Carrick na sa ran United za ta taka rawar gani a kan Leeds, Premier League
Michael Carrick yana sa ran cewa filin wasa na Old Trafford zai cika da sowa da tafi sosai a lokacin da Manchester United za ta karɓi bakuncin Leeds United a Premier League ranar Litinin.
Carrick ya taɓa buga wannan wasan sau ɗaya kacal a 2011 a gasar League Cup, kuma tsawon lokacinsa a Manchester United ya yi ne a lokacin da Leeds ke can tana buga Championship.
Amma kocin ya ce ya san muhimmancin wannan fafatawar ta hamayya sosai, kuma yana sa ran magoya baya za su nuna hakan a daren Litinin.
Ya ce:
“Ina ganin wannan shi ne dalilin da ake da hamayya a ƙwallon ƙafa. Ƙarfin gwiwa da nuna damuwa da kuma sha’awa duk suna cikin wasan hamayya, kuma duk da haka dole a kiyaye iyaka, amma wannan na daga cikin abin da muke so a karawar.”
“Da fatan zai ƙara ɗaga matakin wasan, kuma filin wasa zai mara mana baya. Na tabbata hakan zai faru. Mun riga mun san yadda wasa a gida yake da fuskantar kalubale, kuma ƴan wasa suna amfana daga hakan sosai.”
Mataimakin kocin Carrick, Jonathan Woodgate, wanda ya shahara a matsayin ɗan wasa a Elland Road, yana gudun yin magana mai tsawo kan tsohuwar hamayyar da ke tsakanin ƙungiyoyin biyu.