Ƴan uwa da za su buga kofin duniya a ƙasa daban-daban

Asalin hoton, Getty Images
Gasar Kofin Duniya ta 2026 ba kawai za ta zama ta tarihi ba, saboda yawan ƙasashe 48 da za su halarta a karon farko da yawan wasannin da za a kece raini da tarin filayen da za a buga fafatawar.
Wani abin mamaki da ke jan hankali shi ne tawaga takwas da ƴan uwan juna za su kalabalanci juna a cikin gasar. Abin ban sha'awa shi ne ba duka ƴan'uwa ne ke wakiltar ƙasa ɗaya ba — wasu ma za su fafata da juna a bangarori daban-daban.
Wannan lamari zai ƙara wa gasar armashi, domin ba kawai karawa ce tsakanin ƙasashe ba, har ma wasanni ne da za a kece raini tsakanin iyalai da yawa.
Ƴan'uwa da za su buga wa ƙasa ɗaya gasar kofin duniya a 2026
Wasu daga cikin ƴan'uwan suna cikin tawaga ɗaya da za su wakilta a bana, kuma za su yi ƙoƙarin kai ƙasashensu ga nasarar lashe kofin bana.
Daga cikin su akwai:
Jurrien Timber da Quinten Timber na tawagar Netherlands
Lucas Hernández da Theo Hernández na tawagar Faransa
Laros Duarte da Deroy Duarte na tawagar Cape Verde
Leandro Bacuna da Juninho Bacuna na tawagar Curacao
A wasu daga cikin waɗannan ƙasashe, har ma ƴan'uwa na fafatawa don neman matsayi shiga cikin tawaga, abin da ke ƙara zafi da kalubale tsakanin iayalan da hakan ta kasance da su.
Ƴan'uwan da za su buga wa kasashe daban-daban gasar kofin duniya ta 2026
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne akwai wasu ƴan'uwa da za su buga wa ƙasashe daban-daban gasar cin kofin duniya ta 2026, ma'ana za su iya fuskantar juna a filin tamaula.
Mafi shahara daga ciki su ne:
Nico Williams na tawagar Sifaniya da ɗan'uwansa Iñaki Williams daga Ghana
Desire Doué na tawagar Faransa da ɗan'uwansa Guéla Doué daga Ivory Coast
Brian Brobbey na Netherlands da ɗan'uwansa Derrick Luckassen Brobbey daga Ghana
Harry Souttar na Australia da John Souttar na Scotland
Wannan yana nufin za a iya samun wasannin da ɗan'uwa zai fafata da ɗan'uwansa a babbar gasar tamaula ta duniya ta bana, ko kuma zai taimaka wajen fitar da shi daga gasar.
Me ya sa wannan yake da muhimmanci?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A gasar da ƙasashe 48 za su kece raini, damar samun irin wannan yanayi ya ƙaru sosai. Ba kawai saboda yawan ƴan ƙwallo ba ne, amma saboda ƙasashe da dama suna da ƴancin ɗaukar ƴan wasa ƴan asalin su daga ko'ina a duniya.
Wannan yana haifar da sabon salo a gasar inda iyalai da tushen ɗan ƙwallo da burin da tawaga ke fatan cimma a wasannin ƙwallon kafa.
Tarihin ƴan'uwa da suka kara a gasar duniya
Ba sabon abu ba ne ganin ƴan uwa suna wakiltar kasarsu a lokacin gasar cin kofin duniya. A baya mun ga:
Jordan da André Ayew na Ghana
Eden da Thorgan Hazard na Belgium
Amma a wannan shekarar ta 2026 abin ya wuce haka, domin yanzu ba kawai ƴan'uwa suke buga wa kasa ɗaya wasa ba — suna iya kasancewa a bangarori daban-daban na duniya.
Kofin Duniya na 2026 zai zama ba kawai gasar ƙwallon ƙafa ba, har ma gasar da za ta shafi labaran iyali, soyayya da shakuwa, kuma karawa ce tsakanin jini da juna. Wannan ne ya sa hakan zai zama ɗaya daga batun da za ake tattaunawa a lokacin gasar kofin duniya daga cikin labaran da za su fi jan hankali a duniya.
Ganin ƴan'uwa suna wasa tare ko kuma suna kalubalantar juna zai ƙara wa gasar wani sabon salo da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihi.










