Yadda gwamnati ta ware biliyoyin naira domin gyaran masallatai da coci a kasafin 2026

Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin naira tiriliyan 58.47

Asalin hoton, Presidency

Bayanan hoto, A watan Disamba 2025 ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 da ya kai naira tiriliyan 58.47
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

Kasafin kuɗin Najeriya na shekarar 2026 na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce, bayan bayyanar wasu rahotannin da ke nuna cewa an ware maƙudan kuɗaɗe domin gyaran wuraren ibada da kuma gudanar da ayyuka a masarautu.

Lamarin ya haifar da zazzafar muhawara a tsakanin ƴan Najeriya, inda wasu ke tambayar dalilin ware irin waɗannan kuɗaɗe a lokacin da ƙasar ke fama da matsananciyar tsadar rayuwa, talauci da kuma ƙarancin muhimman ayyukan more rayuwa kamar lafiya, ilimi da hanyoyi.

Masu sukar matakin na cewa kamata ya yi gwamnati ta fi mayar da hankali kan ayyukan da za su inganta rayuwar al'umma, yayin da wasu kuma ke ganin gyaran wuraren ibada da na gargajiya na da muhimmanci wajen bunƙasa al'umma da kiyaye al'adunsu.

A watan Disamba 2025 ne Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a gaban majalisar dokokin ƙasar da ya kai naira tiriliyan 58.47.

A kasafin, Tinubu ya tsara kashe naira tiriliyan 15.25 domin gudanar ayyukan yau da kullum na gwamnati, sannan ya ware naira tiriliyan 26.08 domin gudanar da manyan ayyuka da more rayuwa a ƙasar.

Abubuwan da aka bankaɗo

Ƙungiyar sa ido kan ayyukan gwamnati ta Tracka, ta ce ta gano cewa an saka kimanin naira biliyan 22 a cikin kasafin kuɗin domin zamanantar da masarautu 106, da ware wasu kuɗaɗe domin gyaran masallatai da coci-coci a sassan ƙasar.

Bugu da ƙari, ƙungiyar ta Tracka, ta ce ta gano cewa gwamnatin ta ware maƙudan kuɗaɗe domin ginawa, gyarawa da samar da kayan aiki ga masallatai, majami'u da manyan masarautun gargajiya 11, inda jimillar kuɗin ayyukan suka kai kusan naira biliyan biyar.

Tracka ta kuma ce cikin sauran abubuwan da ta gano akwai ware naira miliyan 750 ga Cibiyar Bincike kan Dabarun Aikin Gona ta Najeriya, domin kammala da kuma gyaran wasu ƙarin fadoji huɗu a jihar Kogi.

Haka kuma, an ware naira miliyan 560 ga Cibiyar Nazarin Al'adu, domin kammala wasu ayyuka da suka shafi sarakunan gargajiya a jihar Neja.

Binciken ya nuna cewa an ware wasu naira biliyan 200 da miliyan 611 ga Kwalejin Haɗin Gwiwa da ke Ibadan, domin gyaran ɗakunan taron al'umma da kuma fadojin sarakunan gargajiya a jihar Legas, ƙarƙashin Ma'aikatar Aikin Gona ta Tarayya.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta sha musanta irin waɗannan zarge-zarge da ƙungiyoyin sa ido kan kasafin kuɗi ke yi, tana mai cewa ana gudanar da kasafin kuɗi bisa tanade-tanaden doka da kuma buƙatun al'umma.

'Ba aikin gwamnati ba ne gina wuraren ibada'

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Masu sharhi na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan batun na ware kuɗaɗe domin gyaran wuraren ibada da masarautu a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.

Darakta a ƙungiyar CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya bayyana damuwa kan yadda ake shigar da wasu tanade-tanaden kuɗi cikin kasafin kuɗi ba tare da cikakken sa ido ba.

Ya zargi ƴan majalisa da gaza yin cikakken bincike kan kasafin kuɗi, inda ya ce hakan ne ke ba da damar cusa abubuwan da ba su da alaƙa da ainihin ayyukan gwamnati.

"Kasafin kuɗi yanzu kawai ana yin sa ne domin a cika wa wasu aljihu. Ba aikin gwamnati ba ne ta riƙa gina wuraren ibada," in ji Rafsanjani.

Ya ƙara da cewa ya kamata a karkata irin waɗannan kuɗaɗe zuwa ayyukan da za su inganta rayuwar jama'a da ci gaban ƙasa.

Ita ma Darakta a ƙungiyar Follow The Money, Hajiya Ummi Hamzat, ta ce sun rubuta wa gwamnati buƙatar samun cikakkun bayanai kan waɗannan tanade-tanaden kasafin kuɗi, kuma har yanzu suna jiran amsa.

"Ba wai muna adawa da a gina ko a gyara masallatai ba ne. Amma idan aka dubi halin da Najeriya ke ciki, za ka ga asibitoci ba su da kayan aiki, haka ma bangaren ilimi na fama da matsaloli."

"Don haka muna ganin ya kamata a fi mayar da hankali kan abubuwan da suka fi shafar rayuwar jama'a," in ji ta.

Ta ƙara da cewa ƙungiyarsu ba ta neman a dakatar da irin waɗannan ayyuka gaba ɗaya ba, sai dai tana ganin akwai wasu fannoni da suka fi dacewa a ba fifiko saboda amfanin al'umma.

Me ya kamata kasafin ya mayar da hankali a kai?

Wani masanin siyasa Henry Olonimoyo da BBC ta tattauna da shi a lokacin da shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin 2026 gaban majalisa, ya ce ya kamata gwamnatin tarayya ta yi bayani filla-filla kan yadda ta aiwatar da kasafin kudin da ya gabata, yayin da shugaban ƙasa ke shirin gabatar da kasafin shekara mai zuwa.

Olonimoyo ya ce akwai damuwa tsakanin al'umma kan cewa har yanzu ba a aiwatatar da wasu sassa na kasafin kudin shekarun 2023 da kuma 2024 ba, inda ya nanata buƙatar ganin ana fayyace duk wasu ayyukan gwamnati gabanin gabatar da sabon kasafin kudi.

"Zan so a ce gwamnati ta yi bayani sosai kan kasafin kudin da ya gabata, kasancewar akwai alamun cewa akwai ɓangarori da dama na kasafin 2023 da 2024 da har yanzu ba a aiwatar ba."

Ya ce bayanai sun nuna cewa duk da umarni da aka bayar na buƙatar bunƙasa yadda ake aiwatar da kasafin kuɗi, akwai ayyuka da dama wadanda ba a aiwatar ba, sai ga shi kuma yanzu an kawo kasafin 2026.

"Ina fatan cewa ko dai daga fadar shugaban ƙasa ko kuma daga ma'aikatar kasafin kudi za a samu wani jami'i da zai bayyana wa al'ummar ƙasa inda ake, domin gane yadda ake aiwatar da kasafin," in ji Olonimoyo.

Masanin siyasar ya kuma dora ayar tambaya kan ikirarin gwamnati game da kuɗaɗen shiga, kasancewar, a cewarsa abin da gwamnati ke fada ya saɓa da wanda ƴan kwangila ke bayyanawa.

"Tabbas shugaban ƙasa ya faɗa sau da dama cewa an samu ƙarin kudaden shiga a wannan shekara, cewa an cimma yawan harajin da aka yi hasashe.

"Amma daga abin da muke ji, ba a iya biyan ƴan kwangila ba, akwai matsaloli. Ko hakan na nufin cewa akwai matsalar kuɗaɗen shiga? Ya kamata shugaban ƙasa ya fito ya yi bayani kan wannan," in ji shi.

Yayin da ake shirin gabatar da kasafin kudin na shekarar 2026, Olonimoyo ya yi kira ga gwamnati ta mayar da hankali kan muhimman ɓangarori da suka shafi rayuwar ƴan Najeriya na yau da kullum.

"Ya kamata gwamnati ta mayar da hankali kan abubuwa masu muhimmanci kamar noma da tsaro da kuma samar da kayan ci gaba, idan aka yi la'akari da ƙalubalen da muke fuskanta."