Yadda cacar baki ta kaure tsakanin Donald Trump da Fafaroma Leo

Lokacin karatu: Minti 5

Shugaban Amurka Donald Trump da Fafaroma Leo XIV sun fara cacar baki game da yakin Iran, bayan Fafaroman ya bayyana sunan Trump karara a karon farko.

An zaɓi Fafaroma Leo XIV a watan Mayu 2025, kuma shi ne Fafaroma na farko da ya fito daga Amurka. Lokacin da ya hau mulki, ya fi nuna natsuwa da rashin shiga rikice-rikicen siyasa kai tsaye, sabanin magabacinsa Fafaroma Francis, wanda ya kan yi suka a fili ga gwamnatin Trump.

Sai dai a 'yan watanni da suka gabata, dangantaka tsakanin Fadar Vatican da Fadar White House ta fara yin sanyi. Wannan sabon cacar baki ya fito fili ne saboda bambancin ra'ayi kan yaki a Iran, wanda ya sa sabanin ya bayyana a sarari.

Manufofin harkokin waje

Cacar bakin ya ƙaru ne bayan Trump ya yi wani dogon rubutu a kafar sada zumunta inda ya soki Fafaroman, yana cewa ba ya goyon bayan ra'ayinsa kan tsaro da harkokin ƙasashen waje.

Ya kuma ce ba ya son wani Fafaroma da ke ganin ya kamata Iran ta mallaki makamin nukiliya.

Trump ya ƙara zargin cewa Fafaroman yana sukar wasu matakan Amurka, ciki har da hare-hare da ta kai wasu ƙasashe. Daga baya ma ya wallafa wani hoto da aka ƙirƙira da fasahar AI a shafukan sada zumunta da ta nuna shi kamar Yesu kafin daga bisani aka goge hoton.

Waɗannan kalamai sun biyo bayan sukar da Fafaroma Leo XIV ya yi kan barazanar da Trump ya yi cewa Amurka na iya lalata Iran gaba daya idan ba ta bi wasu sharuɗɗa ba.

Fafaroman ya ce ba za a amince da irin wannan barazanar ba kuma ya bukaci shugabanni su yi aiki domin samar da zaman lafiya.

A baya ma Fafaroman ya ambaci Trump kai tsaye, yana cewa yana fatan shugaban zai nemi hanyar rage rikici maimakon ƙara tsananta shi.

A wani jawabi kuma, Fafaroman ya sake kira ga shugabanni da su dakatar da zubar da jini.

Ra'ayin Fafaroma Leo XIV kan Iran ya samo asali ne daga irin matsayinsa da ya riƙa ɗauka a wasu rikice-rikicen duniya.

Kwanaki kaɗan bayan zaɓensa a shekarar da ta gabata, ya yi kira da a tsagaita wuta nan take a Gaza, a saki waɗanda aka yi garkuwa da su, kuma a ba da damar kai agajin jin ƙai ba tare da wani cikas ba.

A watan Agustan 2025, ya soki abin da ya kira hukunta jama'a gaba ɗaya da kuma tilasta musu ƙaura, yana mai cewa halin da ake ciki a Gaza "ba abin amincewa da shi bane."

A hudubarsa ta Kirsimeti, Fafaroman ya yi magana kan wahalar da mutane ke ciki a Gaza, yana ambaton yadda suke zaune a cikin tantuna suna fuskantar ruwan sama mai karfi da iska da sanyi.

Ko da yake a wancan lokaci bai samu sabani kai tsaye da Trump ba kan Gaza, jami'an diflomasiyya na Vatican sun nuna damuwa a ɓoye kan yadda Fafaroman ke bayyana ra'ayyinsa wanda mutane da dama suka fassara a matsayin suka ga matakan Amurka da Isra'ila.

A watan Janairu na wannan shekarar kuma, Fafaroman ya nuna damuwa bayan sojojin Amurka sun kama tsohon shugaban Venezuela Nicolás Maduro a Caracas suka kai shi New York domin shari'a.

Ya ce ya kamata jin daɗin al'ummar Venezuela ya fi komai muhimmanci, tare da kira da a kauce wa tashin hankali, a bi hanyoyin adalci da zaman lafiya.

Haka kuma ya bukaci a mutunta ikon cin gashin kai na Venezuela, a kiyaye dokoki kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada, da kuma mutunta haƙƙin ɗan adam da na jama'a.

Batun shige da fice

Batun shige da fice ya zama ɗaya daga cikin manyan dalilan cacar baki tsakanin Fafaroma Leo XIV da Donald Trump.

Fafaroman ya sha sukar tsauraran manufofin shige da fice na Trump, yana kallon lamarin a matsayin wajibi bisa koyarwar Injila da ke ƙarfafa tausayi da mutunta martabar ɗan Adam.

A watan Nuwamban 2025, ya ce ana mu'amala da baƙi a Amurka cikin "rashin mutunci mai tsanani", yana maimaita ra'ayin limaman Katolika na Amurka da suka soki korar jama'a da yawa da kuma gargadin cewa hakan na janyo tsoro da damuwa sakamakon farmakin jami'an shige da fice.

Fafaroman ya ce dole ne a nemo hanyoyin mu'amala da mutane cikin adalci da mutunci, duk da cewa ya amince cewa kowace ƙasa na da 'yancin tsara yadda da kuma lokacin da mutane za su shiga cikinta.

A wani jawabi da ya yi a dandalin St Peter's a watan Oktoba, ya bukaci Katolika da kada su nuna wariya da rashin kulawa ga 'yan gudun hijira.

Addini da ikon siyasa

Sako da Trump ya wallafa a shafukan sada zumunta ya ƙara tsananta cacar baki da Fafaroma Leo XIV inda ya zarge shi da wuce gona da iri wajen sukar sa a matsayin shugaban Amurka. Ya ce yana yin abin da aka zaɓe shi ya yi, kuma ya ƙara da cewa bai yarda da salon Fafaroman ba.

Haka kuma, Trump ya yi iƙirarin cewa Fafaroman ya samu muƙaminsa ne saboda kasancewarsa Ba'amurke, yana mai cewa da ba shi a fadar White House, da Leo ba zai zama Fafaroma ba.

Sai dai Fafaroma Leo ya ƙi shiga ce-ce-ku-ce kai tsaye. Ya ce shi ba ɗan siyasa ba ne, kuma ba ya son muhawara da Trump. Ya jaddada cewa zai ci gaba da yin magana kan zaman lafiya da tattaunawa, ba tare da tsoro ba.

Rahotanni sun nuna cewa Trump ya samu goyon bayan kashi 55 na mabiya Katolika a zaɓen 2024, kuma gwamnatin sa na da alaƙa da shugabannin addini masu ra'ayin mazan jiya, tare da ɗaukar batun yaki da Iran da fuskar addini.

Abun da masana ke tunani

Masana sun ce sauyin salon magana da matsayar Fafaroma Leo XIV na nuna cewa yana son zama muryar ɗabi'a a duniya, musamman a matsayin da zai daidaita tasirin manufofin harkokin waje na Donald Trump.

Wani masani dan Italiya, Massimo Faggioli, ya ce Fafaroman ba ya son a zargi Vatican da yin laushi ga manufofin Trump saboda shi Ba'amurke ne. Ya kuma ƙara da cewa duk lokacin da Leo ya yi magana, yana yin hakan cikin taka-tsantsan, kuma hakan ba haɗari ba ne.

Cardinal Blase Cupich daga Chicago, wanda na kusa da Fafaroman ne ya ce Leo na bin tsohuwar al'adar Fafaroma na kira ga shugabanni su kauce wa yaki. Sai dai ya nuna cewa abin da ya bambanta yanzu shi ne salon saƙon, domin mutane musamman masu magana da Turanci na jin saƙon cikin harshe da suka saba da shi.

Marie Dennis, tsohuwar shugabar ƙungiyar zaman lafiya ta Katolika Pax Christi, ta ce kalaman Fafaroman na baya-bayan nan da kuma kiransa kai tsaye ga Trump na nuna raɗaɗin zuciya sakamakon ci gaba da tashin hankali.

Ta ƙara da cewa Fafaroman na ƙoƙarin isar da saƙo ga mutanen da suka gaji da rikici, yana ƙarfafa buƙatar shugabanci mai ƙarfi da zai kawo zaman lafiya.