Me ya bambanta ƴansandan jihohi da 'askarawan' da gwamnoni suka samar?

Asalin hoton, Zamfara state govt
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Ana ci gaba da tattaunawa a Najeriya kan shirin kafa rundunar ƴansandan jihohi, bayan Majalisar Dokokin tarayyar kasar ta amince da ƙudurin dokar.
Majalisar ta amince da ƙudurin ne bayan karatu na biyu, inda aka zaɓi amfani da ƙudurin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar a maimakon wanda ƴan majalisa suka gabatar tun da farko.
Buƙatar kafa ƴansandan jihohi dai ta daɗe tana cikin abubuwan da gwamnonin ƙasar ke nema. Sun yi ta jaddada cewa rashin ikon kafa rundunar ƴansanda ta jiha na hana su ɗaukar matakan da suka dace wajen magance matsalolin tsaro da ke addabar yankunansu.
Tun kafin wannan yunƙuri, jihohi da dama sun riga sun kafa rundunonin tsaro na cikin gida, kamar ƴan sa-kai, ƴan banga da kuma askarawa, domin taimakawa jami'an tsaro wajen kare rayuka da dukiyoyi.
Sai dai akwai masu nuna damuwa cewa idan aka kafa ƴansandan jihohi, za su iya kasancewa tamkar waɗannan rundunonin da ake da su yanzu, waɗanda ake yawan zargin su da rashin ƙwarewa da kuma cin zarafin jama'a a wasu lokuta.
"Duk inda aka kafa irin waɗannan rundunonin, bincike ya nuna cewa sai da aka samu ɓarna" in ji Group Captain Sadiq Garba mai ritaya, tsohon jami'in tsaro Najeriya.
To amma idan aka kafa ƴansandan jihohi, me zai bambanta su da waɗannan rundunonin tsaro da jihohi suka kafa? Kuma ta yaya za a tabbatar da cewa ba za su maimaita irin matsalolin da ake zargin wasu daga cikin rundunonin askarawa da aikatawa ba?
Wane aiki ƴan sa-kai da askarawa ke yi?
A baya-bayan nan, jihohi da dama sun kafa rundunonin tsaro na cikin gida domin taimakawa jami'an tsaro wajen yaƙi da matsalolin tsaro da suka addabi yankunansu.
Misali, jihohin Kudu maso Yammacin Najeriya sun kafa rundunar tsaro ta Amotekun, wadda ke aiki a jihohi shida na yankin. Haka ma a Arewacin ƙasar, jihohi da dama kamar Zamfara, Katsina da Sokoto sun ƙirƙiri nasu rundunonin tsaro domin taimakawa wajen yaƙi da rashin tsaro.
A Arewa maso Gabas kuma, jihohi irin su Borno da Yobe sun daɗe suna amfani da dakarun sa-kai na Civilian JTF, waɗanda ke taimaka wa sojoji da sauran jami'an tsaro a yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya.
Ƴan banga galibi aikinsu shi ne sintiri a unguwanni, daƙile aikata laifuka, da kuma taimakawa wajen tabbatar da bin doka da oda a matakin al'umma.

Asalin hoton, Zamfara state govt
A Zamfara, rundunar askarawa na gudanar da ayyukanta ne musamman a dazuka da yankunan karkara domin taimakawa wajen yaƙi da ƴan bindiga.
A Kano kuwa, an kafa rundunar ne domin taimakawa wajen yaƙi da barayin waya da masu daba, yayin da jihohin Sokoto da Katsina su ma suka ƙaddamar da irin waɗannan rundunoni domin tunkarar matsalolin tsaron da suka fi addabar yankunansu.
Haka kuma a Kudu maso Yammacin Najeriya, rundunar Amotekun na aiki a jihohin Ekiti, Lagos, Ogun, Ondo, Osun da Oyo, inda aka kafa ta domin taimakawa wajen kare rayuka da dukiyoyi da kuma yaƙi da miyagun laifuka.
Sai dai a lokuta da dama ana zargins u da rashin samun isasshen horo da ƙwarewa, lamarin da ya sa ake yawan korafi kan cin zarafin jama'a, kama mutane ba bisa ƙa'ida ba, da kuma amfani da makamai na gargajiya ko ƙirar gida ta hanyar da ta wuce ƙima ko ɗaukar hukunci da kansu ba tare da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban shari’a ba.
Wane aiki ƴansandan jihohi za su riƙa yi?
Ƙudirin dokar da Majalisar Dattawa ta amince da shi ya tanadi cewa idan ya zama doka, Najeriya za ta kasance da rundunonin ƴansanda biyu: Rundunar Ƴansandan Tarayya da kuma Rundunar Ƴansandan Jiha.
Sai dai kafin wata jiha ta kafa rundunarta, dole ne majalisar dokokin jihar ta zartar da dokar kafa ta bisa ƙa'idojin da Majalisar Tarayya ta shimfiɗa.
Ayyukan rundunar ƴansandan jiha za su haɗa da tabbatar da doka da oda, kare rayuka da dukiyoyi, hana aukuwar laifuka da bincike kan laifuka da aka aikata, da kuma tabbatar da zaman lafiya a cikin jihar.
Sai dai ƙudirin ya tanadi cewa Rundunar Ƴansandan Tarayya za ta iya shiga cikin harkokin tsaro na jiha idan matsalar ta fi ƙarfin rundunar jihar, ko kuma idan gwamnan jihar ya nemi taimakon gwamnatin tarayya.
Haka kuma, rundunar tarayya za ta iya shiga aikin ta jiha idan ƴansandan suka kasa gudanar da aikinsu saboda ƙarancin kuɗi, matsalolin gudanarwa ko wasu dalilai.
Tasirin gwamnoni kan ƴansandan jihohi

Asalin hoton, Getty Images
Ƙudirin dokar ya bai wa gwamnoni ikon naɗa kwamishinan ƴansandan jiharsu daga cikin jami'an da ke aiki a jihar, tare da ba shi umarni kan harkokin tsaro.
Sai dai ƙudirin ya shimfiɗa wasu matakan kariya domin hana amfani da rundunar ta hanyar da ba ta dace ba.
- Ba dole ne kwamishinan ƴan sandan jiha ya bi duk wani umarni da ya saɓa wa doka daga gwamna ba. Maimakon haka, zai iya kai rahoton lamarin ga hukumar kula da ƴansanda ta ƙasa.
- An haramta amfani da ƴan sandan wajen biyan wasu buƙatun siyasa, ko ƙabilanci da addini ko yanki ko wata buƙata ta ƙashin kai.
- Majalisar Tarayya za ta ci gaba da tsara ƙa'idojin ɗaukar aiki, horaswa, tantancewa, ƙarin girma da kuma hukunta jami'an ƴansanda.
- Rundunar ƴansandan tarayya za ta iya bayar da gudummuwa idan aka samu take-haƙƙin ɗan adam, ko razana jama'a, ko kuma idan an samu barazanar tsaron ƙasa.
Sai dai ƙudirin ya ce duk wani matakin da rundunar tarayya za ta ɗauka na bayar da gudummuwa dole ne ya samu amincewar shugaban ƙasa a rubuce.
Wannan iko da aka ba gwamnoni ya sa wasu ke ganin za a iya wuce gona da iri wajen aikin ƴansandan jihohin.
Sai dai duk da waɗannan tanade-tanade, wasu na ci gaba da nuna fargabar cewa ikon da aka bai wa gwamnoni na iya sa a yi amfani da rundunar ta hanyar da ba ta dace ba.
Me zai bambanta ƴansandan jihohi da sauran rundunonin tsaro?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Wani masanin harkokin tsaro, Group Captain Sadiq Garba mai ritaya, ya ce babban abin da zai bambanta ƴansandan jihohi da rundunonin ƴan sa-kai ko askarawa shi ne ingantaccen horo da kuma tsarin gudanar da aiki.
A hirarsa da BBC, ya ce har yanzu akwai buƙatar gwamnatin tarayya ta ci gaba da riƙe wasu muhimman tsare-tsare na rundunar idan ta tabbata, maimakon a miƙa komai ga gwamnatocin jihohi.
"Akwai buƙatar kada a nuna ɓangaranci wajen zaɓen jami'an da za su shiga rundunar a kowace jiha," in ji shi.
Sadiq Garba ya kuma ce idan ana son ƴansandan jihohi su bambanta da rundunonin da ake da su yanzu, dole ne a ƙayyade yadda za su riƙa amfani da makamai tare da tabbatar da sun samu cikakken horo kan amfani da su.
Ya ƙara da cewa akwai buƙatar a soke ko kuma a haɗa rundunonin ƴan banga da sauran rundunonin tsaron sa-kai cikin sabon tsari.
"Idan ana son a samu tsaftatacciyar rundunar ƴansandan jihohi, dole ne a kauda irin waɗannan rundunoni," in ji shi.
A cewarsa, irin mutanen da za a ɗauka aiki da kuma horon da za su samu ne za su tabbatar da bambancin rundunar, domin ingantaccen horo zai sauya salon aikinsu tare da koya musu yadda ake amfani da makamai da gudanar da aiki bisa ƙa'ida.
'Babu abin da zai sauya'
Tsohon kwamishinan ƴansandan Najeriya, CP Muhammad Wakili (Singham), na ganin kafa rundunar ƴansandan jihohi ba zai kawo wani babban sauyi ba idan aka yi la'akari da yadda ake gudanar da wasu rundunonin tsaro na jihohi a yanzu.
Ya ce a ganinsa, waɗannan rundunonin da jihohi suka kafa ba su da wani babban bambanci da abin da ake shirin yi da ƴansandan jihohi, musamman idan aka yi duba da irin mutanen da ake sa ran za a ɗauka aiki.
A tattaunawarsa da BBC, ya ce duk wata babbar matsalar tsaro a Najeriya ba za ta yiwu a magance ta ba sai da sa hannun gwamnatin tarayya da Rundunar Ƴansandan Tarayya.
"Tsaron ƙasar nan ai dole sai gwamnatin tarayya," in ji shi.
Singham ya ce idan ba a samar da isasshen horo da kayan aiki ba, ba zai yiwu a ga wani bambanci ba, domin aikin ɗansanda na buƙatar kuɗi da kayan aiki masu yawa.
Ya ce maimakon ƙirƙirar sabuwar runduna, ya kamata a ƙara zuba kuɗi ne wajen ƙarfafa rundunar ƴansandan tarayya.
"Idan ana son a ga canji, ba sai a inganta na tarayya ba, maimakon ƙirƙirar na jihohi?" in ji shi.
Ya kuma yi watsi da hujjar cewa gwamnoni ba su da iko kan ƴansandan tarayya, yana mai cewa a aikace gwamnoni na da tasiri sosai kan yadda jami'an ke gudanar da ayyukansu a jihohi.
"Babu inda wani gwamna yake bayar da umarni, ɗan sanda ya ƙi bi... Ni dai ban taɓa gani ba. Wasu idan ka gan su ma za ka ɗauka jihar suke wa aiki."












