Badaƙalar kuɗi 5 da suka shafi kamfanin man fetur na Najeriya

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Isiyaku Muhammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Ana ci gaba da tafka muhawara kan wa'adin da kwamitin majalisar dattawa mai kula da kuɗaɗen al'umma wato Public Accounts Committee, ya bai wa masu binciken kuɗi na kamfanin man fetur na Najeriya NNPC Ltd.
Kwamitin ya bai wa kamfanin wa'adin mako guda ya gabatar da takardun da za su yi cikakken bayani kan naira tiriliyan 210 da ake zargin ba a fahimci bayanansu ba a cikin kundin tsare-tsaren kuɗin kamfanin.
Yawan kuɗin ne ya sa mutane suka fara tofa albarkacin bakinsu, inda wasu ke ganin akwai buƙatar a tabbatar an bincika tare da bayyana sakamakon binciken da kyau domin al'umma.
Kamfanin Man Fetur na Najeriya (NNPC) ya sha fuskantar zarge-zargen badaƙalar kuɗi a tsawon shekaru, daga zargin ɓacewar kuɗin man fetur zuwa rikicin tallafin man fetur.
Wannan rahoto ya duba manyan badaƙala biyar da suka fi ɗaukar hankali, yadda suka faru, binciken da aka yi, da kuma abin da ya biyo baya.
Zargin ɓacewar dala biliyan 20
A shekarar 2014, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya zargi NNPC da rashin shigar da kusan dala biliyan 20 daga kuɗin da aka samu daga sayar da ɗanyen mai zuwa asusun gwamnatin tarayya, duk da daga baya ya ce dala biliyan 12.
Wannan zargi ya haifar da babbar muhawara a ƙasar tare da kafa bincike na musamman da kamfanin PricewaterhouseCoopers (PwC) ya gudanar.
An yi zargin ne a zamanin tshuwar minista Diezani Alieson-Madueke, inda ak yi zargin cewa akwai badaƙala a kuɗaɗen da suka shafi sayar da mai, tare da gano wasu kuɗaɗen da ake buƙatar a mayar zuwa asusun gwamnatin tarayya, duk da cewa NNPC ta musanta zarge-zargen cewa an ɓoye kuɗi.
Sai dai daga bisani kamfanin na NNPC ya ce bincike da PricewaterhouseCoopers (PwC) ya yi ya wanke shi.
Manajan-darakta na kamfanin na lokacin, Joseph Dawha ne ya bayyana haka a wata zantawa da ya yi da manema labarai, inda ya ce an gudanar da bincike kuma an gano cewa babu kuɗin da ya ɓace.
Badaƙalar tallafin man fetur – 2012
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wannan na daga cikin manyan badaƙala da suka fi girgiza Najeriya. Bayan cire tallafin man fetur a shekarar 2012, majalisar wakilai ta kafa kwamitin bincike wanda ya gano zarge-zargen almundahana wajen biyan kuɗin tallafin man fetur ga wasu kamfanonin shigo da mai.
Majalisar ta ce ta gano cewa an karkatar da kusan dala biliyan 6 daga asusun tallafin man fetur cikin shekara biyu da suka gabata.
An kafa kwamitin binciken harkokin man fetur ɗin ne bayan zanga-zangar da ta ɓarke a faɗin ƙasar a watan Janairun shekarar, sakamakon yunƙurin gwamnati na cire tallafin man fetur a zamanin Goodluck Jonathan.
Binciken ya ce an gano cewa wasu kamfanonin shigo da man fetur guda 15 sun karɓi sama da dala miliyan 300 a shekara biyu ba tare da sun shigo da wani man fetur ɗin ba. Haka kuma, an ce sama da ƴan kasuwar mai 100 sun karɓi irin wannan kuɗi sau da dama.
Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa shi ne tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya, Farouk Lawan wanda kotu ta yanke wa hukuncin shekara biyar a gidan yari, amma yanzu ya shaƙi iskar ƴanci.
Zargin badaƙalar tallafin kananzir
A wani rahoto da jaridar Premium Times ta yi a shekarar 2014, ta bankaɗo zargin da aka yi wa NNPC na cewa iƙirarin kamfanin cewa sama da kashi 80 cikin 100 na dala biliyan 10.8 da ba a mayar wa asusun gwamnatin tarayya suna tafiya ne wajen tallafin kananzir na iya kasancewa ba gaskiya.
Rahoton ya nuna cewa wasu takardun sirri da aka samu sun nuna cewa tsohon shugaban ƙasa Marigayi Umaru Musa Yar'adua ya bayar da umarnin a cire tallafin kananzir daga tsarin Petroleum Support Fund (PSF) a shekarar 2009, saboda tallafin ba ya isa ga talakawan da aka nufa.
A shekarar 2011, ministar man fetur ta lokacin, Diezani Alison-Madueke, ta ƙaddamar da shirin Kero-Direct, wanda NNPC ta ce zai samar da kananzir ga jama'a a farashin N50 kan kowace lita.
Sai dai rahoton ya nuna cewa kwamitin majalisar wakilai da ya binciki tallafin man fetur a shekarar 2012 ya bayyana shirin a matsayin wata hanya ta damfarar ƴan Najeriya da kuma karɓar kuɗi daga asusun PSF.
Badaƙalar kuɗin gyara matatun mai

Asalin hoton, Getty Images
A watan Maris na shekarar 2021 ne majalisar wakilai ta ce za ta gudanar da bincike kan kuɗaɗen da aka kashe wajen gyaran matatun man fetur na ƙasar, inda ƴan majalisar suka yi zargin cewa an kashe aƙalla dala biliyan 25 wajen gyaran matatun man fetur a tsawon shekara, amma ba a gani a ƙasa ba.
Majalisar ta ɗauki matakin ne jim kaɗan bayan gwamnatin Muhammadu Buhari ta amince da kashe dala biliyan 1.5 domin gyaran matatar mai ta Fatakwal da ke jihar Rivers.
Wannan ya sa majalisar ta ce ya kamata a tabbatar da an yi amfani da kuɗin yadda ya kamata, ganin cewa an shafe shekaru ana kashe makudan kuɗaɗe wajen gyaran matatun amma ba a ganin komai.
A wannan shekarar ta 2026 ma Hukumar EFCC ta ce ta kwato kuɗi da kadarori da suka kai sama da naira biliyan 38.66 a wani bincike da take gudanarwa kan zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware domin gyaran manyan matatun man fetur na gwamnati a Najeriya.
Badaƙalar naira triliyan 210
A shekarar 2026 ce kwamitin majalisar dattawa buƙaci shugabannin NNPCL su bayyana a gabansa domin yin bayani kan Naira tiriliyan 210 da ba a fahimci yadda aka yi da su a cikin rahotan kuɗin kamfanin daga shekarar 2017 zuwa 2023.
Har yanzu dai ana cigaba da gudanar da binciken, inda shugaban kwamitin Aliyu Wadada ya nanata cewa amsoshin da NNPCL ya bayar kan tambayoyi 19 kan binciken badaƙalar ba su gamsu ba.
Ya ce ƴan Najeriya suna buƙatar cikakken bayanai masu inganci da za a iya gamsuwa sosai.











