Arsenal da Liverpool na zawarcin Bouaddi,Manchester City na son Branthwaite

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Arsenal ta fara tattaunawar siyan dan wasan Lille, Ayyoub Bouaddi mai shekara 18, wanda ya taimakawa Morocco ta tashi 1-1 da Brazil a wasan farko na kasarsa a gasar cin kofin duniya ta 2026. (Times - subscription required), external

Ita ma Liverpool na tattaunawar daukar Bouaddi,yayin da Chelsea da Paris St-Germain na bibiyar dan wasan da ake ganin kudinsa zai kai fam miliyan 60. (Talksport), external

Yunkurin da Bayern Munich ta yi na neman dan wasan PSV Eindhoven da Morocco Ismael Saibari, mai shekara 25, zai iya gamuwa da cikas saboda salon kwallon da ya zura a ragar Brazil a gasar cin kofin duniya, zai iya kara kudin da za a biya shi. (Bild - in German), external

Dan wasan Brighton Jan Paul van Hecke, mai shekara 26, ya ce zai warware makomar kulob dinsa bayan gasar cin kofin duniya bayan da kungiyar ta yi watsi da tayi sau biyu da Tottenham ta yi kan dan wasan kasar Netherlands. (Sky Sports), external

Manchester City na sha'awar dan wasan Everton Jarrad Branthwaite, mai shekara 23, domin maye gurbin John Stones mai shekara 32 da ya bar kungiyar sai dai Everton na son a biya ta fam miliyan 70 kan dan wasan na Ingila . (Football Insider), external

Roma na shirin yi wa dan wasan Ingila Mason Greenwood mai shekara 24 tayin fam miliyan 35 ciki harda da batun sayar da shi wanda suke fatan zai shawo kan Marseille ta amince da yarjejeniyar.(Corriere dello Sport - in Italian), external

An tsara yi wa dan wasan Brazil Ederson gwajin lafiyars a ranar Lahadi yayin da dan wasan mai shekara 26 ya kammala shirye shiryen komawa Manchester United daga Atalanta . (Corriere dello Sport - in Italian), external

Manchester United ta kori kocinta Ruben Amorim a watan Janairu, kuma za ta iya samun gagarumar rarar kudi ta fan miliyan 15.9 bayan tafiyarsa, idan dan Portugal din ya karbi ragamar horar da AC Milan.(Mirror)