatar ko makaman masu linzamin sun kai ga wuraren da aka nufa da su ba.

    Fadar shugaban ƙasa ta Maashiq ita ce hedikwatar gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita, kuma wadda ke samun goyon bayan Saudiyya.

    A ranar Laraba, mayaƙan Houthi da ke iko da babban birnin ƙasar, Sana'a, sun kai hari a gefen filin jirgin saman Aden bayan sun bayyana cewa sun kai farmaki kan wani sansanin sojojin ruwa da kuma wani sansanin soja.

    Lamarin na zuwa ne yayin da yaƙin basasar Yemen da ya sake ƙamari ke ci gaba da ruruwa tsakanin bangarorin da ke rikici.

  2. Limamin Juma'a a Iran ya yi kira da a sauya manufar nukiliyar ƙasar ta dace da buƙatar jama'a

    Mohammad Javad Haj Ali Akbari, wanda ke jagorantar sallar Juma'a na rikon kwarya a Tehran, ya yi kira da a sake nazarin manufar nukiliyar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

    Hakan na nufin sake nazarin manufar nukiliya na iya nufin sauya matsaya ko manufa game da mallakar makaman nukiliya.

    Malam Haj Ali Akbari ya ce a hudubarsa ta sallar Juma'a ranar 30 ga Oktoba, cewa wannan batu ya zama "buƙatar al'umma".

    Kasashen Yamma na zargin Iran da ƙoƙarin mallakar makaman nukiliya a ƙarƙashin tsarin da take ikirarin na zaman lafiya ne.

    Sai dai Iran ta sha musanta wannan zargi, tana mai cewa shirinta na nukiliya yana da manufar lumana kawai.

    A wata magana da ta bambanta da irin kalaman da aka saba ji a baya, limamin sallar Juma'ar na rikon kwarya a Tehran ya ce:

    "Wannan batu ba martani ne na gaggawa ko na fushi kawai ba, a'a ya samo asali ne daga wayewar kai da kuma kwarewar tarihi da al'ummar Iran suka samu wajen fuskantar matsin lambar Amurka."

  3. Ƴanbindiga sun kashe mutum huɗu a jihar Filato duk da dokar hana fita

    Ƴanbindiga sun kashe mutum huɗu a wani hari da suka kai wani ƙauye a Jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya, lamarin da ya sake tayar da hankalin jama'a kan tsaron rayuka duk da dokar hana fita da ake aiwatarwa a yankin, kamar yadda jaridar Sun mai zaman kanta ta ruwaito a ranar 30 ga Oktoba.

    An kai harin ne a ƙauyen Sabon Angwa da ke Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a daren 29 zuwa 30 ga Oktoba, lamarin da ya jefa mazauna yankin cikin fargaba.

    Wani mazaunin yankin, Bulus Jok, ya ce maharan sun aiwatar da harin ne duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya a wasu sassa na Filato domin daƙile hare-hare da kuma dawo da zaman lafiya.

    Jok ya ƙara da cewa maharan sun riƙa harbe duk abin da suka gani a gabansu, abin da ya yi sanadin mutuwar mutum huɗu tare da jefa al’ummar yankin cikin tsananin tsoro.

    Ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa matuƙa, musamman ganin cewa an ce an aika da gargaɗin yiwuwar harin ga hukumomin da abin ya shafa tun kwana guda kafin aukuwar harin.

    A ranar 21 ga Satumba, Gwamna Caleb Mutfwang ya sanya dokar hana fita ta dare ba tare da wa'adin ƙarewa ba a ƙananan hukumomi uku, ciki har da Barkin Ladi, da nufin "kare doka da oda tare da dakile barazanar tsaro da ke ƙara bayyana" bayan jerin hare-hare masu muni da suka yi sanadin asarar rayuka.

  4. Amfani da ƙarfin soji ba zai kawo ƙarshen yaƙin Iran ba - Jamus

    Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya yi kira da a warware rikicin yaƙin ta hanyar diflomasiyya, yayin da ake ta hasashe kan yiwuwar Amurka ta sake kai wasu hare-hare a Iran.

    A yayin da yake kammala ziyararsa a Koriya ta Kudu ranar Juma’a, Merz ya ce: “Abin da kawai zan iya roƙa shi ne dukkan ɓangarorin da ke da ruwa da tsaki su amince cewa babu mafita ta soja ga wannan rikici,” in ji shi.

    Kamfanin dillancin labarai na Jamus (DPA) ya ruwaito cewa Merz yana ƙara da cewa Jamus na ƙoƙarin haɗa kai tare da ƙara yawan ƙoƙarin diflomasiyya ta hanyoyi daban-daban domin kawo ƙarshen yaƙin cikin gaggawa.

    Shugaban gwamnatin Jamus ɗin ya kuma bayyana cewa ƙasarsa na da muradin ganin an kawo ƙarshen rikicin da wuri saboda dalilan tattalin arziki.

    A cewarsa, tashin farashin makamashi sakamakon rikicin ya riga ya jawo wa Turai asarar sama da Euro biliyan 100.

  5. El-Rufai ya yi kira ga Trump da Macron su tabbatar a yi masa adalci

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi kira ga Shugaban Amurka, Donald Trump da Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, tare da sauran shugabannin duniya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da su mayar da hankali kan cigaba da tsare shi da ake yi.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, wanda ya zo daidai da cikarsa kwana 256 a tsare, El-Rufai ya ce yana da haƙƙin samun shari’a ta gaskiya da adalci.

    Tsohon gwamnan ya jaddada cewa samun adalci da kuma damar kare kai a gaban kotu haƙƙoki ne na asali na ɗan Adam, waɗanda bai kamata a riƙa daukarsu a matsayin wata alfarma ba.

    Ya kuma yi kira ga Fadar White House da Gwamnatin Birtaniya da Majalisar Dokokin Birtaniya da kuma manyan kafafen yaɗa labarai na duniya kamar CNN da BBC da Al Jazeera da The New York Times da The Economist a cikin saƙon nasa.

    Kiran nasa ya zo ne kwanaki kaɗan bayan wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yi watsi da buƙatar da ya gabatar cewa ba a gabatar da hujjojin da za su sa ya kare kansa a gaban kotu.

  6. Sojoji sun kashe mayaƙan ISWAP 48 a Borno da Yobe

    Dakarun Rundunar Hadin Gwiwa a Arewa maso Gabashin Najeriya ƙarƙashin Operation Haɗin Kai sun kashe mayaƙan ƙungiyar ISWAP 48 a wasu hare-haren da suka kai a jihohin Borno da Yobe.

    Sojojin sun ce lamarin ya faru ne a garin Bitta da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno, da kuma Buni Yadi da ke ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe, a daren ranar 29 ga Oktoba zuwa safiyar 30 ga Oktoba, 2026.

    A wata sanarwa da Muƙaddashin jami’in yaɗa labarai na Hedikwatar Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya fitar ranar Juma’a, ya ce dakarun sun daƙile wani yunƙurin harin da aka kai a Bitta ta hanyar hadin gwiwar sojojin ƙasa da tallafin jiragen yaƙi.

    Ya ce martanin da dakarun suka mayar ya tarwatsa shirin maharan tare da jawo musu mummunar asara.

    A cewarsa, farmakin martanin ya yi sanadiyar kashe ‘yan ta’adda 48, yayin da dakarun suka kwato makamai da alburusai masu yawa daga hannun maharan.

  7. Yaƙi da Iran zai ƙare nan ba da jimawa ba - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya sake bayyana cewa yana ganin yaƙin da ake yi da Iran zai ƙare nan ba da jimawa ba, sai dai bai yi bayanin yadda hakan zai faru ba.

    A wata hira da ya yi da wani gidan rediyo na cikin gida a birnin Kansas City a yau, gabanin zaɓukan rabin wa’adin mulki a Amurka, Trump ya ce:“Za a kawo ƙarshen wannan lamari nan ba da jimawa ba. Muna buƙatar tabbacin cewa Iran ba za ta taɓa mallakar makamin nukiliya ba.”

    A baya, shugaban na Amurka ya ce ƙasarsa ba za ta kai hari kan Iran ba kafin gudanar da zaɓukan.

  8. Binance ta tabbatar da hare-haren kutse na dala biliyan 6.3

    Dandalin hada-hadar kudaɗen intanet na Binance ya ce yana ƙoƙarin shawo kan wani hari mai sar¡ƙaƙiya da ya shafi kadarori da kuɗinsu ya kai kusan dala biliyan 6.3, inda aka samu nasarar dakatar da kusan rabin adadin don hana satar ɗimbin dukiya.

    Kamfanin, wanda shi ne mafi girman kasuwar musayar kudaɗen intanet a duniya ta fuskar yawan hada-hadar yau da kullum, ya ce bincikensa ya gano wasu ƙarin guraben da masu kutse suka bi wajen kai harin, saɓanin rahotannin farko da suka nuna cewa hari ne da ya samo asali daga kwamfuta guda daya da aka yi wa kutse.

    Tun da farko, kamfanin ya fitar da sanarwa daban-daban, wasu ma suna nuna bambancin matsaya, inda ya jaddada cewa “dukiyar masu amfani tana cikin aminci gaba daya”, amma a lokaci guda ya ce zai ɗauki nauyin duk wata asara da aka yi.

    Binance ta tabbatar a shafinta na X na yankin Latin Amurka cewa jimillar asarar da aka kiyasta ta kai kusan dala biliyan 6.3.

  9. EFCC ta kafa sashen sa ido kan kuɗaɗen jihohi don daƙile cin hanci

    Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta ce ta kafa wani sashe na musamman da zai riƙa sa ido kan shigar da fitar kuɗaɗen gwamnatocin jihohi a wani ɓangare na ƙoƙarinta na hana cin hanci da sauran laifukan kuɗi.

    Shugaban hukumar, Ola Olukoyode, ne ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wata maƙala ta musamman domin murnar cika shekaru 30 da kafuwar jihar Zamfara a birnin Gusau.

    Ya ce a yanzu EFCC tana mayar da hankali wajen hana afkuwar laifukan kuɗi tun kafin su faru, maimakon taƙaita aikinta ga gurfanar da masu aikata laifuka bayan an wawure kuɗaɗen gwamnati.

    A cewarsa, sabon sashen da aka kafa zai riƙa bibiyar harkokin kuɗaɗen gwamnatocin jihohi domin hana karkatar da dukiyar alʼumma da kuma almundahanar kuɗaɗen gwamnati.

    Olukoyode ya ce matakin na da nufin inganta gaskiya, riƙon amana da kuma tabbatar da ana tafiyar da kuɗaɗen alʼumma yadda ya kamata.

  10. Tinubu ya bayyana samun gamsuwa bayan kammala Umrah a Makka

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce ya samu cikakkiyar gamsuwa bayan ya kammala ibadar Umrah, a birnin Makka na Saudiyya.

    Shugaban ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan kammala ibadun, inda ya bayyana Umrah a matsayin wata gagarumar ibada da kuma damar yin addu’a ga Najeriya.

    “Ina godiya ga Allah da Ya ba ni wannan dama,” in ji shi.

    Da aka tambaye shi muhimmancin komawarsa ƙasa mai tsarki bayan ya yi Umrah kafin zaɓen shekarar 2023, Tinubu ya ce lamarin yana da matuƙar muhimmanci a gare shi.

    Ya danganta hakan da ƙaunar da jama’a ke nuna masa da kuma jajircewar da yake yi wajen gudanar da aikinsa, tare da nuna cikakken imani da ikon Allah.

  11. Jiragen ruwa uku sun kama da wuta bayan taka nakiya a mashigar Hormuz

    Sashen rundunar sojin ruwa ta dakarun juyin-juya-hali na Iran wato IRGC ya sanar cewa wani babban jirgin dakon mai da ke ɗauke da fiye da ganga miliyan biyu na mai ya fashe tare da kamawa da wuta bayan ya taka wani bam na ruwa a mashigar Hormuz.

    A cewar IRGC, wannan shi ne jirgin dakon mai na uku da ya fashe kuma ya kama da wuta a ranar Juma'a yayin da yake wucewa ta wata hanya da Jamhuriyar Musulunci ta Iran ke kallon a matsayin "wadda ba ta da izini."

    Rundunar sojin ruwan ta IRGC ta ce an bar jirgin a bakin mashigar ruwa na Hormuz, kuma har yanzu yana ci da wuta.

    Sanarwar ta IRGC ba ta bayyana sunan jirgin ba, ko ƙasarsa, ko wasu bayanai game da shi, haka kuma ba ta bayyana halin da ma'aikatan jirgin suke ciki ba.

    Har zuwa yanzu, ba a samu wata majiyar da ta tabbatar da wannan ikirari ta hanyar mai zaman kanta ba.

  12. An fara kwashe mazauna garin Oleshky na ƙasar Ukraine bayan cimma tsagaita wuta

    An fara gudanar da shirin kwashe mazauna garin Oleshky na ƙasar Ukraine, wanda ke ƙarƙashin ikon Rasha, bayan cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta wucin gadi.

    Ana samar da ababen hawa domin bai wa mutane kusan 750 damar ficewa daga garin idan suna so.

    Rasha ta ce ta gudanar da ayyukan cire nakiyoyi domin bai wa ayarin motocin da ke ɗauke da kayan agaji damar shiga yankin.

    An mamaye Oleshky ne jim kaɗan bayan Rasha ta ƙaddamar da cikakken mamayarta ta Ukraine, kuma garin ya shafe watanni yana fama da ƙarancin abinci, tare da shekaru ba tare da wutar lantarki ko ruwan famfo ba.

    Ɓangarorin biyu Moscow da Kyiv sun yaba wa Uwargidan Shugaban Amurka, Melania Trump, kan rawar da ta taka wajen taimakawa wajen ƙulla wannan yarjejeniyar tsagaita wuta a yankin.

  13. An tura bataliyar sojoji jihar Kano domin inganta tsaro

    Rundunar Sojin Najeriya ta ce ta tura sabuwar bataliya da dakarun da ke sarrafa manyan makamai zuwa Jihar Kano a wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa tsaro da kuma inganta yadda ta ke tunkarar barazanar tsaro da ke kunno kai.

    Babban Kwamandan Runduna ta 1 ta Sojin Nijeriya kuma Kwamandan Sashe na 1 na Rundunar Haɗaka ta Operation Fansan Yamma, Manjo Janar Abubakar Muhammad Wase, ya ce sabbin rundunonin da aka kafa na buƙatar jajircewa, juriya da kuma cikakken goyon baya domin cimma manufofinsu na aiki.

    Wase ya bayyana haka ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai Bataliya ta 24 da ke Tudun Wada da kuma Rundunar Artilari ta 311 da ke Dambatta a Jihar Kano tsakanin ranakun 28 da 29 ga Oktoban 2026.

    A cewar wata sanarwa da Mataimakin Daraktan Hulda da Jama'a na Runduna ta 1, Kanal Abubakar Abdullahi, ya fitar a ranar Alhamis, kuma jaridar Punch ta ruwaito, kwamandan ya tabbatar wa jami'an da sojojin cewa rundunar na aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin Jihar Kano domin taimakawa wadannan sabbin rundunoni soma aiki yadda ya kamata cikin gaggawa.

    Ya kuma yi kira ga al'ummomin da ke karɓar bakuncin sabbin rundunonin da su ba sojoji haɗin kai tare da goyon baya domin inganta zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar.

    Rundunar sojin ta ce kafa waɗannan rundunoni biyu wani ɓangare ne na faɗaɗawa da sake fasalin tsarinta, da nufin ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa da kuma haɓaka saurin mayar da martani ga al'amuran tsaro.

  14. Fafaroma Leo ya nemi kaɗa ƙuri'a a zaɓen rabin wa'adi na Amurka

    Wani ofishin zaɓe a Amurka ya tabbatar da cewa Fafaroma Leo ya nemi a aiko masa da takardar kaɗa ƙuri’a ta gidan waya domin zaɓen rabin wa’adi da za a gudanar mako mai zuwa.

    Fafaroman, wanda aka haifa a birnin Chicago, har yanzu yana da rajistar zaɓe a gundumar Will da ke jihar Illinois, inda masu zaɓe za su zaɓi sabon sanata, da wakilan majalisa, da kuma gwamna.

    Idan ya cike ya kuma mayar da takardar kaɗa ƙuri’arsa, zai zama Paparoma mai ci na farko da ya taɓa kaɗa ƙuri’a a wani zaɓen siyasa na farar hula.

  15. Za mu amince da kafa ƴansandan jihohi nan da Disamba - Majalisar dattawa

    Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawan Najeriya, Opeyemi Bamidele, ya bayar da tabbacin cewa za a kammala shirin kafa ƴansandan jihohi kafin ko a cikin watan Disamban 2026.

    Da yake magana kan ƙudirin a ranar Alhamis, Bamidele, wanda kuma shi ne Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan yi wa Kundin Tsarin Mulki na 1999 gyaran fuska, ya bayyana muhimmancin wannan ci gaba na tarihi, kamar yadda jaridar DailyTrust ta ruwaito.

    Ya ce amincewar majalisun jihohi kusan 30 ta cika sharaɗin buƙatar samun goyon bayan kashi biyu bisa uku na jihohin ƙasar kamar yadda Sashe na 9(2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka yi wa kwaskwarima) ya tanada.

    Da yake bayyana matakai na gaba a majalisa, Shugaban masu rinjayen ya ce abin da ya rage yanzu matakai ne na gudanarwa amma masu matuƙar muhimmanci.

    A cewarsa, Majalisar Dokoki ta Ƙasa za ta tattara rahotannin majalisun dokokin jihohin a hukumance, sannan majalisun biyu su amince da ƙudirin da rinjayen kuri'u, kafin a miƙa shi ga Shugaban Ƙasa domin sanya hannu.

    Ana sa ran kammala wannan tsari kafin ko zuwa watan Disamban 2026.

  16. Jirgin da ya yi hatsari a Sifaniya na gudun da ya kai kilomita 195 - Bincike

    Masu bincike sun ce ɗaya daga cikin jiragen da ya yi hatsari a ranar Laraba a Sifaniya ya na gudu ne da ya kai kilomita ɗari da casa'in da biyar a lokacin da ya ci karo da wani jirgin ƙasa na daban da ke tsaye a kan layin dogon.

    Mutane 69 ne dai suka mutu yayin da har yanzu akwai gommai da ba a iya gano su ba.

    A na ta ɓangaren dai Gwamnati na nuni da cewa kuskuren ɗan adam ne ya haifar da hatsarin.

    Tun da farko, an tabbatar cewa shugaban kamfanin da jirginsa ya yi hatsarin ya gargaɗi Majalisar Dattawan Sifaniya makonni kafin bala'in ya auku, cewa akwai matsaloli a tsarin tafiyar da sufuri a layin dogon.

  17. Netanyahu ya gaza samun rinjayen kafa gwamnati a zaɓen Isra'ila

    Sakamakon ƙarshe na zaɓen 'yan majalisar dokokin Isra'ila ya tabbatar da cewa ƙawancen jam'iyyun Benjamin Netanyahu ya lashe kujeru mafi yawa da guda 53, amma ya gaza samun rinjayen da ake buƙata.

    Ƙawancen 'yan adawa ƙarƙashin jagorancin Gadi Eisenkot ya samu kujeru 48, yayin da jam'iyyun Larabawa suka lashe kujeru 19.

    Dukansu Benjamin Netanyahu da Gadi Eisenkot sun sanar da aniyarsu ta kafa sabuwar gwamnati mai zuwa.

    Tattaunawar kafa gwamnati na iya ɗaukar makonni da dama, kuma idan ba a yi nasara ba, akwai yiwuwar sake gudanar da zaɓe.

    Mista Eisenkot ya zargi Benjamin Netanyahu da ƙoƙarin soke sahihancin sakamakon zaɓen ta hanyar zargin cewa an samu katsalandan daga ƙasashen waje domin amfanin jam'iyyun Larabawa.

    Qatar da Türkiye sun musanta rahotannin da ke cewa sun tsoma baki a zaɓen.

  18. Kamfanin Kirifto na Binance ya tafka asarar kusan dala biliyan 6 bayan an yi masa kutse

    Kamfanin hada-hadar kuɗin kirifto mafi girma a duniya (Binance), ya bayyana cewa ya dakatar da amfani da kadarori masu darajar kusan dala biliyan uku, yayin da yake gudanar da bincike kan wani kutse da ya ke zargin an yi masa.

    Kamfanin ya ce akwai yiwuwar lamarin ya auku ne sakamakon kwamfyutar wani injiniya da masu kutsen suka yi amfani da ita wurin gabatar da buƙataun fitar da kuɗaɗe na bogi.

    Wakiliyar BBC ta ce Binance na bai wa abokan huldarsa tabbacin cewa kuɗaɗensu na tsare, amma babu matakin da zai iya ɗauka kan kuɗaɗen da aka riga aka rasa.

    Ya bayyana cewa "jimillar asarar da kutsen ya haifar na iya kai wa sama da dala biliyan shida.

  19. Sallama

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa kai-tsaye, Assalamu alaikum.

    Barkanmu da safiyar yau Juma'atu babbar rana.

    A yau ma, kamar kullum, za mu kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa kamar a Fesbuk da X da Instagram, sannan ku ziyarci shafinmu na YouTube domin kallon bidiyo.