KAI TSAYE, Labaran wasannin BBC Hausa daga ranar 12 zuwa 18 ga watan Afrilun 2026

Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga ranar Lahadi 12 zuwa Juma'a 18 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Mohammed Abdu

  1. Carrick na sa ran United za ta taka rawar gani a kan Leeds, Premier League

    Micheal Carrick

    Asalin hoton, Getty Images

    Michael Carrick yana sa ran cewa filin wasa na Old Trafford zai cika da sowa da tafi sosai a lokacin da Manchester United za ta karɓi bakuncin Leeds United a Premier League ranar Litinin.

    Carrick ya taɓa buga wannan wasan sau ɗaya kacal a 2011 a gasar League Cup, kuma tsawon lokacinsa a Manchester United ya yi ne a lokacin da Leeds ke can tana buga Championship.

    Amma kocin ya ce ya san muhimmancin wannan fafatawar ta hamayya sosai, kuma yana sa ran magoya baya za su nuna hakan a daren Litinin.

    Ya ce:

    “Ina ganin wannan shi ne dalilin da ake da hamayya a ƙwallon ƙafa. Ƙarfin gwiwa da nuna damuwa da kuma sha’awa duk suna cikin wasan hamayya, kuma duk da haka dole a kiyaye iyaka, amma wannan na daga cikin abin da muke so a karawar.”

    “Da fatan zai ƙara ɗaga matakin wasan, kuma filin wasa zai mara mana baya. Na tabbata hakan zai faru. Mun riga mun san yadda wasa a gida yake da fuskantar kalubale, kuma ƴan wasa suna amfana daga hakan sosai.”

    Mataimakin kocin Carrick, Jonathan Woodgate, wanda ya shahara a matsayin ɗan wasa a Elland Road, yana gudun yin magana mai tsawo kan tsohuwar hamayyar da ke tsakanin ƙungiyoyin biyu.

  2. De Zerbi ya fara da shan kashi a Tottenham mai shirin faɗuwa daga Premier, Premier League

    Roberto De Zerbi

    Asalin hoton, Getty Images

    Tottenham ta ƙara shiga cikin matsalar fargabar faduwa daga Premier League a kakar nan, bayan da sabon kocinta Roberto De Zerbi ya fara aiki da rashin nasara a wasan da Sunderland ta ci 1-0 a ranar Lahadi, wanda ya sa ƙungiyar ta koma matsayi na ukun karshen teburin gasar.

    Sunderland ta ci ƙwallon ta hannun Nordi Mukiel, hakan ya kara mata burin shiga gurbin zakarun Turai a baɗi, Tottenham kuwa ta kara shiga matsala.

    Duk da cewa Tottenham ta nuna ƙoƙari da jajircewa, ba ta nuna wani ci gaba ba a fannin cin ƙwallaye, kuma hakan ya sa ta yi rashin nasararsu a Premier League a wasa 14 a jere ba tare da cin wasa ba.

    Yanzu tana da maki 30 daga wasa 32 a Premier, kuma tana kasan West Ham United da tazarar maki biyu, wacce ke ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da ke kusa da yankin faduwa.

    A gefe guda, wannan ita ce nasarar farko ta Sunderland a kan Tottenham a Premier League tun 2010, kuma hakan ya sa Sunderland ta koma matsayi na 10 da maki 46, tana da tazarar maki biyu tsakaninta da Chelsea FC da ke matsayi na shida, wadda za ta buga wasa da Manchester City daga baya a gida.

  3. Forest ta raba maki mai mahimmaci da Aston Villa a Premier, Premier League

    Neco Williams

    Asalin hoton, Getty Images

    Nottingham Forest ta samu muhimin maki a fafutukar ta na tsira daga faduwa daga Premier League a kakar nan, bayan da ta tashi 1-1 da Aston Villa a filin wasa na City Ground.

    Ƙwallon da Nottingham Forest ta ci ta hannun Neco Williams mintuna bakwai kafin hutun rabin lokaci ta soke na farko da Murillo ya zura a raga wanda ya ci gida, hakan ya sa ƙungiyar ta yi wasa huɗu ba tare da rashin nasara ba a ƙarƙashin Vitor Pereira.

    Yayin da Sunderland ta ci Tottenham Hotspur 1-0 a dai ranar Lahadin, wannan sakamakon wasan Nottingham Forest ya sa ta ci gaba da zama da tazarar maki uku tsakani da ƴan ukun karshen teburu, kuma saura wasa shida suka rage a kammala kakar nan.

    A gefe guda, Aston Villa, wadda ke ƙara ƙarfafa burinta na samun tikitin UEFA Champions League, za ta yi nadamar damarmaki da ta kasa amfana, musamman daga wajen Morgan Rogers da Ollie Watkins.

    Duk da haka, ƙungiyoyin biyu za su gamsu da wannan maki, la’akari da wasannin da suka buga a tsakiyar mako a UEFA Europa League, kuma wannan wasa ka iya zama kamar atisaye, kafin wasan wasan zakarun Turai da kowacce za ta yi nan faba.

  4. , Daga Jaridu

    Morata

    Asalin hoton, Getty Images

    Kungiyar Bayern Munich na nuna sha'awar dan wasan gaba na Newcastle United kuma dan England, Anthony Gordon mai shekaru 25, wanda kuma Arsenal ke bibiyarsa. (Caughtoffside)

    Manchester United na fatan amfani da zumuncin da wasu yan wasanta na Ingila ke da shi da dan wasan Nottingham Forest, Elliot Anderson, don su ja ra'ayinsa ya koma kungiyar maimakon Manchester City. (Teamtalk)

    Liverpool na duba yiwuwar daukar dan wasan gefe na Brighton & Hove Albion kuma dan Gambia, Yankuba Minteh mai shekaru 21, wanda ya taba aiki karkashin Arne Slot a Feyenoord domin maye gurbin dan wasan gaba na Egypt, Mohamed Salah mai shekaru 33. (Mirror)

    Arsenal da Manchester City sun shiga takarar neman dan wasan baya na Real Betis, Oscar Mingueza mai shekaru 26, tare da Aston Villa. (Teamtalk)

  5. Robertson zai ci gaba da sa wazo har karshen kakar nan, Liverpool

    Andy Robertson

    Asalin hoton, Getty Images

    Andy Robertson ya yi alkawarin zai ci gaba da sa Ƙwazo har zuwa ƙarshen kakar nan, amma yana ganin wannan bazarar ce lokacin da ya dace ya bar Liverpool.

    Ɗan wasan tawagar Scotland ya bayyana hakan a wannan makon cewa wannan kakar ce ta ƙarshe da zai yi a Anfield bayan shekaru tara, inda ya lashe duk manyan kofunan ƙungiyar ciki har da kofunan Premier League guda biyu da kuma Champions League.

    Ya fara bankwana ne ta hanyar buga cikakken mintuna 90 yayin da Liverpool ta doke Fulham da ci 2-0 a ranar Asabar.

    Dan wasan mai shekaru 32 ya ce:

    “Duk abinda ya yi farko yana karshe. Na shafe shekaru tara a nan kuma ban taɓa tunanin zaɓin haka ba, duba duk kofunan da na lashe.

    “Ina matuƙar alfahari da kasancewa a Liverpool a irin wannan tsawon shekaru tara, amma yanzu lokaci ya yi da ni da iyalina za mu ba Liverpool damar ci gaba da kaiwa kololuwa, ni kuma zan dunga tuna baya da tuna abubuwan ban mamaki da na samu.

    “Tabbas sanarwar ta fito ne a wannan makon. Wannan ya sa ba sai na ci gaba da yi wa kowa ƙarya ba, don haka na ji kamar an sauke mini wani nauyi daga kafaɗa ta.

    “Wannan ne babban dalilin yin hakan, amma yanzu ina mai da hankali sosai kan ƙoƙarin kammala kakar wasa cikin ganiya sosai, domin haka ne wannan ƙungiyar ta cancanta daga gare ni.”

  6. Union Berlin ta naɗa Marie-Louise Eta macen farko da za ta horar a Bundesliga, Bundesliga

    Marie Eta

    Asalin hoton, Getty Images

    ƘKungiyar Union Berlin ta sanar da nada Marie-Louise Eta a matsayin kociyar riƙon ƙwarya har zuwa karshen kakar bana, bayan da ta sallami tsohon kocinta, Steffen Baumgart.

    Eta mai shekaru 34 za ta kafa tarihi a matsayin mace ta farko da za ta jagoranci ƙungiya a babbar gasar tamaula ta Jamus wato Bundesliga. Wannan mataki ya jawo hankalin masu bibiyar ƙwallon kafa, musamman ganin yadda ake kokarin kara bai wa mata dama a manyan mukamai.

    Ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki ne bayan da ta sha kashi da ci 3-1 a hannun FC Heidenheim a karshen mako, sakamakon da ya bar Union Berlin a matsayi na 11 a teburin gasar.

    Kafin wannan sabon mukami, Eta tana horar da ƙungiyar matasa ƴan kasa da shekara 19 ta Union Berlin, inda ta nuna kwarewa da jajircewa. Haka kuma, an riga an shirya cewa za ta karbi ragamar ƙungiyar mata daga kakar wasa mai zuwa.

    A shekarar 2023, Eta ta riga ta kafa wani tarihi bayan da ta zama mace ta farko da ta zama mataimakiyar koci a Bundesliga, wanda ke nuna irin ci gaban da take samu a harkar horar da ƙwallon kafa.

    Nada ta a wannan matsayi na riƙon ƙwarya yana nuna yadda ƙungiyar ke yarda da kwarewarta da kuma burinta na kawo canji a wannan mawuyacin lokaci da ƙungiyar ke ciki. Magoya baya na jiran ganin yadda za ta jagoranci ƙungiyar a sauran wasannin da suka rage a kakar bana.

  7. , Daga Jaridu

    Mohamed Salah

    Asalin hoton, Getty Images

    Aston Villa da Leeds United na sha'awar dan wasan baya na Union Berlin, Danilho Doekhi mai shekaru 27, wanda Besiktas ma ke bibiyarsa. (Inside Futbol)

    Tottenham Hotspur na kokarin daukar dan wasan tsakiya na RB Leipzig, Arthur Vermeeren mai shekaru 21, wanda ya taba taka leda karkashin Roberto De Zerbi yayin da yake aro a Marseille. (Caughtoffside)

    Har yanzu Real Madrid na iya daukar dan wasan baya na Borussia Dortmund, Nico Schlotterbeck mai shekaru 26, duk da cewa ya sabunta kwantiraginsa da kungiyar ta Bundesliga. (Goal.com)

  8. Arteta ba zai yadda da uzurin gajiya daga ƴan wasan Arsenal ba, Arsenal

    Mikel Arteta

    Asalin hoton, Getty Images

    Mikel Arteta ya bayyana cewa dole ne Arsenal ta guji amfani da gajiya a matsayin uzuri, bayan rashin nasarar da ta sha a hannun Bournemouth ranar Asabar a Premier League, inda ya bukaci su kara sa ƙwazo.

    Arsenal ta rasa wata babbar dama ta kara tazarar maki zuwa 12 a saman teburin a kan Pep Guardiola da Manchester City, bayan da aka doke ta 2-1 a Emirates.

    Wannan rashin nasara ya zama karo na uku a jere da Arsenal ta yi a gasar cikin gida, bayan ta sha kashi a wasan karshe a Carabao Cup da Manchester City ta lashe kofin, sannan kuma ta fita daga FA Cup a hannun Southampton, wadda ke matakin Championship.

    Arsenal za ta so ta koma kan ganiya a wasan zagaye na biyu a quarter-final a UEFA Champions League da za ta kara da Sporting Lisbon a London ranar Laraba. Arsenal ce ta ci 1-0 a makon jiya a Portugal.

    Wannan wasa zai kasance na 54 da Arsenal za ta buga a wannan kakar, wanda ya fi na Manchester City da uku tsakani.

    A wasan da suka yi da Bournemouth, wasu daga cikin ƴan wasan Arsenal sun nuna kamar sun gaji, musamman ganin cewa kyaftin Martin Odegaard da Bukayo Saka da kuma Jurrien Timber ba su buga ba fafatawar ba saboda jinya.

    Sai dai lokacin da aka tambayi Arteta ko yana ganin gajiya na cikin matsalar ƙungiyar, ya ce:

    “Ba na son amfani da irin wannan uzuri saboda mun saba buga wasanni da yawa, kusan kowanne kwana uku, kuma dole ne mu ci gaba da yin hakan.

    “Wannan shi ne yanayin da muke ciki, kuma dole ne mu rungume shi, ya kamata mu kara sa kokari a sauran wasannin da suka rage.

  9. Jama'a barkanmu da kasancewa a cikin shirin labarin wasanni da za mu ke sanar da ku wainar da ake toyawa daga wannan ranar zuwa Asabar 18 ga watan Afirilu.

    Sunana Mohammed Abdu za ku iya tafka muhawara a BBC Hausa Facebook ko kuma ku bibiyi labaran da muke wallafawa a BBC Hausa WhatsApp.