An gano "gawa a cikin akwati" ashe yar tsana ce mai kama da mutum

    • Marubuci, Lana Lam
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Sydney
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

'Yan sandan Australia da aka kira domin bincike kan wata gawa da aka samu a cikin wani akwati sun kammala da cewa "gawar" a zahiri yar tsana ce mai kama da mutum.

Mutane biyu ne suka gano akwatin a gefen hanya kusa da ƙaramar ƙauyen Oallen, mai nisan kusan kilomita 230 (mil 143) kudu-maso-yamma da Sydney.

Ƴan sanda sun sanar da fara binciken kisan kai, lamarin da ya ja hankali matuƙa a kan batun, amma sa'o'i kaɗan bayan nan suka janye wannan matsaya, suka ce gwaje-gwajen kwararru ya tabbatar da cewa abin da ke cikin akwatin ba mutum ba ne.

"Da farko an yi kuskuren ɗaukar abin da ke cikin akwatin a matsayin mutum, saboda suna da matuƙar kama da gangar jikin mutum," in ji Sufeto Linda Bradbury daga Yankin 'Yan Sandan Hume.

"Amma mun tabbatar ta wasu hanyoyi cewa ba haka ba ne."

"Yar tsanar tana sanye da kaya, tana da gashi kuma tana da huda a hanci," in ji 'yan sanda, suka ƙara da cewa " ƴar tsanar kuma tana da alamomi masu kama da raunuka da ƙuraje."

Sufeto Bradbury ta ce tawagar ƙwararrun masu binciken da masu gwaje-gwaje sun isa wurin a ranar Lahadi, kuma an bi dukkan hanyoyin da suka dace.

"Manufar ita ce, a yi iya bakin ƙoƙari don kada a sauya yadda wuraren da aka yi binciken, saboda a kiyaye ingancin bincikenmu," in ji Bradbury, ta ƙara da cewa ba ta da "nadama ko kaɗan" kan yadda aka gudanar da lamarin.

Sa'o'i kaɗan kafin sannan, Bradbury ta shaida wa kafafen yaɗa labarai cewa, abin da mutanen biyu da suka gano akwatin suka gani "ya firgita su sosai".

"Abin takaici, suna yawo ne a ƙarshen mako kamar yadda mutane da dawa ke yi, sai suka tsaya domin hutawa," in ji ta.

Ta ce mutanen biyu sun ɗauki "matakin da ya dace" na sanar da abin da suka gani.

"Lamarin ya dame su a jiya kuma za mu tuntube su domin mu sanar da su cewa ba ragowar jikin mutum ba ne," in ji Bradbury.

A yanzu 'yan sanda sun rufe bincikensu.