Gyaran hanyoyi zai rage matsalolin tsaro a arewa - Goje
A Najeriya yayinda matsalar tsaro ke ƙara ta'azzara, ɗaya daga cikin jiga-jigan siyasa a shiyar arewa maso gabashin ƙasar, wato tsohon gwamnan Gombe, kuma sanata mai wakiltar Gombe ta tsakiya Muhamad Danjuma Goje, ya ce ɗaya daga cikin dalilan da ke ƙara rura wutar matsala shi ne rashin hanyoyin sufuri.
A cewar sanatan, ya jima yana jan hankali da neman ganin an inganta hanyoyin jihohin yankin don shawo kan matsalar, kuma da alama a yanzu shugaban kasa ya ji kokensu, la'akari da yadda ya bada kwangilar soma aikin wasu muhimman hanyoyi a yanzu.
A cewarsa, ya ji daɗi a shugaban ƙasa ya amince da fara aikin tagwayen hanya daga Akwanga zuwa Jos zuwa Bauchi zuwa Gombe. "Da ya yi wannan ne sai na sake tashi na yi godiya, sannan na nemi a isar da hanyar ta kai Biu zuwa Maiduguri. Sannan na nemi a yi daga Gombe a yi tagwayen hanyar zuwa Yola ta ratse zuwa Jalingo. Idan an yi haka arewa maso gabas an mana komai."
Goje ya ƙara da cewa ya ji daɗi da ya ga har an je an duba aikin, saboda a cewarsa, "maganar gyara hanya na da muhimmanci, saboda masu ɓarna sun fi yi a wuraren da hanya babu kyau. Idan an gyara hanya, hakan zai taimaka wajen rage matsalolin tsaro a arewa musamman arewa maso gabas."