Mene ne amfanin matatun man China idan Iran ba ta fitar da mai?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Tsawon shekaru, ƙananan matatun mai na ƙasar Sin suna cikin manyan masu sayen ɗanyen man Iran, wanda ake sayar musu da shi kan farashi mai rahusa sakamakon takunkuman da Amurka ta ƙaƙaba. Wannan ya bai wa waɗannan matatun mai masu zaman kansu damar sayen mai ƙasa da farashin kasuwa.

Sai dai yanzu, bayan watanni ana taƙaita fitar da man Iran zuwa ƙasashen waje sakamakon killacewar ruwa da rundunar sojin ruwan Amurka ta yi, waɗannan matatun sun tilasta wa kansu sauya hanyoyin samun ɗanyen mai.

Waɗannan matatun, da ake kira "teapot refineries", waɗanda galibinsu suke a lardin Shandong da ke gabashin ƙasar Sin, sun taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Iran ci gaba da fitar da mai a shekarun da aka ƙaƙaba mata takunkumi. Ba kamar manyan kamfanonin gwamnatin Sin ba, da yawa daga cikin waɗannan matatun sun kasance a shirye su sayi man Iran mai rahusa duk da takunkuman Amurka.

Yanzu da aka taƙaita musu samun man Iran, wasu ƙasashe masu arziƙin mai sun fara cike gibin. Erica Downs, babbar masaniya a Cibiyar Nazarin Manufofin Makamashi ta Duniya (Center on Global Energy Policy) ta Jami'ar Columbia, ta shaida wa BBC Persian cewa man Iraƙi ya zama wani zaɓi mai jan hankali. Man Iraƙi yana da kusan irin ingancin man Iran, amma farashinsa ya fi na man Iran da ake sayarwa da rangwame.

Ga Iran kuwa, muhimmiyar tambayar ita ce ko waɗannan kwastomomin da suka koma sayen mai daga wasu masu samarwa za su koma sayen man Iran idan aka ɗage killacewar da ake yi wa fitar da man nata a nan gaba.

Ma'ajiyar ɗanyen man Iran da ke yankunan teku

Tasirin takunkumin ruwa da Amurka ta yi wa fitar da man Iran zuwa ƙasar Sin bai bayyana nan take ba, sai bayan wasu watanni. Kafin a fara takaita sabbin jigilar kayayyaki, Iran ta riga ta adana ɗimbin man fetur a cikin tankokin ruwa da ke tafiya a tekunan duniya, musamman kusa da ƙasashen Malaysia da Singapore. Hakan ya bai wa matatun mai na Sin damar ci gaba da amfani da hajojin man da tuni suka bar Iran.

Kamfanin nazarin harkokin makamashi na Kepler ya kiyasta cewa zuwa tsakiyar watan Yuli, kimanin gangar mai miliyan 89 na ɗanyen mai da condensate na Iran suna cikin tankokin ruwa da ke wajen yankin killacewar da Amurka ta kafa. Har zuwa watan Satumba ma, kimanin ganga 590,000 na man Iran suna isa Sin a kowace rana, duk da cewa kamfanin bai samu bayanan wata sabuwar jigilar ɗanyen man Iran ba a wannan watan.

A cikin wani rahoto da ya fitar ranar 22 ga Oktoba, Kepler ya bayyana cewa an gano lodin ɗanyen man Iran da iskar condensate na ƙarshe ne a ranar 25 ga Agusta, kuma man da aka adana a cikin tankokin ruwa da ke wajen yankin killacewar ya ƙare zuwa tsakiyar watan Oktoba.

Da samun waɗannan kayayyakin ya ragu, matatun mai masu zaman kansu na Sin sun ƙara sayen mai daga wasu ƙasashe masu samar da mai, tare da kulla sabbin yarjejeniyoyi da masu sayar da mai daga Iraki da sauran ƙasashe masu fitar da mai.

Yaya girman asarar da matatun mai na Sin suka tafka?

Sayen madadin ɗanyen mai ya zo da tsada mai yawa. Rangwamen farashin da matatun mai na Sin suke samu a baya wajen sayen man Iran yanzu ya maye gurbinsa da biyan ƙarin kuɗi domin sayen wasu hajojin mai daga Iraki, Rasha da kuma ƙasashen Afirka.

Wata majiya daga masana'antar tace mai ta shaida wa Reuters cewa matsakaicin asarar da matatun mai masu zaman kansu suka yi a watan Nuwamba ya kai tsakanin yuan 150 zuwa 200 kan kowace tan na man da aka tace, wanda ya yi daidai da kusan dala 3 zuwa 4 kan kowace ganga.

Matsalar da waɗannan matatun ke fuskanta ba ta taƙaita ga hauhawar farashin sayen ɗanyen mai ba kawai. A cikin ƙasar Sin, gwamnati ce ke tsara farashin man fetur da dizal a kasuwar cikin gida, sannan yawancin waɗannan matatun masu zaman kansu ba sa samun damar fitar da man fetur da dizal zuwa ƙasashen waje cikin sauƙi.

Saboda haka, kuɗin da suke kashewa wajen sayen ɗanyen mai ya ƙaru, amma saboda ƙuntatawar farashin mai da gwamnatin Sin ta gindaya, ba za su iya sayar da kayayyakinsu a farashin da zai daidaita da ƙarin kuɗin da suka kashe ba.

Bayanan da kamfanin GL Consulting ya tattara sun nuna cewa matatun mai masu zaman kansu a lardin Shandong suna aiki ne da kashi 54.7 cikin 100 na ƙarfin samarwarsu a makon da ya ƙare ranar 12 ga Nuwamba. Wannan ya fi ƙasa da kashi 50 cikin 100 da aka gani a rubu'i na biyu na shekara, amma har yanzu yana ƙasa sosai idan aka kwatanta da matakin kashi 65 zuwa 75 cikin 100 da aka samu a shekarun 2020 da 2021.

Shin za su koma sayen man Iran?

Erica Downs na ganin cewa komawar matatun mai masu zaman kansu na ƙasar Sin zuwa sayen man Iran zai dogara ne da farashi fiye da komai.

Ta shaida wa BBC Persian cewa:

"Idan aka dawo da fitar da man Iran kuma farashinsa ya kasance mai sauƙi, matatun mai masu zaman kansu za su koma sayen man Iran."

Sai dai Downs ta yi wani muhimmin bambanci tsakanin yanayi biyu: ɗage killacewar jiragen ruwa da Amurka ta yi da kuma ɗage takunkuman da aka sanya wa man Iran.

A cewarta, idan aka ɗage takunkumin kuma aka sake bai wa man Iran damar fita cikin 'yanci ta mashigar ruwan Hormuz, akwai yiwuwar Sin ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan masu sayen man Iran. Amma irin kamfanonin da za su sayi man a Sin zai dogara ne da makomar takunkuman.

Ƙwararriyar ta ce idan Amurka ta ɗage takunkuman da ta sanya wa Iran, manyan kamfanonin man fetur mallakin gwamnatin Sin za su iya komawa sayen man Iran, sannan masu saye daga wasu ƙasashe ma za su iya sake shiga kasuwa.

Downs na hasashen cewa a irin wannan yanayi, ƙaruwa a gasa tsakanin masu saye da kuma ƙarewar rangwamen da Iran ke bayarwa saboda takunkumi zai sa matatun mai masu zaman kansu na Sin su sayi ƙarancin man Iran idan aka kwatanta da abin da suka saya a baya.

A zahiri, man da ya kasance mai jan hankali ga ƙananan matatun mai na Sin a lokacin takunkumi saboda rahusar farashinsa na iya samun sababbin kwastomomi idan aka ɗage takunkuman. Manyan kamfanonin gwamnatin Sin, waɗanda suka guji sayen man Iran tsawon shekaru saboda takunkumin, za su iya komawa kasuwa, yayin da ƙananan matatun za su kasance cikin gasa da manyan kamfanoni masu ƙarfi wajen neman sayen irin wannan man.

Wane tasiri raguwar fitar da man fetur zuwa ƙasashen waje ta yi wa Iran?

Ƙasar Sin ce ta kasance babbar kasuwar da mafi yawan man fetur da Iran ke fitarwa zuwa ƙasashen waje ke zuwa a cikin ƴan shekarun nan. Ma'aikatar Kuɗi ta Amurka ta ƙiyasta a watan Afrilu na shekarar 2026 cewa kusan kashi 90 cikin 100 na man da Iran ke fitarwa yana zuwa ƙasar Sin. Taƙaituwar damar shiga wannan kasuwa, tare da hasarorin da yaƙi da matsalolin sufuri suka haifar, sun jefa harkokin samar da mai da kuma kudaden shiga na Iran cikin matsin lamba mai tsanani.

A cikin rahotonta na ranar 13 ga Nuwamba, Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta ƙiyasta cewa Iran ta samar da kusan ganga miliyan 1.86 na ɗanyen mai a kowace rana a watan Oktoba. Wannan adadi ya yi ƙasa ƙwarai idan aka kwatanta da ƙarfin samar da man ƙasar na dindindin wanda ya kai ganga miliyan 3.8 a rana.

Tasirin raguwar fitar da mai zuwa Sin bai tsaya ga asarar kuɗaɗen shiga daga sayar da mai kaɗai ba. A cikin 'yan shekarun nan, wani ɓangare na kasuwancin Iran da Sin ana gudanar da shi ne ta hanyoyin da ake mayar da kuɗin da aka samu daga sayar da mai zuwa bashi ko lamuni domin sayen kayayyaki da aiwatar da ayyukan raya ƙasa.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito a wani bincike da ya wallafa a watan Satumba cewa Iran na amfani da wata hanya mai kama da musayar kaya da kaya, inda majiyoyinsa suka ƙiyasta cewa kuɗaɗen da ake canjawa ta hanyar ɗaya daga cikin rassanta suna tsakanin dala biliyan 2 zuwa biliyan 2.5 a shekara.

Babban mai nazari na kamfanin Kepler, Homayoun Falakshahi, ya yi hasashe a watan Oktoba cewa kuɗaɗen shiga na Iran daga sayar da ɗanyen mai da condensate za su iya sauka zuwa sifili nan da tsakiyar watan Disamba idan killacewar ta ci gaba. Ya bayyana cewa hakan zai faru ne saboda jinkirin da aka saba samu na wata ɗaya zuwa biyu tsakanin lokacin isar da mai da lokacin karɓar kuɗin sa.

A gefe guda kuma, matatun mai masu zaman kansu na ƙasar Sin, waɗanda suka kasance daga cikin manyan masu sayen man Iran tsawon shekaru, sun riga sun rattaba hannu kan kwangilolin sayen madadin mai har zuwa watan Janairu. Wannan na nuna cewa waɗannan matatun sun daidaita shirye-shiryensu na samar da ɗanyen mai bisa ga kayayyakin da suke samu daga sauran ƙasashe masu samar da mai, aƙalla na watanni masu zuwa.