Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yadda ake koyawa dalibai amfani da makamai a Iran
- Marubuci, Masood Azhar
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Hotuna da rahotanni daga cikin makarantun Iran sun nuna ana koyar da ɗalibai yadda ake amfani da makamai. Bugu da ƙari, an aika wa wasu ɗalibai buƙatar su samar da katunan shaida, yayin da aka ƙaddamar da sababbin shirye-shirye kamar "Matasan Mayaƙa" da "No+Maydaan", waɗanda suka haifar da tambayoyi game da ƙaruwar katsalandan ɗin hukumomin soji da na tsaro a cikin makarantu.
An kuma samar wa wasu ɗalibai katunan shaida da ake ratayawa a wuyansu domin ganewa ko tantance su.
A cewar jami'an Iran, waɗannan shirye-shiryen an tsara su ne domin ba wa ɗalibai horon kariya da kuma cusa masu aƙidar juyin juya hali. Sai dai masu suka na cewa irin waɗannan matakai na ƙara yaɗa tunanin soja a cikin makarantu.
Yarjeniyoyi da ayyukan da aka aiwatar a cikin shekarun baya-bayan nan sun nuna cewa rawar da hukumomin soja da na tsaro ke takawa a makarantu ba ta taƙaita ga ƙungiyar ɗaliban Basij kaɗai ba.
Basij wata ƙungiyar sa-kai ce ta fararen hula mai alaƙa da Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC).
Gwamnatin Shugaba Masoud Pezeshkian ma ta ƙaddamar da wasu sababbin shirye-shirye waɗanda ake zargi da ƙara ƙarfafa tasirin hukumomin soja da na tsaro a makarantun ƙasar.
A ƙarshen shekarun 2000 da farkon shekarun 2010, Basij ta gudanar da wani shiri a makarantu mai suna "Xalqahaa-ye Salihiin" ko "Shajarah Tayyibah Salihiin".
Asalin wannan shiri ya fara ne a masallatai da cibiyoyin Basij da manufar tarbiyyar addini da horas da matasa. Daga baya kuwa makarantu suka fara zama wani ɓangare na ayyukan shirin. Ɗaya daga cikin manufofinsa ita ce jawo ɗalibai zuwa ayyukan Basij.
Masu suka na ganin cewa tanade-tanaden da ke cikin yarjeniyoyin da aka sanya wa hannu na iya bude ƙofa ga faɗaɗa kasancewar ƴan sanda da jami'an tsaro a makarantu.
Yaƙin kwanaki 40 tsakanin Iran da Isra'ila ma ya samar da yanayin da ya sauƙaƙa yaɗuwar wasu daga cikin waɗannan shirye-shiryen.
A watan Fabrairun shekarar da ta gabata, an sanya hannu kan wata yarjejeniya tsakanin Rundunar Ƴansandan Iran da Ma'aikatar Ilimi.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, Ma'aikatar Ilimi ta amince ta yi aiki tare da sassa daban-daban na rundunar ƴan sanda, ciki har da ƴan sandan intanet, masu yaƙi da miyagun ƙwayoyi, ƴan sandan hanya, masu hana aikata laifuka da kuma masu bincike, wajen gudanar da shirye-shirye ga ma'aikata, ɗalibai da iyayensu.
"Matasan Mayaƙa"
Ƙungiyar ɗalibai ta Basij ta fara aiki a makarantu tun shekarar 1990. Sai dai a ranar 1 ga Afrilu, 2026, kafafen yaɗa labarai na Iran sun ba da rahoton gudanar da taron farko na cibiyar ƙasa ta shirin "Matasan Mayaƙa".
Taron ya samu halartar wakilan ƙungiyoyi daban-daban da suka haɗa da Basij.
Shugaban ƙungiyar ɗaliban Basij kuma kwamandan cibiyar "Matasan Mayaƙa", Siavash Moslemi, ya ce:
"Matasanmu na iya zama ƙarfi mafi tasiri a tituna wajen kare juyin juya hali."
A cewarsa, manufofin cibiyar sun haɗa da horas da matasa kan hare-haren yanar gizo da koyar da sa ido da tattara bayanai domin gano masu kutse a unguwanni da kuma shigar da matasa cikin gangami da zanga-zanga, sai kuma horas da su yadda ake amfani da makamai.
A watan da ya gabata, Moslemi ya sanar da ƙaddamar da wani sabon shiri mai suna "No+Maydaan Student League", wanda ya bayyana a matsayin "aiki na haɗin gwiwa na biyu".
An aiwatar da wannan shiri tare da haɗin gwiwar Basij, sashen al'adu na Ma'aikatar Ilimi da sauran hukumomi da dama.
An bayyana manufar shirin a matsayin gano baiwar ɗalibai a fannoni daban-daban da kuma ba su damar bunƙasa ƙwarewarsu.
Shirin ya shafi ɗaliban firamare, sakandare da manyan makarantu. Wani ɓangare na shirin ya ƙunshi horon soja ga ɗalibai.
Kwanan nan, kafofin yaɗa labarai ciki har da Hukumar labaran ɗalibai ta PANA sun wallafa hotuna da ke nuna ana koya wa ɗalibai yadda ake amfani da makamai.
Sai dai kakakin Ma'aikatar Ilimi ya musanta rahotannin da ke cewa ana bai wa ɗalibai katunan shaida masu alaƙa da yaƙi.
Daga musanta samar da "katunan yaƙi" zuwa damuwar iyaye
Duk da sabbin shirye-shiryen da ake aiwatarwa, ilimin kariya da tsaro ya kasance wani ɓangare na tsarin ilimin Iran tsawon shekaru.
Tun daga shekarar 1986, wannan fanni ya zama wajibi a makarantun sakandare.
Darasin ya ƙunshi koyarwar aji da kuma horo a aikace, inda wani ɓangare na horon ke gudana tare da cibiyoyin horarwa na Basij.
Littafin "Shirye-shiryen Tsaro" ya bayyana darasin a matsayin wajibi ga ɗalibai.
A cikin watannin baya-bayan nan, kafafen sada zumunta sun cika da hotuna da rahotanni da ke nuna jami'an soji a wasu makarantu musamman na ƙananan yara, lamarin da ya haifar da damuwa kan faɗaɗar horon soji a cikin tsarin ilimi.
Bayan yaɗuwar hotunan yara suna rarrabawa da haɗa makamai a makarantu da wuraren taro, an kuma ruwaito cewa wasu makarantu sun buƙaci iyaye su samar wa 'ya'yansu katunan shaida.
Wannan ya haifar da martani mai ƙarfi a kafafen sada zumunta.
A garuruwa kamar Bandar Abbas, Kermanshah, Mashhad, Urmia da Karaj, wasu iyaye sun ce makarantu sun nemi su samar da katunan shaida ga ƴaƴansu ko kuma makarantar ta samar da su.
Muhawarar ta ƙara zafi bayan wani bidiyo ya nuna jami'in kashe gobara yana ziyartar wata makarantar 'yan mata domin wani aikin da ya shafi tsaro.
A bidiyon, an ce ɗaliban sun sanya katunan da ke ɗauke da bayanansu.
Lokacin da aka tambayi ma'aikatan makarantar game da kamanceceniyar katunan da na soji, sun amsa cewa:
"Umarnin ya fito ne daga sama."
Sai dai har yanzu ba a san wace hukuma ce ake nufi da wannan magana ba.
Ma'aikatar Ilimi ta sake musanta cewa ana bai wa ɗalibai "katunan yaƙi" tare da cewa shugabannin makarantu ba su da ikon haifar da firgici a tsakanin iyalai.
Tsohuwar takaddama
Batun tasirin yara da matasa a tsarin al'adun yaƙi da sadaukarwa na Jamhuriyar Musulunci ya daɗe yana jawo muhawara.
Ɗaya daga cikin fitattun misalai shi ne labarin Mohammad Hossein Fahmideh, yaro ɗan shekara 13 wanda Ruhollah Khomeini ya kira "jagoranmu".
Hotonsa ya kasance a kan kuɗin Iran na tsawon lokaci, kuma labarinsa ya zama wani ɓangare na littattafan makaranta.
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun dade suna jayayya da hukumomin Iran kan batun amfani da yara da matasa a ayyukan soja da na tsaro.
Iran ta amince da Yarjejeniyar Haƙƙin Yara ta Majalisar Ɗinkin Duniya tun shekarar 1993.
A ƙarƙashin sashe na 38 na yarjejeniyar, wajibi ne ƙasashe su hana yara masu ƙasa da shekara 15 shiga yaƙe-yaƙe kai tsaye ko ɗaukar su aikin soja.
Dokar Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) ma ta bayyana ɗaukar yara ƙasa da shekara 15 cikin yaƙi a matsayin laifin yaƙi.
Jami'an Iran na cewa matasan da suka shiga yaƙin Iran da Iraki sun yi hakan ne bisa son rai don kare ƙasarsu.
Sai dai masu suka suna nuna wasu tarukan Basij ko IRGC da ke karɓar masu sa-kai tun daga shekara 12.
Tasiri ga sabuwar al'umma
Muhawarar ko makarantu sun fara rikiɗewa zuwa cibiyoyin soja ta ƙara ƙarfi a shekarun baya-bayan nan.
Masanin falsafa da ilimin addini Mohammad Mojtahed Shabestari ya taɓa rubuta wa Shugaba Masoud Pezeshkian wasiƙa yana gargaɗin cewa makarantu na komawa "sansanonin tilasta sallar jam'i".
Ya roƙi shugaban ƙasar da kada ya bari makarantu su zama sansanonin addini.
Yayin da hukumomin Iran ke kallon waɗannan shirye-shirye a matsayin wata hanya ta shirya matasa masu biyayya ga juyin juya hali da kuma kare ƙasa, masu suka na cewa suna ƙara lalata iyaka tsakanin ilimin farar hula, horon kariya da kuma shigar da yara cikin harkokin soja da tsaro.
A lokacin da Iran ta fuskanci yaƙe-yaƙe biyu kuma ake ci gaba da tattaunawa kan yiwuwar wani sabon rikicin soja, akwai tambayoyi game da ko horar da yara kan makamai ya dace da bukatun tsaro na zamani, da kuma inda ya kamata a ja layi tsakanin ilimin kariya da kuma amfani da yara a harkokin soji da na tsaro.