Dalilai huɗu da suka haifar da tashin farashin man fetur a Najeriya

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

A ƴan kwanakin nan, farashin man fetur ya sake tashi a sassa daban-daban na Najeriya, inda a wasu gidajen mai a Abuja, babban birnin ƙasar ake sayar da litar fetur kan naira 1,400.

Lamarin ya jawo damuwa tsakanin masu ababen hawa da ƴan kasuwa da fasinjoji da kuma al'umma baki ɗaya, kasancewar fetur na da tasiri kai tsaye kan farashin kaya da sufuri.

Tashin farashin na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke kokawa da tsadar rayuwa, lamarin da ya sa mutane da dama ke tambayar abin da ke haddasa ƙarin farashin duk da matakan da gwamnati ke ɗauka a ɓangaren makamashi.

Masana tattalin arziƙi da harkokin mai na ganin cewa abubuwa da dama ne suka haɗu suka haifar da wannan yanayi, kama daga ƙaruwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya zuwa matsalolin samarwa da rarraba man a cikin gida.

A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi Farfesa Ahmad Adamu na Jami'ar Philomath da ke Abuja kuma ƙwararren masanin tattalin arzikin man fetur, ya bayyana wasu dalilai da ya ce sun taimaka wajen janyo tashin farashin man fetur da ake gani a yanzu.

Tashin farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya

Farfesa Adamu ya ce babban dalilin shi ne tashin farashin ɗanyen man fetur a kasuwannin duniya.

Masanin tattalin arziƙin na man fetur ya ce yaƙin Iran na daga cikin batutuwan da suka ƙara tsananta tsadar ɗanyen mai, musamman yadda mashigar Hormuz ta zama tsakiyar yaƙin.

A ranar Lahadi ne Amurka ta sake ƙaddamar da hare-hare kan tsibirin Larck na Iran, inda ita ma ta mayar da martani kan wasu sansanonin sojin Amurka a yankin Gulf.

''A farkon makon nan ana sayar da gangar ɗanyen mai samfurin Brent kan dala 85, amma zuwa Talata ya koma 92, kuma ana ganin farashin zai ƙaru sakamakon wannan abu da ya faru,'' in ji shi.

Hasashen ƙarancin mai nan gaba a kasuwa

Masanin na harkokin man fetur ya ce wani ƙarin dalilin shi ne hasashen da aka yi cewa nan gaba za a samu ƙarancin man fetur a kasuwar duniya.

''Saboda haka yanzu duk wani kwantiragin cinikin mai da ake ƙullawa yanzu za ka tarar ana yin sa ne da tsada'', a cewar malamin jami'ar.

Ya ƙara da cewa wannan ne dalilin da ya sa matatun mai ke ƙara farashi a yanzu ta yadda za su iya samun kuɗin saro wani ɗanyen man a nan gaba.

Rashin tallafi daga gwamnati

Farfesa Adamu ya ce a baya idan aka samu yanayin da farashin man fetur ya tashi a a kasuwannin duniya, to gwamnatin Najeriya kan tallafa domin rage wa ƴan ƙasa raɗaɗi.

''Kasancewar yanzu gwamnatin Najeriya ta cire tallafin man fetur, ya sa yanzu ƴan ƙasa ne ke ji a jikinsu, idan aka samu tashin farashin man a kasuwannin duniya'', in ji masanin harkokin man.

A shekarar 2023 ne dai Shugaba Tinubu ya sanar da cire tallafin man fetur, saboda abin da ya bayyana da cewa tsiraru na arzurta kansu da tallafin.

A baya-bayan ɗantakarar shugaban ƙasar na jam'iyyar ADC, Atiku Abubakar ya alƙawarta mayar da tallafin man idan aka zaɓe shi a 2027, kodayake gwamnatin ta soki matakin Atikun da cewa siyasa ce kawai.

Taƙaddamar Dangote da ƴankasuwa

Wani dalilin kamar yadda masanin ya bayyana shi ne taƙaddama tsakanin Matatar Dangote da kuma masu kasuwancin man fetur kan batun shigar da man fetur daga ƙasashen waje.

A makon da ya gabata ne Matatar Dangote ta ce za ta fara fitar da tataccen manta zuwa kasashen waje, kasancewar gwamnatin Najeriya na barin ƴankasuwa suna shigar da tataccen mai daga waje, maimakon saye daga wurinsa.

Ana sa ran wannan mataki zai iya fara aiki tun a wannan makon, matuƙar ba a samu matsaya ba bayan ƙarin tattaunawa.

Sai dai Farfesa Ahmed Adamu ya ce doka ta bai wa ɗankasuwa damar saro mansa a duk inda yake so.

''Ita matatar mai ta Dangote tana da ƙarfin tace man da ma ya fi ƙarfin buƙatun Najeriya, sannan a nasu ɓangare su ma ƴan kasuwa suna da damar sayo man fetur a duk inda suke so'', in ji masanin tattalin arzikin na man fetur.

Ya ƙara da cewa idan Dangote yana so, zai iya karya farashinsa, kuma idan ya yi hakan ƴan kasuwar ba za su iya ci gaba da saro mai daga waje ba.

Ko za a iya rage farashin fetur a ƙasar?

Farfesa Ahmed Adamu ya ce akwai hanyoyi biyu da gwamnatin Najeriya za ta iya tallafawa wajen rage wa yan ƙasar wannan raɗaɗi.

''Hanya ta farko mai gajeren zango ce da ta ƙunshi amfani da matatar Dangote wajen samun sassauci'', in ji shi,

A cewar masanin ya kamata gwamnati ta yi amfani da matatar Dangote wajen sayar masa da mai da sauƙi da nufin idan ya tace shi ma ya sayar wa ƙasa da sauƙi.

Dangane da mataki na dogon zango, masanin ya ce ya kamata gwamnati da ƴan ƙasa su fara shirin rage dogaro da man fetur wajen rayuwarsu ta yau da kullum.

''Ai yanzu ka ga mafi yawan man fetur ana amfani da shi ne wajen sufuri, amma yanzu duniya ta fara mayar da hankali wajen amfani da motoci masu amfani da lantarki, ya kamata ƴan Najeriya su fara shirin irin wannan rayuwa'', in ji shi.

Ya ce yana da kyau gwamnatin Najeriya ta yi amfani da iskar gas wajen samar da wutar lantarki da ƴan ƙasa za su yi amfani da su.