Wane ne sabon sarkin Gumel Lawan Ahmed?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Gwamnatin jihar Jigawa ta sanar da Lawan Ahmed Muhammad a matsayin sabon sarkin Gumel, kwana uku bayan rasuwar mahaifinsa.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar, wadda ta samu sa hannun sakatare gwamnatin Bala Ibrahim, ta ce "Bisa ga shawarar masarautar Gumel da kuma majalisar sarakuna ta jihar Jigawa, gwamnan jihar Umar Namadi ya amince da naɗin Dr Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Gumel na 17".

Gumel na daga cikin masarautu masu daɗaɗɗen tarihi a ƙasar Hausa.

A ranar Alhamis, 3 ga watan Satumba ne masarautar Gumel ta sanar da rasuwar sarki na 16 Ahmed Muhammed bayan shafe shekara 46 a kan karaga.

Marigayin ya shafe tsawon mako shida yana jinya a wani asibiti da ke birnin Alqahira na ƙasar Masar, kuma rasuwarsa ta kawo ƙarshen mulkin ɗaya daga cikin sarakuna mafi daɗewa kan karaga a arewacin Najeriya.

Wane ne sabon Sarki Lawan Ahmed?

Mai martaba Lawan Ahmed Muhammad masani ne kan fasahar sadarwa ta zamani, inda yake da digirin-digirgir a fannin kwamfuta da tsarin sadarwa na zamani daga jami'ar Putra a ƙasar Malaysia.

Ya kuma yi karatun digiri na biyu kan ilimin kwamfuta a Birtaniya bayan samun digirin farko a ɓangaren lissafi daga Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya.

Kafin naɗin nasa, ya kasance shi ne Ciroman Gumel kuma daraktan sashen tabbatar da tsaron intanet a Hukumar Bunƙasa Fasahar Sadarwar Zamani ta Najeriya (NITDA).

Ya kuma koyar a makarantu daban-daban a Najeriya da ƙasashen waje, ciki har da Jami'ar Hafr Al-Batin da ke ƙasar Saudiyya.