Luguden bam na jirgin yaƙi ya kashe gomman fararen hula a Borno da Yobe

Asalin hoton, Nigeria army
Rahotonni daga jihohin Borno da Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya na cewa wani harin jirgin yaƙi ya kashe gomman mutane da suka je cin kasuwar Jilli da ke kan iyakar ƙananan hukumomin Gubio da Geidam a jihohin biyu.
Wata majiyar tsaro daga yankin ta tabbatar wa BBC faruwar lamari, amma ta ce ba za ta yi ƙarin haske kan lamarin ba.
Hon. Lawan Zanna Nur kansilar mazaɓar Futchimiram da ke yankin ƙaramar hukumar Geidam ɗaya daga cikin wuraren da lamarin ya faru ya ce an kai harin ne ranar Asabar da tsakar rana, lokacin da ake tsaka da cin kasuwar ta Jilli.
''Kodayake abin ya faru da rana da misalai ƙarfe 2 zuwa 3 na rana, labari bai zo mana ba sai da daddare, saboda nisa da kuma rashin sabis ɗin waya a yankin'', kamar yadda ya shaida wa BBC.
''Mutanen suna tsaka da cin kasuwa sai suka fara jin ruwan bama-bamai daga sama ba tare da ankarewa ba'', kamar yadda ya bayyana.
Kafofin yaɗa labaran Najeriya sun ruwaito cewa waɗanda suka mutu a harin sun kai 50 zuwa 60, kodayake sun ce akwai wahalar tantance adadin saboda nisa da rashin sabis ɗin waya a yankin.
Hon Zanna Nur ya ce gomman mutane ne suka mutu sakamakon harin, inda da dama suka jikkata waɗanda yanzu haka ke asibitoci daban-daban tsakanin Borno da Yobe.
''Daga bayanan a muka ji daga bakunan waɗanda suka jikkata shi ne waɗanda suka mutu sun kai aƙalla mutum 200'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.
Hon. Zanna wanda ya ziyarci babban asibitin Geidam inda aka kwantar da suka jikkata ya ce a gabansa mutum huɗu suka mutu cikin waɗanda aka kai asibitin na Geidam.
Kasuwar ta Jilli ta sharaha ne da ci mako-mako a kowace ranar Asabar, inda ake hada-hadar abubuwa da dama ciki har da kayan abinci.
Kansilan yankin ya ce wasu daga waɗanda suka jikkata an kai asibitocin garuruwa da dama na jihar Borno, kasancewar kasuwar na kan iyakar jihohin biyu.
Me hukumomin Najeriya suka ce?
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kai hari kan ƴanta'adda a yankin na Jilli, amma ba ta tabbatar da kai wa kasuwa hari ko kashe fararen hula ba.
Ckin wata sanarwar da rundunar Operation Hadin Kai mai yaƙi da yanbindiga a yankin arewa maso gabashin ƙasar ta fitar, ta ce ta kai harin wanda ta kira tsararre a kan maɓoyar ƴanta'addan a yankin bayan samun sahihan bayanan sirri.
Sanarwar sojin ta ce sojojin sun kai harin ne kan mafakar ƴanbindigar da ke ƙauyen Jilli - wanda mazaunansa sun riga sun tsere.
''Yanki ne da ya yi ƙaurin suna wajen harkokin mayaƙan ISWAP'', in ji sanarwar sojojin.
Sojojin sun ci gaba da cewa a ranar 11 ga watan Afrilu sun samu rahatonni da dama da suka ce an ga maya kan ISWAP a kan ababen hawa da suka ha da da motar yaƙi da babura a yankin.
Sojojin sun kuma jaddada haramcin hawa babur a jihohin Borno da Yobe, da aka jima yi a jihohin biyu.
Hare-haren kuskuren jiragen yaƙi a Najeriya
A lokuta da dama a Najeriya jami'an tsaro kan yi kuskuren kai hare-hare kan fararen hula a ƙoƙarinsu na yaƙi da ƴanbindiga a ƙasar.
A baya BBC ta taɓa yin nazarin wasu hare-haren kuskure 12 da sojojin ƙasar suka kai kan fararen hula.
A watan Disamban 2023 ma wani harin kuskure na jirgi maras matuƙi da sojojin ƙasar suka kai garin Tudun Biri a jihar Kaduna ya kashe gomman mutane.











