KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 24/07/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, Juma'a 24/07/2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido
  • xxx
  • Zanga-zanga a aAfirka ta Kudu
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. MDD ta buƙaci a kuɓutar da matuƙa jiragen ruwan da suka maƙale a Hormuz

    Shugaban hukumar kare haƙƙin biladama ta Majalisar Dinkin Duniya, Volker Türk, ya yi kira ga ƙasashen da ke da hannu a yaƙin Iran su taimaka wajen fitar da matuƙan jiragen ruwa kusan 6,000 da suka maƙale a mashigar Hormuz.

    kakakinsa ya ce ya kamata ɓangarorin da ke rikicin su sauƙaƙa hanyoyin da za su ba su damar wucewa cikin aminci.

    Yayin da faɗan ke ci gaba da tsananta, hukumomin Iran sun gargaɗi fararen hula su nisanci sojojin Amurka da ke yankin.

    Haka kuma Iran na ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya kan kadarori da sansanoni Amurka, a matsayin martani ga hare-haren bama-bamai da Amurka ke ci gaba da kai mata.

  2. 'Matakai uku da muke bi don ceto ɗaliban da aka sace a Borno'

    Gwamnan Borno

    Asalin hoton, Governor Borno/X

    Fiye da wata biyu bayan sace ɗalibai a makarantu uku da ke garin Mussa a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, har yanzu iyaye na jiran ganin an ceto ƴaƴan nasu.

    Yawaitar satar yara a makarantun Najeriya a baya-bayan nan na daga cikin abubuwa da ke nuna cewa har yanzu matsalar tsaron da ƙasar ke fama da ita na nan, duk da iƙirarin da gwamnatin ƙasar ke yi na cewa tana bakin ƙoƙarinta.

    A baya-bayan nan ƴan bindigar sun ƙara ƙaimi wajen sace ɗalibai a sassa daban-daban na ƙasar.

    A ranar 10 ga Yulin 2026, gwamnatin Najeriya ta sanar da ceto wasu ɗalibai da malaman makarantar da aka yi garkuwa da su a jihar Oyo, kwanaki 56 bayan sace su daga makarantarsu da ke ƙaramar hukumar Orire a yankin Ogbomoso na jihar Oyo.

    Gwamnatin Bornon tya bayyana wasu matakai uku da ta ce tana ɗauka don tabbatar da kuɓutar da yaran.

  3. Jamus ta naɗa Jurgen Klopp sabon kocin ƙasar

    Jurgen Klopp

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar ƙwallon ƙafar Jamus ta bayyana tsohon kocin Liverpool, Jurgen Klopp, a matsayin sabon kocin tawagar ƙasar.

    Naɗin nasa na zuwa kwanaki bayan murabus ɗin Julian Nagelsmann, wanda ya ajiye aiki bayan da tawagar Jamus ta fice daga Gasar Kofin Duniya tun a matakin ƴan 32.

    Klopp, wanda ke cikin manajojin a duniyar ƙwallon ƙafa - bai riƙe wani aikin horaswa ba tun bayan da ya bar Liverpool shekaru biyu da suka gabata.

    Aikinsa na baya-bayan nan shi ne shugaban harkokin ƙwallon ƙafa na duniya na kamfanin Red Bull, tare da yin sharhi a talabijin kan harkokin ƙwallon kafa.

    Yanzu yana fuskantar ƙalubalen farfaɗo da martabar wannan babbar tawagar Turai, wadda ta taɓa lashe Kofin Duniya har sau huɗu a tarihinta.

  4. Gwamnan Sokoto ya bai wa ma'aikatan jihar hutu don rajistar zaɓe

    Ahmad Aliyu Sokoto

    Asalin hoton, Ahmad Aliyu Sokoto/FB

    Gwamnan jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya ayyana yau Juma'a 24 ga watan Yuli a matsayin ranar hutu ga ma'aikatan jihar domin waɗanda ba su yi rajistar zaɓe ba su zamu damar yin hakan.

    Cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan, Gwamnan, Abubakar Bawa ya fitar ya ce gwamnan ya buƙaci ma'aikatan gwamnati a jihar su yi rajistar domin samun damar kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen ƙasar da ke tafe cikin shekara mai zuwa.

    Gwamnan ya ce ya ɗauki matakin ne domin tabbatar da ma'aiakatn jihar sun samu cikakkiyar damar aiwatar da ƴancinsu.

    A baya-bayan nan ne dai hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da tsawaita wa'adin rajistar zaɓen da mako biyu, wanda zai ƙare ranar 26 ga watan Yulin da muke ciki.

    Gwamna Ahmad Aliyu ya buƙaci sauran al'ummar jihar da ba su yi rajistar zaɓen ba, su yi amfani da damar tsawaita wa'adin don yin rajistar.

  5. Matakin ministan Isra'ila kan Masallacin Ƙudus ya fusata musulmi

    Masallacin Kudus

    Asalin hoton, Getty Images

    Kasashe takwas na Larabawa da na Musulunci sun yi Allah wadai da shigar wani ministan Isra'ila - da kuma yahudawan ƴan kama wuri zauna cikin Masallacin Al-Aqsa - cikin Masallacin Al'aqsa da ke Ƙudus.

    Cikin wata sanarwar hadin gwiwa ministocin harkokin wajen ƙasashen Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Jordan da Masar da Qatar da Turkiyya da Pakistan da kuma Indonesia sun yi kakkausar suka kan shigar Itamar Ben-Gvir, Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra'ila, tare da wasu yahudawan Masallacin, wanda ke birnin Ƙudus a gaɓar Yamma da Kogin Jordan.

    Sanarwar, wadda aka fitar da maraicen Alhamis, ta bayyana cewa wannan mataki ya saɓa wa matsayin tarihi da na doka da aka tanadar wa Masallacin Al-Aqsa, tare da bayyana shi a matsayin tsokanar da ba za a amince da ita ba, wadda za ta iya haddasa karin tashin hankali a yankin.

    Ƙasashen na musulmi sun kuma buƙaci:

    • Mutunta matsayar Jordan a matsayin mai kula da wurin ibadar mai tsarki ga Musulmi da Kiristoci a Birnin Kudus.
    • Kin amincewa da duk wani yunƙuri na sauya matsayin tarihi da na doka da ya shafi Masallacin Ƙudus
    • Bukatar dakatar da matakan abin da suka kira tsokana da kuma ɗaukar matakai ba tare da tuntɓa ba, waɗanda za su iya jefa tsaro da zaman lafiyar yankin cikin hadari.
    • Bin dokokin duniya da kuma ƙudurorin Majalisar Dinkin Duniya da suka shafi Birnin Kudus.

    An fitar da sanarwar ne bayan da Mista Itamar Ben-Gvir ya shiga harabar Masallacin Al-Aqsa tare da ɗaruruwan yahudawa ƴan kama wuri zauna.

    Matakin ya jawo suka daga Falasdinawa da Jordan da kuma wasu ƙasashen Larabawa da na Musulunci.

  6. Sojojin Najeriya na farautar wani soja kan zargin sayar wa ƴanbindiga kakin soji

    Sojan da ake nema

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Sashen kula da kayan aiki na rundunar sojin ƙasa ta Najeriya ta ayyana neman ɗaya daga cikin jami'anta ruwa a jallo, saboda zarginsa da sayar da kakin soji ga ''ƴanta'adda da masu aikata laifuka''.

    Jami'in sojin wanda kurtu ne, mai suna Mohammed Yusuf Amutu tuni ya tsare daga wurin aikinsa bayan da zargin da ake yi masa ya fito fili.

    Cikin wata sanarwar da sashen kula da kayan aikin soji na rundunar sojin ya fitar, ya ce yana ƙoƙarin gano inda sojan yake domin kama shi don fuskantar ladabtarwa.

    Rundunar ta jaddada matsayin na rashin lamuntar saɓa wa aiki ko rashin ɗa'a ko duk wani abu da zai janyo wa rundunar sojin ƙasar barazana.

    ''Duk wani jami'inmu da muka samu da laifin taimaka wa ayyukan ƴanta'adda da masu aikata laifuka ko wasu ƙungiyoyi da gwamnati ta haramta, ta hanyar sayar musu da kakin soji ko wasu kayyaki, to zai fuskanci hukunci ƙarƙashin dokokin soji da kundin tsarin mulkin ƙasa'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

    Sojan Najeriya da ake nema

    Asalin hoton, Nigerian Army/X

    Sanarwar ta kuma yi kira ga mutane su taimaka wajen kai rahoton jami'in a duk inda suka ganshi.

    ''Muna kira ga jama'a duk inda suka ganshi su yi ƙoƙarin sanar da sojoji mafi kusa da su ko wata hukumar tsaro mafi kusa'', in ji sanarwar.

  7. Trump ya sanar da ƙara haraji ga ƙasashe ciki har da Najeriya

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, A watan Afrilun 2025 ma Trump ya sanya wa wasu ƙasashe haraji

    Trump ya sanar da ƙaƙaba sabbin harajin shigar da kayayyaki Amurka daga wasu ƙasashe da dama, ciki har da Najeriya.

    Shugaba Trump ya ɗauki matakin ne a ƙoƙarin farfaɗo da manufarsa ta kare masana’antun cikin gida - matakin da ake ta ƙalubalanta a kotu.

    Sabbin harajin, waɗanda suka kai tsakanin kashi 10 zuwa 12.5 cikin 100, sun dogara ne kan zargin cewa abokan hulɗar kasuwancin Amurka ba sa yin abin da ya dace wajen daƙile ayyukan tilasta wa jama'a.

    Matakin ya maye gurbin wani harajin wucin gadi da aka sanya bayan da Kotun Ƙolin Amurka ta soke wani jerin harajin daban-daban da gwamnatin Trump ta kakaba a baya.

    Ƙasashe da dama sun nuna rashin jin daɗinsu game da wannan mataki, inda Brazil da Australia, suka ce babu wani dalili na sabon harajin.

    Yayin da Japan ta bayyana matakin a matsayin abin takaici, New Zealand cewa ta yi ta ji matuƙar takaici da matakin na Amurka.

  8. Hare-haren Amurka sun faɗa tashar jiragen ruwan Iran

    Gidan talabijin na gwamnatin Iran ya ce an ji ƙarar fashe-fashe sakamakon hare-haren makamai masu linzami da Amurka ta kai a wurare da dama da ke gaɓar Tekun Fasha.

    Rahotannin sun ce hare-haren sun shafi tsibirin Qeshm da kuma tashar jiragen ruwa ta Bandar Abbas, tare da wasu bayanan da ke nuna cewa an kuma samu fashe-fashe a yankunan yamma da tsakiyar Iran ɗin.

    Haka kuma rahotannin sun ce an kunna garkuwar sararin samaniya a babban birnin ƙasar Tehran.

    Lamarin na zuwa ne bayan Shugaba Trump na Amurka, ya yi barazanar abin da ya kira hukunta Iran da ƙawayenta na Houthi da ke Yemen, a kan hare-haren da mayaƙan Houthin ke kaiwa kan jiragen ruwa na dakon man Saudiyya a Tekun Maliya.

  9. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Juma'a, haji babbar rana kamar yadda Hausawa ke yi mata kirara.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku domin kawo muku halin da duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.