Real Madrid ta dage kan Rodri, Arsenal za ta gabatar da tayin Álvarez

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid na aiki kan yarjejeniyar ɗaukar ɗan wasan tsakiya na Manchester City, Rodri, inda ƙungiyar ta Sifaniya ke da kwarin gwiwar cewa za ta iya cimma matsaya kan kyaftin ɗin na Sifaniya mai shekara 30. (The Athletic)
Arsenal na nazarin gabatar da tayi wanda zai haɗa da ɗan wasa da kuɗi domin sayen ɗan wasan gaba na Argentina kuma tauraron Atletico Madrid, Julián Álvarez mai shekara 26. Yarjejeniyar za ta iya haɗawa da komawar ɗan wasan gaban Sweden Viktor Gyökeres mai shekara 28 zuwa ƙungiyar ta Sifaniya. (Cadena SER)
Roma na sha'awar ɗaukar ɗan wasan gefe na Norway, Oscar Bobb mai shekara 23, daga Fulham, duk da cewa watanni shida kacal suka wuce da komawarsa daga Manchester City. (Football Italia)
Paris Saint-Germain har yanzu ba ta kai tayin fam miliyan 102 (euro miliyan 120) a hukumance ba domin sayen ɗan wasan gefen Ivory Coast na RB Leipzig, Yan Diomande mai shekara 19. Wannan ya ba Liverpool, Arsenal, Real Madrid da Manchester City sabuwar dama ta shiga fafatawar nemansa. (Bild)
Ɗan wasan tsakiya na Brazil kuma tauraron Newcastle United, Bruno Guimarães mai shekara 28, shi ne babban burin Arsenal a wannan bazarar, sai dai kuma ɗan wasan tsakiya na Bournemouth kuma ɗan tawagar Ingila, Alex Scott mai shekara 22, na cikin zaɓin da ƙungiyar ke dubawa. (Telegraph)
Rahotanni sun ce za a yi watsi da tayin fam miliyan 70 da Arsenal ta yi wa Newcastle domin sayen Guimarães, duk da cewa ɗan wasan yana son komawa Emirates. (The Times)
Haka kuma ana cewa kocin Arsenal Mikel Arteta a shirye yake ya kai tayin har zuwa fam miliyan 90 domin kammala cinikin ɗan wasan na Brazil. (Mundo Deportivo)
Manchester United ba ta da niyyar sayar da kyaftin dinta, Bruno Fernandes mai shekara 31, duk da rade-radin da ke alaƙanta ɗan wasan tsakiyar na Portugal da barin Old Trafford. (TeamTalk)
Ƙungiyar Como ta Italiya na sa ran ganawa da Chelsea a ranar Asabar yayin da take ƙoƙarin ɗaukar ɗan bayan Ingila Trevoh Chalobah mai shekara 27. Sai dai Chelsea ba za ta amince da sayar da shi kan ƙasa da fam miliyan 30 ba. (Sky Italia)
Chelsea ta gabatar da tayin farko domin sayen matashin ɗan wasan gefe na Bosnia-Herzegovina kuma na Bayer Leverkusen, Kerim Alajbegovic mai shekara 18. (Kicker)
Arsenal da Hamburg na tattaunawa kan makomar ɗan wasan tsakiyar Portugal Fábio Vieira mai shekara 26, wanda ke son komawa ƙungiyar Bundesliga bayan zaman aron da ya yi a can a kakar wasan da ta gabata. (Florian Plettenberg)
An kuma gayyaci ɗan wasan gaban Ingila Marcus Rashford mai shekara 28 ya shiga cikin wani shirin fim na bayan-fage da Amazon ke shirya wa Manchester United. Rahotanni na nuna hakan alama ce cewa manyan jami'an ƙungiyar na son ci gaba da riƙe shi a Old Trafford. (Mirror)















