Mece ce Hantavirus? Cutar da ɓeraye ke yaɗawa wadda 'ba ta da magani'

    • Marubuci, Yang Tian
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 4

Mutum uku sun mutu sanadiyyar ɓarkewar wata cuta da ake zargin hantavirus ce, a cikin wani jirgin ruwa da ke tafiya kan tekun Atlantika, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta sanar.

Yanzu haka an tabbatar cewa mutum ɗaya ya kamu da ƙwayar cutar, yayin da ake ci gaba da bincike kan wasu mutum biyar, wadanda su ma ake zargin suna ɗauke da ƙwayar.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta shaida wa BBC cewa "ana ci gaba da gudanar da cikakken bincike game da lamarin", ciki har da gwaje-gwaje a ɗakunan bincike.

An bayar da rahoton ɓarkewar cutar ne a kan jirgin shaƙatawa na MV Hondius, wanda ke kan hanyarsa daga ƙasar Argentina zuwa Cape Verde.

Ga bayani kan abin da muka sani game da ƙwayar cutar hantavirus.

Mece ce ƙwayar cutar hantavirus?

Hantavirus wasu ƙwayoyin cutuka ne da ɓeraye da dangoginsu ke yaɗawa, inda ɗan'adam kan iya ɗaukar cutar ta hanyar shaƙarta a iska daga busasshen ɓurɓushin kashin ɓera.

Cutar na yaɗuwa ne a lokacin da ƙwayoyinta daga fitsari, kashi ko kuma yawun ɓera suka shiga cikin iska, kamar yadda Cibiyar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta Amurka (CDC) ta bayyana.

Sannan kuma cutar na iya yaɗuwa ta hanyar cizo ko yakushin ɓera, duk da ba a cika samun irin hakan ba.

Ƙwayar cutar za ta iya haifar da miyagun cutuka biyu masu tsananin haɗari.

Cuta ta farko da ƙwayoyin ke haddasawa ita ce wadda ke shafar huhu da kafofin iska, wato 'Hantavirus Pulmonary Syndrome' (HPS), inda da farko mutum zai fara da jin kasala da ciwon kai, sai a fara ganin jiri da jin ɗari da kuma ciwon ciki.

Da zarar mutum ya fara samun wahalar numfashi, to akwai yiwuwar rasa rai da kimanin kashi 38%, kamar yadda hukumar CDC ta Amurka ta bayyana.

Cuta ta biyu da ƙwayoyin ke haifarwa ita ce zazzaɓi da zubar jini, wato 'Haemorrhagic Fever with Renal syndrome' (HFRS).

Wannan ita ce cutar da ta fi haɗari kuma tana shafar ƙoda ne.

Alamominta da kan biyo baya su ne saukar yanayin jini, zubar jini a cikin jikin ɗan'adam da kuma mummunan lalacewar ƙoda.

Ya girman Hantavirus a faɗin duniya?

Akan samu kimanin mutum 150,000 da ke kamuwa da cutar zazzaɓi da zubar jini (HFRS) bayan cin karo da ƙwayar cutar a duk shekara, inda aka fi samun irin wannan a ƙasashen Turai da na Asia, in ji rahoton Kwalejin Nazarin Lafiya ta Birtaniya.

Ana samun rabin masu kamuwa da wannan nau'i na cutar ne a ƙasar China.

Alƙaluma na baya-baya a Amurka sun nuna cewa daga shekarar 1993, lokacin da aka fara sanya ido sosai kan cutar, zuwa shekara ta 2023, an samu mutum 890 waɗanda suka kamu da cutar a ƙasar.

Akwai kuma wani babban nau'in cutar da ake kira Seoul virus, wanda jajayen ɓeraye ke yaɗawa, ana samun wannan cutar a fadin duniya, har a Amurka.

Yadda ake magance cutar?

Babu wani takamaiman maganin cutar hantavirus.

Hukumar Yaƙi da Cutuka masu yaɗuwa ta Amurka na bayar da shawarar bai wa mutane magungunan da za su taimaka musu ne kawai, kamar iskar da za ta taimaka wajen numfashi da bayar da magungunan kashe ƙwayoyin cuta da kuma wankin ƙoda.

Idan ciwon ya yi tsananin ana buƙatar kwantar da mutum a sashen kula da marasa lafiya da ke cikin matsanancin hali a asibiti, haka nan idan abin ya ƙara tsanani wajibi ne a zura bututun shaƙar iska zuwa cikin huhu.

Hukumar CDC na bayar da shawarar guje wa hulɗa da ɓeraye a gidaje da wuraren aiki domin rage haɗarin yaɗuwar ƙwayoyin cutar.

An bayar da shawarar toshe duk wata kafa da ɓera zai samu ta shiga cikin muhalli da gine-gine.

Haka nan ana buƙatar masu aikin share wuraren da ke ƙunshe da kashin ɓera su sanya takunkumin kariya na fuska da kuma kayan kariyar jiki domin gudun shaƙa ko kuma taɓa fitsari ko kashin ɓera.

Ko an samu ɓarkewar cutar hantavirus a baya-bayan nan?

A watan Fabarairun 2025, wata mata mai suna Betsy Arakawa, mai ɗakin sanannen ɗan fim ɗin Amurka Gene Hackman ta rasu sanadiyyar cutar kafofin shaƙar iska, wadda ke da alaƙa da ƙwayar cutar hantavirus.

Masu bincike sun yi yaƙinin cewa Arakawa ta kamu ne da cutar kafofin shaƙar iska mai nasaba da hantavirus wadda ta yi ajalinta.

An gano wuraren ɓoyon ɓeraye a kusa da gidan da aka same ta a mace.

Yansanda sun gano cewa ta nemi bayani a shafin intanet kan alamun mura da cutar korona kafin mutuwar ta.