Tarihin jami'o'i na farko da aka fara kafawa a Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Ziyarar da tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy, ya kai Senegal a watan Yulin 2007, ta haifar da zazzafan ce-ce-ku-ce bayan wani jawabi da ya gabatar kan Afirka mai cike da takaddama a jami'ar Cheikh Anta Diop da ke Dakara kasar Senegal.
Ya ce: "Abin takaicin da ke faruwa a Afirka shi ne cewa ɗan Afirka bai shiga tarihi sosai ba." Baƙar fata na Afirka… maimaitawar lokaci kawai ya sani".
Tun daga wannan lokaci, 'yan Afirka da dama suka fara mayar da martani ga Sarkozy, wanda ya nuna rashin sanin ya kamata, ta hanyar musanta irin gagarumar gudunmawar da Afirka ke bayarwa ga ci gaban bil'adama.
Wadannan masana sun yi nuni da cewa, nahiyar Afirka ta mallaki manyan cibiyoyin ilimi a zamanin da, kuma ta kasance gida ga jami'o'i, tun kafin kafa jami'o'in Turai na farko, irinsu Bologna wadda ta kasance jami'ar yamma da ta fi tsufa - an kafa ta a shekarar 1088, sai Oxford (1096), Sorbonne (1257) ko kuma Harvard (1636).
A wannan maƙala, BBC ta yi waiwaye da kuma duba kan cibiyoyin ilimi shida mafi girma a tarihin Afirka - waɗanda tasirinsu ya zarce fiye da nahiyar.
1 - Cibiyar ilimi ta Alexandria (Masar)

Asalin hoton, Getty Images Nastasic
A cikin Masar, ƙasa mai dala, muka samu ɗaya daga cikin mahimman cibiyoyin ilimi tun zamanin da: Ɗakin karatu na Alexandria.
Alexandria ita ce birni na biyu mafi girma a Masar, tana kusa da tekun Mediterranean.
Birnin ya samo sunan shi daga Alexander wanda ya kafa shi a shekarar 331.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Birnin ya yi suna a zamanin baya saboda kasancewarsa cibiyar ilimi.
Mun gano cewa "Ptolemy I Soter ne ya kafa cibiyar, wanda shi ne ya kafa daular Lagid na Girka kuma sarkin Masar (305-283 BC), kafin magadansa su bunkasa cibiyar.
Cibiyar ta zama ɗaya daga cikin cibiyoyin ilimi mafi girma a duniya, inda take ɗauke da takardu sama da 200,000, ko ma fiye da haka.
Wannan ɗakin karatu yana "malalai da ɗalibai kusan 5000," a cewar Paul Tiyambe Zeleza.
"Wannan babban wurin karatu ne kuma malamai da dama, kama daga Afirka da Girka da Romawa da kuma Yahudawa sun yi karatu ko kuma aiki a cibiyar a wani lokaci a rayuwarsu," in ji shi.
Manyan mutane a duniya sun gina gidaje a wannan birni mai ɗimbin tarihi.
A wurin ne ɗaruruwan masana suka yi fassarar farko ta Tsohon littafin Alkawari daga Hebrew zuwa Girka.
Ɗakin karatu na Alexandria ya dusashe bayan ɓarnatar da shi lokacin yaƙe-yaƙe, abin da ya tilastawa masana barin wurin saboda rashin daidaiton siyasa da ya faru lokacin karshen mulkin Romawa.
Cibiyar ta yi shura har zuwa ƙarni na 7, lokacin da ya faɗa hannun Farisawa zuwa kuma Larabawa.
Cibiyar ta taɓa fannoni da dama kama da daga darussan lissafi da kimiyya da falsafa da kuma addini.
2 - Jami'ar Ez-Zitouna a Tunis (Tunisiya)

Asalin hoton, Getty Images CJ_Romas
Jami'ar Ez-Zitouna na ɗaya daga cikin daɗaɗɗun cibiyoyin ilimi a ƙasashen Musulmi.
An kirkiro da jami'ar tun shekarun 737 - Ubayd ibn al-Habhad ne ya kafa jami'ar.
Ta fara ne a matsayin karamin masallaci, inda ta faɗaɗa zuwa babbar cibiyar ilimi.
Da farko jami'ar ta mayar da hankali wajen koyar da ɓangaren fikihu, harshen Larabci da kuma Qur'ani - daga baya ta faɗaɗa hakan zuwa falsafa, tarihi, ilimin zamantakewa da kuma shari'a.
Dubban malamai ne suka yi karatu tare da kammalawa a jami'ar ta Ez-Zitouna,
An kuma kirkire ta ne tun kafin kafa jami''o'in kasashen yamma.
3 - Jami'ar Al-Qarawiyyin a Fez (Moroko)

Asalin hoton, Getty Images
Fatima al-Fihri ce ta kafa jami'ar al-Qarawiyyin da ke birnin Fez a shekara ta 859 - kuma tana ɗaya daga tsoffin jami'o'i a duniya da ke ci gaba da aiki.
Babbar cibiyar ta ilimi addinin Musulunci, kimiyya da kuma falsafa ta kasance Masallaci a can baya.
Jami'ar ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na cibiyar koyarwa lokacin yaɗuwar addinin Musulunci.
An koyar da ilmin lissafi, ilmin taurari, da fannonin da suka shafi shari'ar Musulunci a cikin jami'ar, wanda ɗalibansa suka haɗa da Ibn Khaldoun, masanin tarihi, falsafa da kuma zamantakewa da kuma ɗan siyasa, Muhammad al-Idrisi, masanin ƙasashen Larabawa.
4 - Jami'ar Al-Azhar a Alkahira (Masar)

Asalin hoton, Getty Images Juha Huiskonen
Jami'ar Al-Azhar babbar cibiya ce a duniyar Musulmi.
A lokacin da Musulmi 'yan Sunna suka fuskanci tambayoyin tauhidi, suna komawa ga Azhar domin neman shawara da jagoranci.
An kafa jami'ar a shekarar 970 miladiyya karkashin khalifancin Fatimid, domin koyar da ilimin fikihu da kuma karatun Qur'ani.
Jami'ar Al-Azhar na ɗaya daga cikin cibiyoyin ilimi da ake girmamawa a duniyar Musulmi, wadda ta yi suna a matsayin cibiyar bincike da koyarwa ta Musulunci.
Ta koyar da darussa kan fannin falsafa da sauran fannonin ilimi da dama.
5 - Masallacin Djinguereber da Jami'ar Sankoré ta Timbuktu (Mali)

Asalin hoton, Credit: Getty Images Guido Cozzi/Atlantide Phototravel
Abin da mutane da yawa ba su sani ba shi ne, an kafa ɗaya daga cikin tsofaffin jami'o'i a Afirka, a yankin Timbuktu na Mali a shekarar 989 miladiyya.
Jami'ar Sankore a Timbuktu na koyarwa kan darussa da dama waɗanda suka haɗa da ilmin taurari, likitanci, nahawu, tarihi da labarin kasa da sauransu.
Timbuktu ya kasance babbar cibiyar koyon addinin Musulunci a can baya.
Birnin na ɗauke da muhimman rubuce-rubuce da aka yi kan tarihin Afirka da kuma Larabci, waɗanda har yau akwai wasu daga ciki.
Hukumar kula da al'adu da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta ayyana wurin a matsayin cibiyar tarihi.
An ce birnin Timbuktu ya taɓa karbar bakuncin ɗalibai kimanin 25,000 daga ƙasashe daban-daban da suka zo karatu a shahararriyar jami'ar ta Sankoré.
Birnin yana kuma da ɗakunan karatu mafi girma da takardu kusan 100,000.
6 - Gidajen ibada na Kiristoci

Asalin hoton, Getty Images Smarthshots International
Ba ya ga ɗakin karatu na Alexandria, Masar ta kasance ɗaya daga cikin cibiyoyin addinin Kiristanci na farko a duniya, daga nan ne aka fara gina gidajen ibada a ƙarni na 3, a cewar Paul Tiyambe Zeleza.
"Dubban Kiristoci ne suka yi ta tururuwar zuwa gidajen ibadar, ba kawai don guje wa cin zarafi na Romawa ba, har ma don sadaukar da kansu ga rayuwa ta tunani."
Gidajen ibadar da dokoki da suka kafa su sun ba da fage mai mahimmanci don yin tunani, rubutu da kuma samun ilimi.
"Ra'ayoyin da kuma tsarin gidajen ibada sun bazu zuwa sauran sassan Afirka da sauran sassan duniya har zuwa Ingila da Georgia a Turai da Farisa da Indiya a Asiya, wanda ya haifar da jami'o'in da suka samu cigaba daga baya," in ji Zeleza.











