Ko Trump zai yi nasara kan toshe tashoshin ruwan Iran?

Lokacin karatu: Minti 4

Babu mai tantamar cewa sojojin Amurka za su iya toshe tashohin ruwan Iran sannan su ƙaƙaba takunkumi kan jiragen dakon kaya a yankin Gulf. Amma abin tambayar a nan shi ne, me ake so a cimma da matakin?

"Ina ganin abu ne mai yiwuwa kuma ko shakka babu yana da ƙarancin haɗari idan aka kwatanta da ɗaya zaɓin da ake da shi, wanda za a matsar da Iran baya daga gaɓar ruwanta ƙarfi da yaji, sannan a samarwa jiragen da ke wajen hanyar wucewa," in ji wani sojan ruwan Amurka da ya yi ritaya Mark Montgomery a hirarsa da BBC.

Wasu matakan da Shugaban Amurka Donald Trump ya riƙa yunkurin kawowa a makonnin bayan nan, kamar kwace tsuburin Kharl da rakiyar da sojoji za su riƙa yiwa jiragen ruwan da za su bi mashigar Hormuz, da an yi hakan da ya haifar da haɗari mai yawa kuma zai ja asarar kuɗaɗe.

A wannan matakin da ake ciki, dakarin Amurka za su zama ba su da kariya daga hare-haren jarage marasa matukan Iran da makaman rokarsu da jiragen ruwansu masu gudu. Haka kuma zaman tashoshinsu ba tsaro zai sake haifar da wata barazanar.

A ɗaya hannun kuma, tsoshe tashoshin zai baiwa jiragen ruwan yaki na sojojin Amurka damar zama cikin aminci daga nesa a tekun na Oman, su riƙa sanya idanu kan kowanne jirgi da ya fito daga tashar ruwan Iran su dakatar da su idan da buƙatar hakan.

"Haɗarin ba shi da yawa idan an kwatanta da zamansu a mashigar Hormuz," in ji Admiral Montgomery.

Sojojin ruwan Amurka da wasu dakarun tsaro na musamman da jiragen ruwan yaƙi da jirage masu saukar angulu na da ƙarfin ba da wannan tsaron.

Yadda aka tsare tashoshin Venezuela da Cuba a baya-bayan nan ya nuna Amurka za ta iya ƙara hakan.

A kuma farkon watan Janairun wannan shekarar da aka kwace tankar man Rasha a tekun North Atlantic ya nuna za s iya ci gaba da irin wannan aiki a ko ina aka ga dama.

Cibiyar tsare-tsaren yaƙi ta Amurka ta ce aikin tare tashoshin Iran ɗin za a yi sa ne ba tare da wani son zuciya ba, amma ba zai shafi jiragen da suka fito daga wasu tashoshin da ba na Iran ba.

A cewar cibiyar jiragen da ke ɗauke da kayan agaji za a riƙa barinsu suna wucewa, sai dai ko wanne ne "sai an yi masa bincike".

Anya wannan matakin zai yi aiki kuwa?

A zahiri dabarar take. Tun da aka fara yaƙin Iran na iya fitar da manta ta yakin Gilf, tana samun biliyoyin dala, yayin da a gefe guda kuma ta hana wasu ƙasashen yakin sayar da na su.

Idan Amurka ta yi nasarar tashe tashoshin za ta dakatar da wannan abu na Iran, sannan ta hana gwamnatin IRan samun kuɗin da ba ta cancance su ba, kuma ta raunata tattalin arziƙinta.

Amma Iran wadda ta nuna jajurcewa kan hare-haren Amurka da Isra'ila za ta ɗauki wannan matakin a matsayin sabon rikici, kuma zai iya ƙara tashin farashin mai a duniya.

"Sun yi amannar za su iya jurewa wannan yanayin shi ma, tun da itama Amurka tashin farashin man zai shafeta, kuma daga baya ƙasashen Gulf za su matsawa Amurka lamba domin su buɗe mashigar," in ji David Satterfield, tsohon jakada na musamman na ayyukan jinkai na Amurka a Gabas ta tsakiya a hirarsa da BBC.

Ya ce Amurka ta raina Iran ne a lissafin da ta yi tun da fari.

"Suna tsammanin sun yi nasara," in ji David Satterfield. "Iran ta yi ammanar za ta iya jure wani raɗaɗin sama da Amurka."

Kwararru kan harkokin sojin ruwa suna sanya ido kan jiragen ruwa da suke barin tashoshin Iran suke bin mashigar Hormuz domin tabbatar da matakin da Amurka ta ɗauka na rufe tashoshin.

" Ina ganin jirage na wucewa ta wurin kai tsaye," in ji Michel Wiese Bookman,wani mai sharhi kan harkokin leken asiri a teku. " Idan ni matuƙin jirgn ruwa ne, zan shiga damuwa."

"Mun ga sauye-sauye kan yadda jiragen ruwa ke gudanar da ayyukansu tun bayan sanarwar da Trump ya fitar," In ji Richad Mead editan jaridar Lloyd List mai wallafa kasuwancin harkokin ruwa.

Ya ce cikin awa 48 da suka wuce sun ta ganin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz, mafi yawa tun bayan fara yaƙin a ƙarshen watan Fabirairu, jiragen da suke wucewa an sansu an san daga inda suka fito da inda za su.

" Teku sai hanƙoro take saboda kaiwa da kawowar da ake yi cikinta," in ji shi.

Yayin da batun tsagaita ruwa ke ci gaba da tafiya, yaƙin Iran ya zama toshe mashiga tsakanin masu adawa da juna biyu, yayin da kowa ya sa tattalin arziƙin duniya a gabansa.

Yayin da ake cewa China na ci gaba da baiwa Iran kwarin gwiwar shiga cikin tattaunawar ta Islamabad, Washington na fatan matakinta zai ƙara matsawa Beijing ta matsawa Tehran.

China ita ce ta fi sayan man Iran a duniya, kuma ba za ta iya jurar wannan dogon lokacin ba babu mai.

Wannan matakin na Donald Trump zai iya zama wani abu kamar caca, sai dai za mu jira mu gani matakin zai fi kai wa bango a nan gaba.