Wane ne Murtala Garo, matashin da zai zama mataimakin gwamnan Kano?

Asalin hoton, Garo Facebook
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika da sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin jihar domin neman tantancewa a matsayin mataimakinsa.
Hakan na zuwa ne bayan murabus ɗin da Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya yi a ranar 27 ga watan Maris ɗin 2026.
Wannan dai ya samo asali ne sakamakon sauye-sauyen sheƙa da aka samu tsakanin gwamnan da mataimakinsa da wasu 'yan majalisar jihar da sauran masu ruwa da tsaki cikin gwamnatin.
Gwamna Abba Kabir da aka sani tare da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, ya ci zaɓe ƙarƙashin jam'iyyarsu ta NNPP, ya koma jam'iyyar APC mai mulki, yayin da mataimakinsa Kwamred Aminu Abdussalam Gwarzo ya ƙi bin sa jam'iyyar ta APC ya koma ADC tare da Kwankwaso.
Wannan ya janyo wani sauyi mai yawa a siyasar Kano, inda mutanen da aka sani da tsohon Gwamnan Kano kuma shugaban Jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje suka koma wajen Kwankwaso ciki har da tsohon ɗan takarar gwamna a APC na 2023 Nasiru Gawuna.
Murtala SUle Gari na daga cikin mutane uku da aka yi ta tsammanin gwamnan zai ɗauki mataimakin nasa a cikinsu.
Yanzu dai burin Garo na zama mataimakin gwamna na dogon lokaci ya cika, sai dai ba a tsarin da ya hau layi ba a baya ta wani tsarin na daban.
Wane ne Garo ?

Asalin hoton, Garo/Facebook
Sunansa Murtala kuma ɗa ne ga Alhaji SUle Garo wani attajiri da aka yi a jihar Kano. Garo kuwa sunan garinsu ne wanda ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Kabo da ke Arewacin jihar Kano.
Murtala Sule Garo na ɗaya daga cikin fitattun 'yan siyasar Kano masu ƙarancin shekaru da ke da tasiri da kuma mabiya waɗanda mafi yawansu matasa ne.
Ya riƙe matsayin kwamishinan ƙananan hukumomi a jihar Kano ƙarƙashin shugabancin tsohon gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje har na tsawon shekaru.
Gabanin nan, ya taɓa zama mai bai wa gwamna shawara na musamman. An kuma taɓa zaɓarsa a matsayin shugaban ƙaramar hukumar Kabo wadda ita ce ƙaramar hukumar da ya fito.
Matashin mai shekaru 48 ya kuma riƙe shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi a jihar Kano mai yawan ƙananan hukumomi 44.
Garo ɗan shekara 48, ya shafe kusan shekara 20 cikin harkokin siyasa, inda ya riƙe muƙamai daga waɗanda aka zaɓe shi zuwa waɗanda aka naɗa shi na tsawon waɗannan lokuta.
Garo mutum mai cike da taƙaddama

Asalin hoton, Garo/Facebook
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Shi dai Garo ya yi fuce cikin taƙaddamar siyasa musamman sunansa ya yi amo a lokacin da aka samu matsalar kammala zaɓen 2019, lokacin da Abdullahi Ganduje ya koma gwamna a karo na biyu.
A lokacin ne aka ga bidiyonsa tare da Nasiru Gawuna wanda suka yi takara a 2023, a hannun 'yan sanda inda aka zarge su da kawo tsaiko a harkokin zaɓe.
Garo ya taka rawa lokacin da Kwankwaso ya dawo kan mulki a matsayin gwamnan Kano a 2011, shi ne kuma ya yi masa jami'i mai tattara sakamakon zaɓe a lokacin.
Sule Garo wanda siriki ne ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, inda yake auren ƴarsa ya janyo ce-ce-ku-ce kan neman matsayin mataimakin Gwamnan da yanzu aka aika sunansa domin tantancewa.
Ka zalika Garo siriki ne ga Sanata Rabi'u Kwankwaso, inda Kwankwason ke auren 'yar uwarsa.
Murtala Garo na cikin 'yan siyasar da ake shakka a Kano, ko dai don yawan mabiya ko kuma don rashin haƙurin da yake da shi na idan an taɓa shi ba ya bari.
A baya sa-in-sa ta taɓa haɗa shi da Alasan Ado Doguwa, wanda daga baya aka shiga tsakani, kuma suka fito cikin jama'a suka nemi afuwar juna tare da yafar juna.
Murtala Sule Gari ya kasance na gaba-gaba a gidan siyasar tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje wani abu da ake ganin shi ne babban dalilin da ya sa gwamna Abba ya zaɓe shi tun bayan komawar Abban jam'iyyar APC.











