KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 13/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar, 13 ga watan Yuni, 2026.

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Kutama
  • xxx
  • XXX
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Hezbollah ta ce ta yi artabu da sojojin Isra’ila a Kudancin Lebanon

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Hezbollah ta sanar da cewa dakarunta sun yi arangama da sojojin Isra’ila da ke ƙoƙarin isa garin Majdal Zun da ke kudancin Lebanon.

    Ta ce ta harba roƙoƙi kan sojojin Isra’ila a ranar Alhamis, lamarin da ya tilasta musu ja da baya.

    A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ƙara da cewa a ranar Juma’a ta sake kai hare-hare da makamai masu linzami da kuma roƙoƙi.

    Har ila yau, ta ce ta kai wasu ƙarin hare-hare kan sojojin Isra’ila a yankunan kudancin ƙasar.

    A ɓangare guda, sojojin Isra’ila sun buƙaci mazauna wasu ƙauyuka uku a kudancin Lebanon da su bar gidajensu, yayin da rahotanni suka ce ana ci gaba da kai hare-hare a yankuna daban-daban.

    Hukumomin labaran Lebanon sun kuma ruwaito ƙararrakin fashe-fashe masu ƙarfi da harba makamai a kusa da yankin Ali Taher.

  2. Farashin mai ya faɗi sosai saboda hasashen cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya faɗi sosai cikin kusan watanni huɗu, sakamakon fatan da ake da shi na cewa za a cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran nan ba da jimawa ba.

    Farashin danyen mai na Brent ya sauka zuwa dala 87.33 a kowanne ganga, inda ya ragu da dala 3.05, wato kimanin kashi 3.4 cikin ɗari idan aka kwatanta da ranar da ta gabata.

    Haka zalika, farashin danyen mai na Amurka ya sauka zuwa dala 84.88 a ganga, ragin dala 2.83, ko kuma kashi 3.2 cikin ɗari kenan.

    Wannan shi ne mafi ƙasƙancin farashin danyen mai na Texas cikin kusan watanni uku, tun daga watan Afrilu da ya gabata.

    Masu kasuwa na ƙara samun kwarin gwiwa cewa yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran na dab da kammaluwa, abin da ke rage fargabar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

    Wani masani a harkar saka hannun jari, John Kilduff na kamfanin Again Capital, ya ce abin da ya janyo faduwar farashin shi ne bayanan da Iran ta bayar na cewa akwai takardar fahimtar juna da ake shirin kullawa da Amurka, wanda ya sa masu zuba jari ke sa ran samun daidaito a kasuwar mai.

  3. Ɗalibai da malamai da aka sace na cikin gandun dajin Old Oyo - Makinde

    ....

    Asalin hoton, Seyi Makinde/X

    Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa ɗalibai da malamai da aka sace a karamar hukumar Oriire na jihar har yanzu suna hannun masu garkuwa a cikin gandun dajin Old Oyo National Park.

    Ya bayyana hakan ne a sabon bayanin da ya fitar game da ƙoƙarin ceto su, kusan makonni hudu bayan aukuwar lamarin.

    Makinde ya ce jami’an tsaro na ci gaba da aiki tukuru domin kubutar da wadanda aka sace a yayin hare-haren da aka kai makarantu a garuruwan Yawota da Ahoro-Esinle a ranar 15 ga watan Mayu, 2026.

    A cewarsa, rahotannin sirri sun nuna cewa har yanzu ana tsare da su a cikin babbar gandun dajin Old Oyo, wadda ke da fadin kusan kilomita murabba’i 2,500 a yankuna da dama na jihar.

    Ya kara da cewa girma da wahalar shiga yankin na kawo kalubale ga jami’an tsaro, don haka ana bukatar tsari mai kyau da hadin gwiwa domin samun nasarar aikin ceto.

    Gwamnan ya tabbatar wa al’umma cewa ana bin duk wata sahihiyar hanya domin ganin an ceto wadanda aka sace ba tare da wata illa ba.

    Ya kuma bukaci jama’a da su kasance cikin shiri su kai rahoton duk wani abin da ke da alaka da laifi ta hanyar layin gaggawa na jihar, tare da gargadin cewa yada jita-jita na iya kawo cikas ga aikin ceto

  4. Iran ta yi iƙirarin nasara yayin da tace saura ƙiris a cimma matsaya da Amurka

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa ƙasarsa ta samu muhimman nasarori waɗanda suka kawo su kusa da cimma yarjejeniya da Amurka domin kawo ƙarshen rikicin da ake fama da shi.

    Ya ce batutuwan da ake tattaunawa sun haɗa har da batun buɗe mashigar ruwan Hormuz, wanda ya ce yana da matuƙar muhimmanci a yarjejeniyar.

    A wata hira da ya yi a gidan talabijin na cikin gida a Iran, Araqchi ya ce bangarorin biyu sun kai mataki mafi kusa da cimma matsaya fiye da kowane lokaci a baya.

    Ya bayyana cewa yanzu haka ana dab da fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka, yana mai cewa “an kusa cimma matsaya, saura kaɗan ne.”

    Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai na Iran da su guji yin hasashen da zai iya jefa shakku ko ya dagula tattaunawar, yana mai cewa irin waɗannan rahotanni na iya lalata damar da ake da ita na cimma yarjejeniya.

    A cewarsa, takardar fahimtar juna da ake aiki a kanta ba ta wuce shafi ɗaya da rabi zuwa biyu ba, amma duk da haka an shafe watanni biyu ana nazari da tattauna kowace kalma da ke cikinta sosai.

    Araqchi ya ƙara da cewa an kasance ana sanar da hukumomin tsaro, ciki har da Majalisar Koli ta Tsaron Ƙasa, game da duk wani ci gaba a kai a kai.

    A ƙarshe ya jaddada cewa sakamakon wannan aiki zai ƙara ƙarfafa matsayi da ƙarfin Iran a cikin gida da kuma a idon ƙasashen duniya, yana mai cewa mashigar Hormuz na ƙarƙashin ikon Iran da Oman.

  5. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin BBC Hausa barkanmu da ganin safiyar yau Asabar.

    Aisha Babangida ce ke fatan kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na Facebook da X da kuma Whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.