Kotu ta yi watsi da ƙarar buƙatar gyaran zaɓen fidda gwanin APC a Magama/Rijau ta jihar Neja
Babbar Kotun Tarayya da ke Minna ta yi watsi da wata buƙata da aka gabatar domin sauya sunayen ɓangarorin da ke cikin ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwani na jam’iyyar APC a mazaɓar Magama/Rijau ta jihar Neja.
Ƙarar dai ɗan takarar APC, Shehu Auna, ya shigar ta hannun lauyansa, Abubakar Danjuma, yana ƙalubalantar sahihancin zaɓen fidda gwani da aka gudanar a ranar 16 ga Yunin 2026, wanda ya tsayar da Yakubu Auna a matsayin ɗan takarar jam’iyyar.
A hukuncin da ya yanke, Mai Shari’a Abdullahi Aminu Dan-Ige ya ce masu ƙarar sun kasa gabatar da gamsassun hujjoji da za su sa a amince da buƙatarsu saboda haka kotun ta yi watsi da ita.
Sai dai lauyan mai ƙarar ya ce hukuncin bai shafi ainihin ƙarar da ke ƙalubalantar zaɓen fidda gwanin ba.
Kotun ta ɗage ci gaba da sauraron shari’ar zuwa ranar 22 ga Yulin 2026.
























